Sashe 213
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai tsaye a yanzu ba zan zargi Malam D'aha da cewa shima kwad'ayin dukiya ne ya sanya shi daukar yarsa 'karama irin wannan ya bawa tsoho wanda idan da ya yi aure da wuri babu shakka ya kusa jika da ita domin dai Hajara ta wuce a ce 'yarsa idan auransa na fari ya d'ore duk da lokacin ma sai da ya zama tuzuru ya yi ya kuma fara da mace to ba ba shakka Hajara sai dai ta zo a jikanyarsa ta farko.
Fisabillahi Malam D'aha bai dubawa yarinyar nan ba kuma ya tauye mata rayuwa ko da Alhaji Sulaiman ya yi aure eh tabbas budurwa ce amma wadda ta jima bata auru ba domin na ga calendar su shi da ita ta girmi Hajara sosai a k'alla ita za ta yi irin ashirin da biyar zuwa da bakwai.
To idan ya zame masa dole auran budurwar sai ya nemi mai k'wari ba irin Hajara ba wadda yanzu ne take tasowa ba tasan ma menene auran ba.
Na yi zaman sati daya a gidan na kuma fahimci cewa gidan na da tarbiya masu wadatar zucci da malunta ina ganin saboda kwad'ayin dukiya ba zai d'auki yarsa ya bayar ba sai don wani dalili nasa ko hango nagarta da tabbacin za a ri'ke masa 'yarsa a kula da ita.
Wannan shine abinda na fi gazgatawa daga gare shi ba wai ya bashi ita ba ne domin ganin yana da kudi da rufin asiri.
Kwanan tunani da zullumi na yi kan wannan lamari gabad'aya kaina ya d'aure na rasa yadda zan yi na auna mas'alar a sikeli domin hango cancanta da dacewa.
Ina fitowa daga wanka kira ya shigo wayata dake aj
iye a gefan gado na k
rasa da sauri na d'auka.
Baban Saude ne gabana ya yanke ya fadi domin ban kawo komai ba sai mutuwa.
Shikkenan Dada ta rasu ban je na dubata ba Allah ya raba ganawarmu.
Hannuna na rawa na sanya wayar a kunnena cikin mutuwar jiki da saranda na yi sallama.
Ya amsa da dakakkiyar muryarsa wadda hakan bai zame mini abin mamaki ba tunda sanin da na yi masa mutum ne tsayayye ba komai ne yake gigitashi ba ko da kuwa mutuwar ce.
Murya na rawa na gaishe shi ya amsa a dakile kafin ya rufe ni da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita.
Na yi kasa'ke da waya a kunnena ina sauraransa domin dai abinda ya tsana kenan yana magana a katse shi shiyasa na bari sai da ya tsahirta tukkuna gabana na dokawa na furta." Baban Saude Hauwa sharri ta yi mini wallahi tallahi ina ko'karin ganin na kiyaye shiga hakkinta wallahi Allah d'aya kenan ban san abinda yake tsakaninta da mijinta ba.
Bana ta'ba yarda ranar girkinta na 'kebe dashi na tsayin lokaci ko jiya ma ita ta gaya mini bashi da lafiya na hau domin duba shi kuma babu abinda ta same mu muna yi a zaune kawai ta same mu."
Ya furta." Na dai gaya miki ki kula idan har don kina ganin kin fi ta fada a wajensa kuke had'e mata kai har ku dinga shiga hakkinta ki daina domin ba ni so a ce ranar lahira kun tsaya a gaban Ubangiji ana yi muku hisabi yadda ta kira ni tana kuka haikan shine abinda ya daga mini hankali Amina kada ki zalinci duk matan da zai kawo gidanki, ki yi iyakacin bakin kokarinki wajen ganin kin fita hakkin kowa ki kuma nuna masa kuskuran abinda yake aikatawa.
Kada don kin samu dama a wajensa ki cutar da wata mu maza ba mu da tabbas watarana zai iya juyowa kan ki hakkin wad'anda ki ka zalinta ya fara bibiyarki.
Ko kin ta'ba jin an ce gaskiyar mutum ta k'are.
Idan kina da gaskiya da gudun hakkin wani sai ki ga kin zauna lafiya a duniya domin Allah ba ya shiri da mai zalinci.''
Ya kai k'arshen maganar da tausawa.
Na ce." In sha Allahu Baban Saude zan kula na gode sosai Allah Ya kara girma."
Ya amsa da "Amin Ya Allah."
Muka yi sallama.
Na ajiye wayar ina dubawa.
Lallai Hauwa bata da mutunci yau kuma abinda ta shiryo mini kenan.
Kayana kawai na zura zuciyata na tsalle na fita falon shiru ina d'an jiyo maganganun yara a d'akinsu suna shirin makaranta.
Na buga kofar dakinta da d'an karfi na ji tana fadin." Wanene?" Kai tsaye na ce." Ni ce"
Ta d'auki murya bata sake magana ba jim kad'an ta bude tana sanye da kayan bacci cotton riga da wando da hula.
Muka had'a ido ganin yadda fuskata take a murtuke ya sanya itama ta daidaita yanayinta.
Na ce." Daga yau sai yau kada jahilar k'wakwalwarki ta yi miki tunanin kiran wayar wani daga cikin alhalina ki kai masa 'karata Hauwa wai shin me na yi miki ne?
