← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 276

Sashe 29

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya juyo a razane a lokacin ni kuma na yun'kura na tashi duk da ciwon da jikina yake yi mini hakan bai hana ni tunkararsa ba.

Da sauri ya bude kofar ya fita dan yadda ya nuna mafisar ta ishe shi haka in ba haka ba ya tsaya mu yi mana.

A baranda na riske shi don bai kai ga sauka ba.

Na ri'ke shi ta baya kamar mai shirin yin kokawa.

Zuciyata sai tunzura ni nake yi, na rasa wane hukunci zan yi masa kuka kawai nake yi na ri'ke shi katamau!

Hankalin Hajja da Anti Yagana ya yo saman domin gunji nake yi ba kad'an ba.

Shi kuma duk ya diririce!

Sai kamo ni yake ko'karin yi yana cewa." Ki bi fa komai a hankali, kin ga an yi ne? da za ki tayar da hankali, ni dai ban cuceki ba."
Ganin Hajja tana nufo benan na fara cewa." Don zaka yi aure sai ka sanya ni a gaba kana zagin ubana, me ya yi maka?

Ina lefinsa da ya haife ni, ni ka zage ni mana amma ka daina ambato sunan mahaifina kana zagi ai bai nema a wurinka ba, a wurin Allah yake nema, wallahi Hajja na gaji ba zan iya ba." Na k
rasa maganar da kuka mai karfin gaske....

Hajja ta dube shi da mamaki a tare da ita ta.

Kafin ma ta furta wata kalma anti Yagana da take ta jefo mini harara ta ce." To idan auran zai yi ai ba za ki hana shi ba, wane irin wulakanta kai ne wannan Amina." Hajja ta ce.'" A a Yagana a yi magana ta hankali mana, iyaye ai ba abin wasa ba ne, kina jin fa abinda ta fad'a."
"Wallahi tallahi idan duk jikina kunnene ba zan yarda da cewa ya zageta ba, Hajja na san halin kayata."
Hajja ta girgiza kai tana dubansa ta ce." Tajo ashe aure za ka yi ba labari."
Yar dariya ya yi irin ta takaici yana ko'karin cire rigarsa dake ri'ke a hannuna ya ce." Ban tashi yin ba dai kawai ta ji muna waya da Hauwa shine ta daga hankalinta.

Sai ta dube ni tana dan murmushi wanda na kasa tantance ko na menene ta ce." To ki yi hakuri kin ga kina tare da lalura, kishi a yanzu ba na ki ba ne, fatan mu dai ki sauka lafiya."
Sai na yi kasa'ke ina kallonta.

Anti Yagana taja tsaki ta bar wurin na san haushina take ji kan abinda na yi.

Ganin haka sai shima ya silale Ina kallonsa ya sauka da saurin gaske.

Hajja ta fara rarrashina akan na nutsu kada na daga hankalina tunda ai banga an yi ba.

Sai a lokacin kunya da nauyin matar suke kama ni.

Idan na ce zan yi irin wannan dibar albarkar to zahiri zan bata kwa'bar da na yi.

Hakama ina shiga d'aki anti Yagana kamar ta dake ni tana cewa.

Wallahi kada ki bari ki kai mutanan nan karshe Amina, in banda rashin mutunci da samun wuri ina ruwanki da shiga lamarinsa da 'yan uwansa, idan auran ma yace zai yi menene abin damuwa, mutumin da bai tauyeki ba shine zaki tona masa asiri har da cikwukwuye masa riga saboda kawai kin ga suna sonki, ko kuwa sa'anki, babba dashi irin haka, waye ya gaya miki yanzu ana irin wannan kishin na hauka, ba ki ta'ba ban haushi ba irin yau wallahi.

Na nemi gefan gado na zauna jikina a sabule hawaye na silalowa daga idona na ce." Anti Yagana zagina fa ya yi wai don ubana, ina ga duk rikicin da za mu yi dashi idan cin zarafin iyaye ya shigo sai inda karfina ya kare wallahi."
"Bango ki ka kaishi, ai tunda na zo gidan ina fuskantar irin zaman da kuke yi, wasu lukutan kamar kece kike auransa abinda kika ce shi za a yi, dama ai mai ha'kuri bai iya fushi ba.

Na ja hanci raina na cigaba da suya domin na gama fahimtar cewa anti ba zata saurari uzuri na ba, kuma har yanzu ta kasa gane abinda nake ji a zuciyata game da maganar Hauwa.

A dake ka kuma a hanaka kuka. na kwanta kusa da Hadiza da take ta bacci duk maganganunmu bai sai ta motsa ba, anti ta cigaba da maganganu tana fad'in.

" Ina ce ba daga gidan kishiyoyi ki ka fito ba, Alhaji Muntari wannan bagidajen mutumin ba matansa biyu ba, kece fa ta uku kin san ba kya son kishiya me yasa ki ka aure shi, sai wannan saboda kin fahimci lagonsa akanki kike dabdala a kansa.

Wallahi ki ki yayi fushin irinsu, kuma idan ki ka ce ta irin wannan salon za ki dinga nuna kishinki zaki fice masa daga rai.

