Sashe 181
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba mu da iyaye wallahi domin ba zamu ta'ba nuna ku a matsayin iyayenmu ba."
Suka yi shiru anti Yabi ta yi kasa da kanta tana fad'in." Ba haka ba ne Nusaiba wallahi kada ki zarge mu domin rashin Maryam na kowane.
Ba mu da yadda za mu yi da Bashir tunda ya zo yake daga mana hankali wai a raba gado a bashi rabonsa, amma mu ai mun fi buk'atar Maryam akan abinda ta tafi ta bari na dukiya."
Babu wanda ya ce mata komai, ya sake duban Nusaiba a karo na uku yana fadin." Ya aka yi har ya shigo ya yi miki Illa abinda nake so na ji kenan.
Tana kuka ta ce." Wai sai na bashi wayoyin Momi da atm din da kuma mukullin dirowar da take ajiye muhimman abubuwanta."
Ya gyad'a kansa cike da tsananin al'ajabi da mamaki, shi kaddararsa kenan abokinsa ya rasu ya bar shi da rikicin iyalinsa in ba haka ba shi a tarihin rayuwarsa da family dinsu wani abu na tashin hankali makamancin wannan bai ta'ba faruwa ba.
Ya kama hanyar fita yana fad'in." Zo mu je d'akin ki nuna mini dirowar.
Ta tashi da sauri tare da sanya yaranta a gaba ta bi bayansa su kuma suna tsaye cikin jin kunya Ruky ce kawai take tsugune gaban Nabila tana yi mata tofi.
Madaidaiciyar dirowa ce ta mussaman domin ba irin ta gado ba ce wannan maybe daban ta sanya aka yi mata.
Ya d'an ta'ba ya ji yanayin katakon yana da nauyi.
Sukairaju ya kira a waya ya ce ya dawo.
Ya fito falon Salim da Adam suna tsaye suna magana ya a kira Mairo.
Adam ya dinga bubbuga kofar dakinsu tana fad'in." Wanene a cikin tsoro."
Sai da ta yi muryar Adam din tukkuna ta bude ta fito Taburni ta biyo bayanta duk sun gigice kuma a tsorace suke.
Ya ce su had'o kan yaran kaf su biyo bayansa.
Haka akayi kuwa yaran duk suka fito ganin Babansu ya sanya suka ruga wajansa suna kuka tunda a gabansu abin ya faru lokacin da Bashir din ke ko'karin kai wa Nusaiba duka ga fuskar Nabila da ta'bon yanka da jini."
Duk da Bashir din baya gidan Nusaiba kasa zama ta yi a gidan dalili ta tsorata ainun da 'yan uwan momin nasu.
Salim da Adam ne kawai suka koma dakinsu ita kuma ta bi bayansa da yaranta tana kuka cikin tashin hankali ga wuyanta yana d'an yi mata zugi kad'an dole sai ta je asibiti.
littafin gudun aure na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Haka muka k
rasa kwana cikin alhini da damuwa mai tsananin gaske.
Da safe da wuri Salim ya shigo ya biyo ni har d'aki ya gaishe ni amma bai yarda mun had'a ido ba ya ce mini asibiti za su je yanzu da Nusaiba na biyo shi falon sai na same su tare da maigidan a tsaye suna magana itama ta gaishe ni cikin jin nauyi na amsa tare da tambayarta jikin ta ce da sau'ki.
Sai bayan da suka fita ne tukkuna ya juyo yana kallona tare da cewa." Ina yaran suke?"
Na ce." Suna tare da Mairo a can d'akin Baba Tabawa."
Ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce." Sun dawo gidansu daga yau." Cike da godiyar Allah na furta." Allah Ya taya mu riko ya kuma albarkace su."
Sama ya nufa yana amsawa.
Ban bi bayansa ba sai da na kintsa jikina tukkuna na hau na same shi shima ya yi wanka yana dan duba wayarsa.
Na ce." A kawo maka abin kari ko?"
Ya ce." Bari zuwa an jima kad'an, abin nan da ya faru ya daga mini hankali Amina, wai me wasu suka mayar da zumunci ne, mutane idonsu ya rufe akan abinda duniya.
Yar uwar nan ta su sanin da na yi mata lokacin da take raye ta wahalta musu kwarai da gaske domin ko kafin rasuwar iyayensu itace jigon kula da su Alhaji Amadu na yin nasa ko'karin.
Ina daya daga cikin mutanan da suka dinga bashi Sha'awar bata goyon baya tare da ha'baka kasuwancinta tunda iyayenta ba su da k'arfi kuma itace babba.
Ta yi musu zumunci k'warai ta kuma dinga ko'karin halakar da kanta duk akan su rayu yanzu ta fad'i ta mutu suna rigima akan abinda ta bari, abinda ya fi ba ni tsoro Bashir da yake ko'karin halaka yarinyar nan Nusaiba akan abinda bashi da hakki."
Ajiyar zuciya na sauke tare da fad'in." Gaskiya da tsoratarwa a cikin wannan lamarin.
Jiya da daddare na ji ita Nusaiban tana cewa shi Bashir din ya gudu an neme shi an rasa amma yana jin rasuwar ya dawo wai a bashi hakkinsa."
Dariya ya yi irin ta takaici kafin ya ce." Ba shi da hankali ai da alama shaye-shayen da yake ya fara ta'ba masa kwakwalwa wannan barin irinsu ai babbar masifa ce, yana can hannun hukuma ai dama nemansa suke yi d'an iska."
Na kalle shi jin ya yi zagi tabbacin abin ya yi masa ciwo sosai na furta." Allah Ya rufa asiri yasa mu fi karfin zukatanmu."
