Sashe 114
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin zuciyata na godewa Allah da bai sa na cuceta a zamantakewarmu ba abinda suka yi a can baya shine yake damunta
Towol din goyansa ta d'auko mini na goya shi a bayana, cikin kankanin lokaci bacci ya d'auke shi.
Ina daga tsaye ina dan jijjigashi tana gaya mini irin rigimar da ya dinga yi kafin su yi arba'in har yanzu bashin baccin da ta tara bai sake ta ba.
Maigidan ya shigo amaryarsa a bayansa ta nade jikinta da wata lafiyayyar lifaya irin ta manya.
Duk shigar da za ta yi da gayu ba abin mamaki ba ne domin ko bata auran mai dukiya ita kanta hajiyar kanta ce ga uwar dukiyar da aka mutu aka bar mata da yaranta.
Fuskarta a sake ta zauna kan kujera tana dariya yayin da take kallon Hauwa tana ce wa." Maijego ina fatan ba ki yi fushi da ni ba ko?"
Hauwa ta dan yi murmushi irin wanda babu nisha'di a takaice ta furta." Ban yi ba Hajiya ai maigidan ya ce ba ki ji dad'i ba ya jikin naki?"
Ta ce." Wallahi kam a lokacin na yi ta fama da zazzabi da mura har da ciwon kai, dalilin da ya sanya kenan ban samu zuwa ba."
Ta ce." Allah Ya sawwa'ke abinda ake ta fama dashi kenan."
Na kwanto yaron fuska a sake na mik'a mata shi ta kar'ba da walwala a fuskarta.
Ko ba a fad'a ba ita din macace mai masifar son yara ko ba na bata ne wallahi irin rikon da take yi wa Yusi ko ni albarka duk abinda yaranta za su sanya a jikinsu za su ci babu bambanci wannan kad'ai ya kan sanya ni jin kunya da nauyin yin tutsu akan lamarinta.
Kuma sam ba ta da fitina a haka dai tana zaune da kowa lafiya ban ta'ba ganin kishi a idonta ba.
Dad'in ganinmu mun sake muna hira gabad'ayanmu ya sanya shi kashingida kan kujera yana ta murmushi tunda suka shigo bai ce komai ba sai kallonmu yake yi yanayinsa ya nuna ya ji dadin ganin yadda muka fara fahimtar juna.
Sai bayan mun nutsu tukkuna ya gyara zamansa domin mu tattauna tare da samun matsaya akan yadda za mu shirya zama.
Legos ne kowacce bata so a cikinmu amma kuma tilas ya kama mu duka saboda babu yadda za a yi ace mu bar shi a can shi kadai alhalin duka muna raye adalci shine a ce a raba.
Ni ya bawa damar magana tunda ni ce gaba dasu gidan cikin nutsuwa na ce." Ni na amince zan dau'ki wattani shida idan ya so ku kuma sai ku raba kowacce wata uku ina ganin hakan zai fi."
Hajiya Maryam tana murmushi cikin nutsuwa ta ce." Anya kuwa ni zan iya akwai abubuwa da yawa da suka sha kaina anan din wallahi ba na so na yi nesa yanzu ko kad'an shi Yallabai din ya sani da za ku yi mini alfarma sai na ce ku barni a nan babu damuwa ta b'angarena in sha Allahu."
Falon shiru ya yi bayan maganarta.
Yana zaune bai ce komai ba alamu sun nuna tun a gidanta sun gama maganarsu ya d'aukota ya kawota ne don ya wanke kansa kada mu zarge shi.
Na dubi Hauwa da tun da muke maganar ba ta ce uffan ba na ce." To ke me ki ke ga ni Hauwa."
A takaice ta ce." Duk yadda kuka tsara ya yi mini sister."
Sai na dube shi a nutse na ce." To ka ji abinda kowa ya fad'a menene ra'ayinka?"
"Ra'ayina shine naku giwa, ku tsara yadda kuke ganin za ku zauna babu takura idan kun yi mata alfarmar da ta nema ni a wajena daidaine amma kada wadda ta kalubalanceni anan gaba.
'Yar uwarku ce ta kuma fito ta gaya muku dalilanta nasan zamanta anan din cikinku duk kun sani, idan kun goya mata baya to duk 'karuwar ta mu ce bakidaya."
Ban yi mamaki da sunan da ya kira ni ba, domin a wasu lukutan da sunan yake kira na mussaman idan yana so ya rarrashe ni idan mun yi fada ko neman wata buk'ata.
Zai ce giwa ko zinariya
Cike da takaicin maganganun da yake yi na ce." To wa ka ji ya ce bai amince ba, na d'auka ai zaman da muka yi gabad'aya don mu samu matsaya ne a junanmu, ni ta b'angarena babu damuwa tunda har na iya d'aukar rabi na basu rabin na ce su raba a tsakaninsu Allah Ya taimake ka duk wannan maganganun ba su taso ba."
Hauwa ta zum'buri baki tana fad'in." To ni ma dai haka na ga ni."