Ni ce matsalarki ko mijinki Hauwa? me yasa ki ka sanyo ni a gaba ki ke haka kan ki sukuni a kaina me na tsare miki na fad'a da babban sautin da kowa zai ji na ce.'' Yau sai kin gaya mini abinda na yi miki a gidan nan Hauwa ashe rashin mutuncin na ki har ya kai ki kira Baban Saude ki juya masa magana a kaina ni na yi mini ko mijinki da za ki nemi ki hada ni da iyayena."
Kada ki karanta wannan littafin ba tare da kin biya ba na kudi ne
Babu damuwa a tare da ita ta furta." Abinda ki ka yi mini a bayyane yake Amina tunda kin buk'aci ki sani ai zan gaya miki ko kin zata tsoronki nake ji ne?
"
Ta fito falon sosai ta tsaya daf da ni ta cigaba da cewa." Na gaji da wannan kisan mummuk'en da ki ke yi mini a gidan nan, na gaji shiyasa na sanar da Baban Saude tunda na lura shi kad'ai ne yanzu zai gaya miki ki ji kuma ba mazalinci ba ne, kin had'a kai da miji kun ware ni kuna nuna mini cewa ni ba matar gida ba ce.
Kin kanainaye shi da kissa kin hana shi yin mu'amula da ni, me yasa zan yi shiru a kan ki Amina ai ba ki isa ba wallahi dole ne na gayawa magabatanki."
Na ce." Banza shashasha sakarai kawai to kin fad'a kin ji dad'i duk yadda ki ke ganin Baban Saude ya ba ki goyon baya ba zai ta'ba ajiye ni ya d'auke ki ba, gaud'iya kawai wadda ba ta da lissafi."
Ba ta tsammaci wad'annan maganganun daga wajena ba ta tunzura ainun ta fara auno mini zagi manya-manya tana kusanto ni kamar yadda dai ta dinga yi wa Hajiya Maryam.
Masu aiki kaf dinsu da yaran suka fito suka tsaya muryarta ce kawai take tashi.
'Yar iska kawai ni za ki kira jahila wanda asali da nasabata ta fi taki.
Matsiyaciya na fa san tarihin rayuwar da ki ka gudanar a baya kafin ki yi tsalle ki shigo gidan nan ta karfi da ya ji kin dabaibaye mini miji ta ko'ina.
Amina ba tsoronki nake ji ba fa ki ka kara zagin.......Ba ta kai ga k
rasa maganar ba ya d'auke fuskarta da wani lafiyayyan mari.
Da yake ita kadai ce ba ta ga sakkowarsa tunda ta juya baya tana kallona tare da nuna ni da yatsa shiyasa ba ta ankara ba amma ni da masu aiki da yaran duka mun ga lokacin da ya sauko a ki'dime domin duk zurfin samansa sai da ya ji shouting dinta.
Ta dafe kuncinta a gigice tana nishi ta juya suka dubi juna ita da shi yanayin fuskarsa ya canza ainun da mugun takaici da b'akinciki.
Ya furta." Kin gani ko?
Hauwa idan na ce miki kece matsalar gidan nan ki ji haushi yanzu tsakani da Allah menene haka wace irin sakarai ce ke mara hankali da wayo tsokane mata ido za ki yi ne ko kuwa dukanta za ki yi ba ki duba abinda take d'auke da shi a cikinta a gaban yara kina ta zaginta me ki ke so ki nuna musu?"
Hawaye suka dinga karakaina a kumatunta tana fad'in." Ita ba ka ji zagin da take yi mini ba yanzu ban girmi Amina ba idan lissafi shekaru za a yi me ya sanya don ta zo a Uwargida nake mutuntata daidai gwargwado ita sheda ce har dakinta nake bin ta na gaisheta me yasa za ta kira ni da sakarai shashasha.
Kuma na zauna ina kallonta da kai da ita abinda kuke yi mini Ubangiji Allah yi muku fin sa."
Ya furta." Gaisuwar banza da wofi daga yau ki daina gaisheta tunda ba don Allah ki ke yi ba.
Duk abinda kuke yi ina hankalce kuma nasan halin kowacce daga cikinku rashin mutunci za ki yi mini a gida abinda nake ji yana faruwa a waje shine ki ke ko'karin wanzar mini da shi a gaban yarana.
Dame ki ke so su tashi ko su tasirantu, ke ba za a taba zaman lafiya dake ba ballantana na sanya a raina cewa ko bayan raina za ku had'e mini kan yarana su gaza banbance uwar da ta haife su.
Wata matsalar ki ke so ki samar mini da ita a gida ta zage-zage Allah Ya jikan Maryam duka tarbiyar da ta yi musu tare da goyon bayan wad'annan bayin Allan mai inganci ce tunda nake da yaran nan ban ta'ba jin wani ya yi mini zagi a gida ba saboda baki da mutunci ki tsaya gaban uwarsu kina zaginta akan wane dalili?"
Ta yi shiru tana kuka mai tsuma zuciya domin dai zahiri marin nan da ya taska mata a kumatu ya dakushe duk wani karsashi da 'kumajinta.
Ya dube ni rai a b'ace yana fad'in." Wannan ya zama na farko ya kuma zama na karshe Amina ba zan d'auki wannan shashacin ba.
Kada ku kuskura makamacin abinda ya sake faruwa da wannan safiya ya kara kasancewa.