Sashe 235
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai daf da magriba muka yi sallama ta tafi. ban yi niyyar girki ba mun dai yi waya da Hamusu tun jiya da rana ya ce mini zai zo mu yi lissafi sai na ce masa ya taho mini da towo daga gidan Gwaggo shiyasa ban shiga kicin ba ko da rana ma Sahura wainar fulawa ta soya mana kayan manja da yaji muka ci cikin marmari.
Sai da na yi sallar isha'i tukkuna na kunna wayata.
A hankali ina duba wayar kimanin minti goma sha biyar ya kira na bari sai da ta katse ya sake kira tukkuna na daga nasa a kunnena na ji ya sauke ajiyar zuciya cikin taushin kalami ya kira sunana ." Na amsa da "Na'am."
Ya furta." Kina lafiya ko ya gajiya?"
Na ce." Kalau nake ina
yara?''
Ya sake sauke ajiyar zuciyar da nake jin saukarta a kunnena kamar yana gabana.
Ya ce." Suna lafiya Amina me yasa ki ka kashe wayarki ne?"
A takaice na ce." Na huta gajiya ne shine dalili?"
Ya yi shiru na dan wani lokaci kafin ya ce." To shikkenan sai da safe ko na kira ne domin na ji ya ki ke."
Har zai kashe na ce." Ina son zuwa gidan Gwaggo gobe ko jibi."
Ya furta." Allah Ya tsare."
Na amsa da Amin jikina a d'an mace ganin duk abinda na ce zai amsa babu korafi."
Ya ce." Ba dai wata matsala ko?"
"Umm!" Na ce saboda na ji haushi da bai tambayeni yaushe zan koma ba.
Ya sake fad'in." Sai da safe?"
Na ce." Allah Ya ba mu alheri."
Ya kashe wayar ni ma na kashe tawa jikina gabad'aya ya mutu da abinda ya tsiro da shi wato tunda na ce sai na haihu zan koma ya daina takura mini.
Sai na ji hakan bai yi mini dadi ba.
Ko da hamusu ya zo ma a daddafe mu kayi lissafin towon da ya kawo mini kad'an na ci na ajiye ragowa da safe na dumama.
Na kwanta da takaicin abinda yake faruwa. haka na tashi sukuku babu kuzari.
Ruwan shayi kawai na sha sai da rana ta yi tukkuna na dumama towon.
Zuwan Kamalu da Yusi shi ya d'an warwarar da ni na samu walwala ganinsu cikin tsabta da nutsuwa da kamala.
Na dinga godiya ga sarki Allah da ya yi mini wannan tagomashi kowa ya dogara da k'afafunsa sai a lokacin ma nasan da abinda yake faruwa shirye shirye ya gama kammala karshen watan da muke ciki na musulunci yaron zai ta fi jami'ar musulunci ta madina bisa sahalewar uban rik'on nasu shine ya yi masa jagoranci ya kuma shirya masa tafiyar.
Ban nunawa yaron cewa ban sani ba muka tafi kan cewa ai na san da tafiyar na kuma yi masa addu'a kwarai da gaske da fatan alheri.
Yini muka yi tare suka ce daga nan gidan Gwaggo suka nufa na ce su gaishe da ita sannan su sanar da ita ina tafe ni ma.
To abinda ya dinga faruwa kenan a tsakaninmu.
Zai kira ni a waya kullum mu gaisa da kulawa amma fa ba ya yi mini maganar komawa sbuja zai dai ce mini yara suna kewata amma shi ba zan tantance halin da yake ciki ba tunda yana ko'karin daurewa ya nuna mini bashi da damuwa.
Ni kuma takaicin abinda yake yi ya hana ni gaya masa ga ranar da zan dawo amma zahiri hankalina gabad'aya ya koma can da tunanin kada Hauwa ta samu damar yi mini dariya ko wata kafar da mutuncina zai zube.
Sati uku da bikin Usaini ya kawo mini amarya tun safe ya har yamma muna tare Hajara ta zama 'yar gari yarinya ta murmure ta kara kyau kuma ta fara koyar kwalliya irin ta 'yan birni sosai na ji dadin wannan lamari.
Muna tare har dare domin cewa ya yi sai ya taso daga kasuwa tukkuna zai zo ya d'auketa su tafi da muka yi waya ya ce mini yana gidanmu amma gashinan akan hanya.
muna hira a falo ni da ita maigidan ya shigo wannan karon tare da Ade suke.
Haka kawai na tsinci kaina cikin faduwar gaba domin ban tsammaci zuwansa ba don bai gaya mini ba duk da da safe mun waya bai ce yana hanya ba.
Daga bakin kofa Ade ya gaishe ni ya juya ya fita da saurin gaske.
Ita kuwa Hajara tun kafin ya shigo cikin falon sosai ta zame daga kan kujera gwiwarta a kasa ta fara gaishe shi.
Ya d'an yi jim yana kallonta kafin ya amsa ya dube ni a tsanake ya ce." Amarya ce ko?" Yadda ya fadi maganar ya tabbatar mini da cewa bai ma gama sheda ta sosai ba duk kuwa da cewa a lokacin da ake tirka-tirka auransa da ita da hotonta daya a wayarsa wanda shi ya nunawa Hajja wata'kila ya d'auketa hotone a lokacin domin ya kare mata kallo ya ga ko ta dace da abinda ake buk'ata Allah ne dai masanin dalilin hakan.
Na saki fuskata sosai Ina fad'in." Itace ta zo gaisuwa da ban gajiya."