A tak'aice ya amsa da "Amin."
Idona ya sauka kan bakuwar dirowar da na ga Sukairaju ya shigo da ita a tun jiya da daddaran.
Ganin inda nake kallo ya sanya ya ce." Sun ce wai muhimman abubuwanta na ciki an rasa mukkulin kuma dalilin da ya sanya na ce a d'auko mini ita gabad'aya idan na samu nutsuwa zan sanya a bud'e a gaban yaran domin su tabbatar da abinda yake ciki na game da dukiyar uwarsu."
Na ce." Hakan ya yi, Allah Ya kawo musu sau'ki ya kuma takaita."
Ya sake amsawa da Amin Yana fad'in." Kafin na shigo yanzu ai na sake shiga gidan tare da ba su umarni kan cewa duk su had'a kayansu su tafi basu da amfani sam gida kuma ba na Maryam ba ne ballantana su yi magana na Alhaji Amadu ne da y'a'yansa, ba su da gurin zama a cikinsa."
murmushi kawai na yi irin na takaici ina mamakin karfin halin wasu mutanan, a ce akan kudi mutum sai ya sarayar da mutumcinsa.
Duk kawaici irin na mutumin nan sun 'kure shi yana korarsu Allah na gode maka daka sanyawa iyayena wadatar zucci shima Baba Sule Allah ya taimake ni ya daina ya kama kan sa ganin yana tara surukai.
Da yamma can kira ya shigo wayata da sabuwar number.
Da mamaki na daga tare da sallama.
Nusaiba na ji tan fad'in." Anti Amina Ina yini."
Na amsa da kulawa ina sauraranta tana fad'in." Na kar'bi lambarki ne a wurin Adam dama zan gaya miki cewa Salim ya wuce da ni gidana bayan mun dawo daga asibiti ana I gobe addu'ar bakwai zan zo sai na kwana idan an yi addu'a sai na tafi."
Cikin nutsuwa da kulawa na ce." To shikkenan hakan ya yi, Allah Ya huta gajiya ya kuma kiyaye faruwar hakan anan gaba.
Ita kuma Mominku Allah Ya yi mata rahama."
Ta amsa da "Amin cikin sanyin jiki muka yi sallama.
Koda na gayawa maigidan yadda muka yi da ita yace ai ta sanar da shi.
A daran ranar Mairo da Taburni suka had'o kan kayansu da na yaran gabad'aya kayansu na sanyawa da kayan wasansu irin wanda Momin take saya musu Minal ta dinga bin Mairo tana kuka wai sai ta tashi sun koma gida a daran.
Ta'ki jin rarrashi Hassana da Husaina dama babu fuska domin ba su ganta ba a wajena suna zaune dai suna kallonta duk sun yi shiru kamar a tsorace suke da ni.
Sun 'ki sakin jikinsu rigima take yi sosai lallai sai Mairo ta tashi sun tafi na kamo ta ina fad'in." Za ki je wurin Baba?"
Ta d'aga kanta.
Na dubi Mairo tare da fad'in." Ta ja su d'akinsu da na ware musu a falon su ci abinci.
Baba Tabawa ta samu mataimakiya Taburni tare suka shiga kicin a yammacin ranar.
Na ce su yi sallah isha'i tukkuna kafin su ci abincin."
Ta amsa da "To." Wanda ya yi daidai da lokacin da ya sauko ya dubi Khalil yana fad'in." Yi maza ka dauro alwala mu je massalaci."
Ya tashi da sauri.
Ya dube Minal din dake saman cinyata tana kuka.
Hannu ya mik'a mata ta sauko daga jikina ta nufe shi ya sunkuya ya d'auketa ya sanyata a k'ugunsa irin d'aukar dai ake yi yaran da ba su wuce shekara biyu zuwa uku ba.
Ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya ya dube ni yana fad'in." Me aka yi mata ne?"
Na tashi tsaye ina fad'in." Wai sai Mairo ta tashi sun tafi gida."
Ya yi murmushi yana cewa." Amina rigima ai a gidan kike."
Na ce." Gidan Momi fa take nufi."
Ya dire ta a kasa ganin Khalil din ya fito ya ce." Momi ai tana can gidanta na gaskiya Amina, ita kuma Minal nan ne gidansu."
Ya kama hanyar fita Khalil ya bi shi a baya da sauri.
Kaina na girgiza kawai na shige d'akina domin gabatar da tawa ibadar.
To ranar sadakar bakwai din kamar yadda ya fad'a abinda ya faru kenan bai ma zauna balle a zo a taya shi zaman.
Addu'a kawai ya sanya aka yi mata a massalatai.
Nusaiba anan wurina ta kwana duk da Nabila tana can gidansu ita bata tafi tana tare da su Salim don bala'i har da kukanta tana fad'in ba zata iya tafiya ta bar su su kadai ba, kuma mamansu kafin ta rasu ta ce ko bayan ranta ta tsaya ta kula mata da yaranta.
Haka suka ha'kura suka kyaleta shima Yallabai din da ya ji cewar ba ta tafi ba sai da abin ya bashi haushi sosai ya k:yaleta ne kawai domin ya ga iya gudun ruwanta.
Duk da Nusaiba ta san tana gidan hakan bai sanya ta shiga ba nan su Salim din suka same ta.
Ta shiga cikinsu Mairo suka yi aikin funkaso da fanke manyan kuloli aka fita da su domin sadaka.
Tun bayan azahar ya shirya ya fita.
Muka kasance da Nusaiba da yaranta har bayan la'asar kafin ta yi shirin tafiya gidanta.