Ita kam dariya ta yi tana fad'in." Na gode sosai, Allah Ya daidaita zamanmu ya kuma amfani zuriyarmu, na gode ni zan koma." Ta mike tsaye tana gyara yafen lifayar da take jikinta.
Na ce." A haba Hajajju ai babu buk'atar godiya duka taimakon kai ne wallahi kada ki damu an zama daya gabad'aya Allah Ya shige mana gaba."
Ta amsa da "Amin." Fuskarta yalwace da fara'a ta kama hanyar fita tana fad'in." Sai na sake zuwa mu gaisa da yarona yanzu bacci yake yi ba mu gaisa sosai ba." Hauwa ta ce." To shikkenan sai an jima.
Tana fita Hauwa ta dube shi kamar za ta fashe ta ce." Gaskiya zan gaya maka irin yadda kake nunawa matar nan kamar itace take auranka ya yi yawa.
Ina lefi akan kawaici da karar da muka yi mata har sai ka fad'i wasu maganganu, ai sai ta d'auka hassada muke yi mata, kuma macace mai mutunci da sanin ya kamata gatanan babu wata matsala a tare da ita."
Ya ce." Mai na yi muku kuma, shikkenan daga na fad'i magana sai ku juya mini, halinta na fad'a tana da sau'kin kai gashi dai duk ta girmeku amma bata nuna muku gadarar hakan.
Sannan duk da dukiyar da take da ita bata d'auki kanta a wata tsiya ba, ta sake daku sosai ta daukeku 'yan uwa daga fad'in haka sai ya zama lefi."
Na ce." Mu ai dama ba muce maka wata tsiya ba ne, kuma duk abinda take yi ai ba a sanyata ba gani ta yi zata iya, abinda dai zan gaya maka idan zama ya sake hadamu irin wannan muddin kasan zaka goyu da bayan b'angare daya to kawai ka yi shiru da bakinka domin kuwa yin hakan zai janyo maka bacin rai za ka rikita gidanka da kanka."
Don girman Allah kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Ya ce." Tunda kece Hajja sai ki ba ni umarni kin ji ko, ku abu kad'an mutum zai yi sai ku zarge shi Allah Ya sawwa'ke."
Yana rufe baki Adam da Yusi suka shigo janye da wata madaidaiciyar akwati gaban Hauwa suka ajiye Adam ya ce." Momi ce ta ce wai gashi na Khalil ne."
Ta ce." Ku ce mata na gode sosai Allah Ya kara arziki."
Suka juya za su fita muka had'a ido da Yusi sai yasa dariya ya rike hannun Adam na d'auke kaina ina fad'in." Taka zata kawo ka wurina ne yaro."
Har za su fita sai ya kira su ya dubi Yusi yana fad'in." Mai ka yi mata take harararka?"
A hankali ya ce." Babu komai Baba, ai muna shigowa kullum mu gaisa da ita ko ?" Ya fad'a yana kallon Adam da yake murmushi.
Ya amsa da "E Muna zuwa." Ya ce musu ku tafi abinku rigima take nema."
Suka bud'e kofa suka fita kamar wasu 'yan tagwaye komai na jikinsu iri d'aya ne.
Kaya ne na waje irin wad'anda take sayarwa cike da akwati kayan nan kudinsu zai haura dubu dari uku domin duka babu k'ananu har da takalma da tarkace dai kala kala.
Tare muka duba kayan yana zaune bai ce mana komai ba, har muka gama dubawa muka rufe akwatin bai tanka ba daga karshe ma sai ya tashi ya haye ya sama ya barmu a falon mu biyu.
To ganin yadda muka k'ulle muka zama tsintsinya madaurinki d'aya ya sanya shi shiga hankalinsa sosai.
Tun ranar da muka yi zaman nan bai sake yin wata magana da ta danganci matarsa ba saboda ganin yadda muka nuna masa ba mu yarda ba a tun farkon fari.
Dama neman magana ne kawai tunda na farko ai bai ga mun ware ta ba, sannan bai ga muna neman fitina da ita ba, maganace a ka zauna ana tattaunawa wadda kowa yake da hakki akai to babu dalilin da zai sanya shi ya budi baki ya yabe ta a gabanmu bayan alfarmar da muka yi mata.
Macace mai nagarta kuma wadda take amfani da ilminta a inda ya dace.
Duk irin kushe da kiyayyar da mutum zai yi a kanta wallahi kyawun halinta sai ya sanya wataran mai kushiya akanta ya yaba mata......
Muje zuwa
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.
Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.
'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.
A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*76*
Ina jin kunya da nauyinta sosai, ba don komai ba sai don yadda take k'aunar abinda ya jib'anceni.
Na jima ban ga mutum mai kara da kawaici irinta ba.
Daf da zamu tafi Legos muka yi waya da Sahura take gaya mini an kawo kudin Yusra an kuma sanya rana shekara daya mai zuwa.
Na ce har saurayin ya gama ginin kenan ta ce mini saura kad'an.