Ya gyada kansa da d'an murmushi a tare da shi ya ce." Ya yi kyau, ina angon naki yake?"
Ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi kunya take ji."
Na ce." Yanzu aka yi waya da shi yana zuwa su tafi."
Rufe bakina ke da wahala kuwa Usaini ya shigo.
Ganinsa ya sanya ya risina yana fad'in." Barka da dare ya kuwa sanya hannu ya dago shi ganin yana ko'karin tsugunawa ya dinga mika masa hannu domin su yi musabaha yaron yana nok'ewa ya'ki kar'bar hannun cikin girmamawa sai sinne kai yake shi kuma yana yi masa dariya tare da tsokanarsa ango na amarya."
Ya rike hannunsa sosai Yana fad'in." Allah Ya sanya alheri ka ji ko, ka kula na so na samu zama da kai kafin d'aurin auran Allah bai nufa ba, yanzu gashi mun had'u na yi maka murna kwarai domin ka yi dace da yarinyar arziki ka kula da amana da kuma hakkinta Ubangiji Allah Ya taya ka riko."
Ya dinga amsawa da Amin ya rabbi na gode ranka ya dad'e Allah ya saka muku da alheri Ubangiji Allah Ya biya bukatu."
Ya amsa da Amin Ya Allah babu buk'atar godiya Malam Usaini ai kai dan'uwana ne?"
Ya fad'a tare da kallona Yana cewa." Ko ba haka ba ne?"
Na gyad'a kaina jikina a d'an sanyaye na ce." Tabbas."
Usaini ya dube ni yana cewa." Anti za mu tafi sai mun yi waya Allah Ya saka da alheri."
Na yun'kura na tashi a hankali itama ta tashi na rika hannunta ina fad'in." Na gode da ziyara Hajara a gaida gida ki kuma kula da shawarwarin da na baki."
Ta ce." In sha Allahu rabbi anti."
Suka juya wajan da yake tsaye yana murmushi shima suka yi masa sallama.
Ya fara laluban aljihunsa ya fito da kudi yan dubu sabbi kar da su ba su dai da yawa ba su wuce dubu ashirin ba ya mi'kawa mata yana fad'in." Ga shi a sayi jan baki da hoda." Ta'ki kar'ba da sauri ta bi bayan mijinta sai ni na kar'bi kudin na bi bayansu da sauri.
Koda na dawo cikin falon baya nan ya hau saman don haka sai na bi shi a daddafe na k
rasa hawa na same ya cire rigar jikinsa yana zaune da singeliti da dogon wando agogon hannunsa yake ko'karin cirewa.
Ya zuba mini ido har na k
rasa kusa da shi na zauna ya furta." Hajiya Giwa manya."
'Dan juyar da kaina na yi a gajarce na furta." Ya hanya amma ba ka gaya mini kana tafe ba."
Ya ce." Hakane tafiyar ta same ni bagatatan ai kin san Alhaji sammani ko mutumin nan da ya cutar da ni shekarun baya."
Na ce." Na dai ji labarinsa.
Ya ce." Mahaifiyarsa ce ta rasu kin san mutanan Dambatta ne kuma tare suke da Hajja kawaye ne tun lokacin k'uruciya ni da shi kuma abokai ne na unguwa an tashi tare har dai ya zama amintaccena a wancen lokacin kafin ha'inci da son zuciya ya shiga."
Na ce." Allah sarki Ubangiji Allah Ya gafarta mata."
Ya amsa da "Amin a takaice.
D'akin ya d'auki shiru na d'an wani lokaci kafin ya dube ni ya ce." Ya yara na ina fatan suna lafiya." Ya fad'a idonsa kan cikina.
Na ce." Suna nan kalau sun ce a gaisheka."
Ya saki fuska kuwa yana cewa." Ina amsawa amma ai gaisuwar iri-iri ce ko?"
Na yi shiru ban ce masa komai ba illa ido dana sanya masa ganin yadda ya kara haske fatar jikinsa ta yi kar har kumari ya yi a cikin wannan satikan da ban gan shi ba idan ba gizo idona yake yi mini ba, ban hangi wata kewa da damuwa a tare da shi ba ban sani ba ko wata ga'ba ya d'auka domin daina nuna mini so da rawar jiki.
Jikina duk ya yi sanyi na kasa janye idona daga kansa iina Jin wani bala'in kishi a cikin raina sabon gida sabuwar soyayya tunda nake da shi ban ta'ba zama a gefansa bai ta'ba ni ba hannuwana suna shan mutsika idan ya rike haka zalika ya dinga sumbatar wuyana kenan yana shishshige mini yanzu da muka yi kusan sati biyu bamu ga juna ba babu wani abu na kewa da marari dana hanga a tattare da shi.
Ya furta." Bari watsa ruwa ki ba ni abinci ko?"
A takaice na ce." Ban yi girki ba." Na yi na yi na ha'kura kada na nuna jin haushin abinda yake yi na kasa jurewa.
Ya ce." Ba ki yi girki ba kamar Yaya da me ki ka ciyar da ba'kin da ki ka yi?"
Na ce." Na dare ne ban yi ba dama daga gidan Gwaggo Hamusu ke kawo mini towo ba kasafai nake girkin dare ba."
Ya d'an yi jim yana kallona na wani lokaci kafin ya ce." Ko ni zan yi miki girkin ne Hajiyata."
"Idan za ka yi zan ci."
Ya ce." Zan yi kuwa yanzu jira ni na yi wanka."
Ban ce masa uffan ba ya tashi ya nufi toilet na bi shi da kallon takaici da b'acin rai.