Ko waye ya gaya miki anayi wa namiji irin haka ya cuceki idan zaki farka ki farka."
Cikin kuka na ce." Anti Yagana don Allah ki kyaleni haka ba ki san abinda nake ji ba ne, shiyasa kike yi mini wannan maganganun lamarin bai zo kanki ba ne."
"To shikkenan ki yi mini rashin kunya don na gaya miki gaskiya ba sai kin kara ganina a gidan naki ba, duk abinda za ki yi, ki je ki yi rayuwarki ce, ke za a yi ta lissafawa aure, ace kowane d'a da ubansa."
Hawaye ya kara shararo mini shiru na yi mata ban sake cewa komai ba.

Ita tunda ta ce haka ba ta sake wata maganar ba, ta fita falo wajen Hajja.

Ko'karin daure zuciyata na yi duk da abinda yana sasakata ban nuna ba ina so mu rabu lafiya don ganin yadda take ta jin haushina tana fushi da ni, na dinga bata ha'kuri har sai da huce tukkuna, na hada mata abubuwa masu yawa da kudi haka ma maigidan dubu dari biyu ya bata wai ta sayawa yara alawa.

Koda zata ta tafi kasa daurewa na yi kuka na dinga yi haik'an! kamar 'kan'kanuwar yarinya Ita kam bata wani nuna alhini a zahiri ba amma dai na san cikin zuciyata tana jin rashin dadi.

Ina kallo su Hadiza da Yusi suka tafi rakata filin jirgi, ni kuwa ya ce na zauna kawai a gidana.

Haushinsa ya kara nauyi a zuciyata.

Ita kanta Hajja sai da ta goge kwalla domin gaskiya sun shaku sosai da Anti Yagana.

Duk yadda na so da na manta da abin kasawa na yi domin sai nake ganin kamar ni ya takewa hakki.

Akwai cin fuska a cikin abinda ya yi mini, dalilin ma da ya sanya kenan na yanke shawarar akan ba zan sake lamunta yayi waya da wata mace a cikin gidan ba koda kuwa ma'aikatansa ne.

Idan har yana so ya zauna da ni lafiya.

Ni ba namijin da zan zauna ya zagi Ubana gobe kuma na washe masa baki wallahi sai na nuna masa kuskuransa ba ruwana da kudi da shekarunsa iyaye ba abin wasa ba ne.

Tare nake zaune da mahaifiyarsa ban ta'ba gaya mata bakar magana balle har na dubi tsabar idonsa na zageta.

Ubana bai yi masa komai ba, ba kuma zan yarda ya saba da zaginsa ba ai kud'i ba hauka ba ne.

Sati biyu babu jituwa a tsakanina domin duk yadda ya so da ganin mun shirya naki bashi fuskar hakan.

Gaisuwa ce kawai take hadamu idan na sako daga samansa ba na sake komawa sai wata safiyar ina kula sosai domin kada Hajja ta fahimci akwai matsala a tsakaninmu.

Tun yana rarrashina har dai ya ha'kura ya zuba mini ido.

Muka cigaba da zama a hakan.

Ranar wata lahadi na tashi da ciwon kwankwaso domin tunda cikina ya shiga wata na bakwai nake jin sauye-sauye a tare da ni. ji nake yi kamar haihuwar fari don ba karamin wahala nake ci ba.

Da kyar na yi wanka na zura jallabiya wajejen takwas da kwata na nufi saman nasa.

Na same shi yana ta waya na zauna na yi kasa'ke ina sauraransa ya kammala ya dube ni.

Uffan bai ce mini ba.

Na turbune fuska da kyar na ce." Ina kwana.''
Ya yi mini shiru bai amsa ba."
Na ja hanci takaicinsa kamar ya kashe ni domin dai na fahimci da Hauwan yake magana da sassafe 'yar iska ko uban me take gaya masa oho."
Na ce." Wai me kake jira ne kai ba yaro ba haka zalika itama ba yarinya ba tsohuwar guzuma ce fa ko yau a d'aura muku aure sai muga k'aryar wayar sassafe."
Babu sukuni ya ce." Saurin me kike yi madam an kusa in sha Allahu rabbi."
Sai na ji kamar ya soka mini mashi a wuya.

Na ja tsaki tare da kawar da kaina gefe."
Ya ce.'" Wai ke daman haka ki ke ne, ba ki da kunya?"
Shiru na yi ban ce masa komai ba."
Ya sake girgiza kai a karo na biyu ya furta." Ba tsoronki nake ji ba, kuma duk take takenki na gane wallahi ba zan rabu dake ba dan zan yi aure, kuma zan fito miki da asalin kalata tunda baki da mutunci."
Hawaye suka 'kwace mini na ce." Ni ce ma ba ni da mutunci ko?

Wallahi idan kuwa kana son zama da ni cikin salama sai ka bi dokokina domin kuwa ba zan zauna ka dinga raina mini hankali ba.

Ka zage ni ka zagi Ubana akan wane dalili.

Ni bana asiri amma zan had'aka da Allah idan har rabuwarmu itace alheri Allah Ubangiji ya tursasaka ka ba ni takardata.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.
Chapter 29 · 0% Book details