← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 255 OF 276

Sashe 255

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Akwai wani abokinsa matarsa da ta rasu ya buk'aci auranta yaransa tara marayu a yanzu auran shine rufin asirinta.

Na ji gabad'aya lamarin bai kwanta mini a rai ba abokin Babanmu ai da shakarunsa kuma ko auran za ta yi a yanzu akwai buk'atar zuciyarta ta nutsu kada don an ganta cikin ibtila'in rayuwa a yi kokarin k'
rasa kassara mata rayuwa saboda bata da jayayya tunda mafaka take nema kai tsaye zata amince ko da ranta baya so.

Da yake ni ce na zo da maganar kuma nake buk'ata sai ya ha'kura ya amince mini.

Anti Yagana ma ba ta yi jayayya ba ta nuna goyon bayanta dangane da hakan tana fad'in idan ta huta hankalinta ya dawo jikinta shekara daya zuwa biyu sai ta dawo gida ko kuma ta yi aure.

Akan haka muka tsaya kuma a ranar da yamma Magaji ya je ya d'aukota duk abinda ya faru ga rayuwarta na labartawa Hajja har da kuka tana fad'in sannu baiwar Allah kin ga jarabawa Allah Ya yafe miki mu kuma mugun ji da gani Ubangiji Allah Ya kare mu.

Hadiza tun a gidan Hajja ta fara yin dawainiya da su Hasan sai ta kar'be ni tunda da tare muke yi da iyami Hajja na dan yin abinda za ta iya amma zuwanta sai ta kar'be ni a duk sanda zan daga ido na kalleta sai k'walla ta cika mini ido.

Mace 'yar garu da ta samu gatan uwa a lokacin da take sharafi da jiki mai kyau ta koma haka Hadiza ko da can ba ni da abinda zan nuna mata tunda ta yi tashen 'yan matanci kuma bata ta'ba yin saurayi talaka ba masu arziki ne daidai gwargwado ne suke zuwa neman auranta.

Fara ce tas haka suke dukansu tunda Ummansu ma fara ce ta fi ni haske tana da kirji sosai a wancan lokacin ni kuma baya na fita da tsayuwar hallita mai kyau dalili ni jikina ta ko'ina dumur yake koda na yi haife-haife nan babu inda ya saki ya ragaje alhamdulillahi.

Ita kuma irin jikin Ummansu ne da ita a sake amma akwai kirji cikakke a lokacin budurci ba yanzu da suka risina ba saboda wahala da shekaru tunda kwanaki biyar kacal ta ba ni ba wani nisa a tsakaninmu amma wallahi ta fi ni tsufa hakan yana da ala'ka da wahala da rashin samun hutu zullumi fargaba da rashin 'koshi.

Alhamdulillahi ni kam kullum cikin hutu nake da kuma cima mai kyau tunda tsakani da Allah idan ba a zaman makokin nan na Gwaggo ba sai na ce na fi shekara tara rabona da shan ruwan pure water sai da mugun dalili ko maiduguri na je gidan anti Yagana ruwan gora Babansu Fadila yake sayo mini har na gama zaman da zan yi a gida.

Rabon zakkar da ya fitar ta zagaye dangina kaf daga can maiduguri Baban Saude ne wakili nan kuma Sunusi ne wakilinsa babban yaron baba Sule duk wanda sako ya same shi sai ya kira ni a waya ya yi godiya domin babu hanyar da za su same shi su yi masa godiya Y
'yan biyun gidanmu da su fari ana gobe za mu tafi suka zo muka yini tare muka sha ruwa cikin sakewa a bangaran da nake har ya shigo ya same mu muna raha abin mamaki sai ya zauna a cikinmu kunya kuwa duk ta kama su mussaman Hadiza da ta kasa daga kanta ta kalleshi dalilin abubuwan da ta yi a can baya ta dinga kar'be masa kudi tana shirya k'arya.

Ya dinga jan ta da magana duk domin ta sake amma ina ta kasa kanta a kasa har ya tashi ba ta dago ba.

Sahura ba ta samu zuwa mun yi sallama ba sai dai ta kira ni a waya ta yi mini godiya sosai domin itama ta kar'bi zakka da kayan abinci rigijib a wajan aikinsu
Komai nasa cikin tsari da lissafi duk yadda ya yi mini haka ya yi a b'angaran Hauwa domin da kunnena na ji Hajja na waya da Inna Uwani kan kayan abincin da aka fitar musu da zakkarsu ta ce abincin dai a sa direba ya kai mata can bauchi kudin kuma bayan sallah za ta kar'ba sai a lokacin ne ma Hajjan ta san da cewar har yanzu tana abujan ba ta koma gida ba.

Ranar da azimi ya yi ashirin muka tafi bayan mun yi sallama da Hajja Yusi ya na gaya mini cikin sallah zai zo ya yi mana kwana biyu cikin 'yan uwansa na ce to Allah Ya kawo shi lafiya.........
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*168*
Abinda ya so ya d'an ba ni mamaki bai wuce ganin ya tafi gidanta ya kwana ba.

To matarsa ce har yanzu tunda bai saketa ba a tunanina ni zaman da nake yi ba su samu matsaya ba har yanzu a cikin rikicin suke tunda bai ta'ba nuna mini cewar sun daidaita ba a lokacin dana tambaye shi ina yara bayan tafiyar masu aiki umara a takaice ya ce mini suna gidanta.

Ni da Hadiza muka kwana a gidan da safe muka tashi da aikin gyare-gyare zuciyata ta'ki tsayuwa waje daya sai tunanin yadda aka yi suka iya shawo kansa cikin k'an'kani lokaci duk da fusatar da ya yi akan lamarin to ko shine manufar rashin tafiyar inna Uwani a lokacin da ya koma bayan mun zo duba Gwaggo nake tunanin suka daidaita tsakaninsu amma abin ya ba ni mamaki sosai.

Na yi kokarin dannewa saboda samun kwanciyar hankali da nutsuwa zuciyata tana gaya mini gwara duk rintsi su shirya domin ko da ya yi musu abinda suke so zai iya auro wata tunda ya riga ya saba zama da mata biyu.

Amma yanayin yadda suka dinga jujjuya maganar ne ita da uwarta ke ba ni mugun mamaki tabbas Inna Uwani tsufa ya yi gardama kuma an yi fad'uwar ba'kar tasa.

Bai shigo ba sai wajan d'aya da wani Abu yanayin shigar da ya shigo mini da ita ya tabbatar mini da cewa daga massalaci ya fito.

Babu wani abu dana nuna masa a fuska ya zauna a falo cikinmu ni da Hadiza har k'asa ta durkusa ta gaishe shi Hadiza wani irin ladabi ta koyo a gidan gyaran halin da ta zauna
Ya amsa kuwa cikin kulawa ta tashi tsaye da Usaini a hannunta za ta nufi bedroom dina Hasan ya sanya kuka yana mika mata hannu wai sai ta d'auke shi.

Kwanaki shida kacal a tare damu yaran sun yi sabo da ita.

Uban ya kar'be shi daga hannuna yana fad'in." In ban da rigima da wane hannun za ta d'aukeka ka ci girma mana."
Ya dinga tsala ihu yana zillo tare da mika mata hannu shi kuma Usaini na kwance a kirjinta ya yi luf.

Na kar'be shi daga hannunsa abin mamaki ya'ki yarda wai lallai sai ta d'auke shi, kishi dai irin nasu.

Haka duka ta ciccibe su a 'kui'binta ta rirrikesu da hannunta ta nufi bedroom dina tana dariya yaron ya yi shiru ya daina kuka da zanbarwa.

Ya dube ni a nutse yana fad'in." Tausayi take ba ni sosai 'yar uwar nan taki Giwa."
A takaice na ce." Mun gode sosai Allah Ya kara rufin asiri?"
Ya zuba mini ido babu halin ri'ke hannu ko runguma saboda muna cikin ibada tunda ma Gwaggo ta rasu muka fara azimi ba mu yi wata kwanciyar kirki ba saboda abubuwa da ya wasa da suka sha kansa.

Ya sauke ajiyar zuciya ba tare da ya janye idonsa daga kaina ba ya ce." Zan tura miki kudi kamar yadda muka saba kowace shekara
domin ki sayi abinda ki ke buk'ata na sallah.

Yara Hauwa ta saya musu wurin k'awarta suna wurinta ta ce a gaya miki idan an jima suna shigowa yi miki gaisuwa.

"
Na ce." Ban gane hausar ba?"
"Ina nufin kayan s
allar yara takalma da riguna na kanti an saya akwai saura wurin telansu zai kawo cikin satin nan inshallah."
Na d'an yi jim ina nazarin maganarsa a wannan karon kenan ita ta kar'bi kudin ta saya musu kayan wajan k'awarta sanin da na yi duk salla marigayiyace Maryam ke yi musu wannan hidimar amma dai har yanzu telansu da yake yi musu d'inki yana nan shi yake yi musu ko bayan rasuwar wadda ta d'auke shi aikin ya cigaba domin ni ma wasu lukutan yakan yi mini d'inkin amma ba sosai ba watannin baya ne da ya ce a fitar da kayansu gabad'aya ya sanya a aka kawo musu sabbin 'yankati to me hana wannan karon ma bai sanya an kawo musu ba.

A tak'aice na ce." To shikkenan." Ya dube ni yana fad'in.'' Ko hakan bai yi miki ba ne?"
Na ce." Ko bai yi mini ba ai dole na ha'kura tunda zaman lafiya nake so ko, amma ai da can ba ita take saya musu ba."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." To yanzu don ta nuna ra'ayinta ai ba lefi bane ki duba kayan sosai idan ba su yi ba sai a canza musu
ku dai zauna lafiya da juna, ita mun samu daidaito da ita kuma mun yi alkawari a zaman da muka yi domin har sai da kawunta ya zo mun zauna da ita Inna Uwanin ta yi alkawari kan cewa za ta gyara tare da ko'karin kawo zaman lafiya a junanku.''
Shiru na yi ban iya ce masa komai ba saboda mamaki.

Ya tashi ya hau sama ban bi shi ba na yi zamana ina nazarin yadda abubuwa suke canzawaa daga wannan sai wannan zuciyata tana gaya mini kudi ta kar'ba masu kauri a hannunsa domin ta 'karu tunda dama neman hanyar da za ta dinga samun kudi take yi.

Ita kuwa wadda ta rasu tana yi ne da dukiyarta bata neman kwabonsa ita nata salon kenan tunda tana da arziki.

Ita kuwa Hauwa na tabbatar da cewa ta yi hakane domin 'karuwarta.

Da yamma muna kicin tare da Hadiza muna shirin abu bude ba'ki suka shigo..
Chapter 255 · 0% Book details