← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 276

Sashe 124

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba na yi maka kallon masoyi."
Ya jima yana kallona kafin ya gyad'a kansa ya nufo ni, na kuwa zabura domin kallon dodo nake yi masa na ce." Kada ka zo inda nake na rantse da Allah zan illataka."
Bai daina tafiya ba har sai da ya cimmani zai ri'ke hannuna na fizge da sauri na wancakal da nasa hannun cikin zafin nama na yi wajan madubina na zari wata doguwar kwalba ta turare na ri'ke a hannuna.

Ya sake nufo ni yana fad'in." To illatani kin ji, na ce ki illatani tunda kin 'ki tsayawa mu fahimci juna.

Da k'araji na ce." Har abada na sake aminta da maganar munafiki."
Ya 'bata fuska ainun yana fad'in." Kada kuma ki wuce gona da iri, kin naushe ni a ma'karfafata d'azu na kyale ki yanzu kuma kina kira na da munafiki ranki zai b'aci fa ba ni son rashin hankali."
Na ce." Ya 'baci ma ai ba tsoro nake yi ba, menene karshen hukuncin shine saki ko to ka sake ni kaga yadda ake liyafa ai ni kassara mini rayuwata ka yi zama dakai bai amfanar da ni komai ba."
Ya kuwa 'kadu da wannan furucin ya ce." Har yaran da muka haifa ba su da amfani?" Na ce." E, ai ba nawa ba ne tunda ka d'aukesu ka bawa bushshiyar matarka nata ne taje na bar mata."
Ya dinga kallona da mamaki mai yawa kafin ya sake tunkaro ni a karo na biyu na daga abinda yake hannuna zan buga masa ya yi saurin ri'ke hannun tare da k'wacewa.

Muka yi cirko cirko a tsaye shima nishin yake yi kamar yadda nake yi kamar wanda ya yi tsere.

Mun jima haka ya ri'ke ni katamau na ja tsaki tare da yun'kurin bangaje shi ya riko kafadata jikinsa duk ya yi la'asar.

Na ce ka cika ni na gaya maka
na rantse da girman Allah da Annabi sai yaran nan sun bar hannunka tunda ka gaza ri'ke su tsakani da Allah ko da hakan zai yi sanadiyar rabuwarmu
"Ba ki da hankali har yanzu ko Amina?"
Na ce." E, ba ni dashi tunda kai din shine da kai." Murmushi ya yi ya girgiza kansa yana fad'in." Ke kam kin ci sa'a ina sonki ina ga da babu wannan da tuni mun rabu baram-baram, iskanciki da rashin kunyarki ya ishe ni.

Yanzu ni ne mara hankali Amina baki da kunya ba ko."
Juyar da kaina gefe na yi ban ce komai.

Sai ya girgiza kansa a nutse ya fara ko'karin jan hannuna yana fad'in." Zo mu je mu zauna domin mu tattauna."
"Ba zan zauna ba domin ba ni son had'a numfashina da kai." Na fad'a tare da buge hannunsa da yake jana.

Sai kuwa ya sanya mini karfi ban ankara don kamar tanka'dani ya yi na fadi a da'bas a wurin.

Kafin na yun'kura na tashi ya cimmani ya sake tura kirjina da k'arfi na kwanta kaina ya tallafo kawai yasa bakinsa a nawa ya dinga d'ura mini yawun bakinsa ba don ya ji dad'i ko don na ji yake kiss din bakina ba domin ya sanya mini yawunsa ne.

Tsayin minti hud'u zuwa biyar ya cire bakinsa tare da tashi tsaye ya tsaya a kaina yana kallona idonsa ya kada sosai da tsantsar tashin hankali a cikinsu.

Na tashi zaune hawaye masu d'umi suna silalowa daga idona.

Kamar mai koyon tafiya haka na dinga jan k'afa ina kuka na isa gefan gado na zauna kamar an kwad'e mini gwiwata da tabarya lallai Allah Ya jarrabeni da shu'umin mutum.

Ya biyo ni shima kamar wanda aka kuzawa ruwan sanyi jikinsa duk a sanyaye.

Yana zama a gefena na yi kukan kura cikin wani yanayi na bazata na sake kai masa naushi a kirjinsa ya kuwa yi kwanciyar da bai shirya ba na zabura da sauri na d'auki fillo na raba k'afafuna akan ruwan cikinsa na danna masa fillon a hancinsa ina ihun nake fad'in." Sai na kashe ka wallahi, na yarda ni ma a kashe ni, ni ce ajalinka tunda ba zaka bari na huta ba."
Fad'a sosai muka dinga yi tiki tiki yana yun'kurin tashi ina sake turmushe shi nauyina gabad'aya na saki a kansa ina kuka.

Cikin tashin hankali da nishi tare da fitowar numfashi ya fizge a guje ya dira daga gadon yana kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!

Bai fita ba yana tsaye a bakin kofar d'akin ya ki'dime sosai ko da ya ga na sake durfafoshi bai yi yun'kurin bude kofar ya fita ba.

Ina isa kuwa ya kama ni da karfin da ban san yana da shi ba.

Cikin rawar murya da tsananin damuwa yake fad'in." Yi ha'kuri, ki yi hakuri na ji na yi lefi, amma ki fahimce ni ki bari na gaya miki abinda yake zuciyata kafin ki kashe ni din."
Na yi shiru hawaye na fita daga idona, ina jan hanci na ce ." Wallahi ba zan sake yadda yarana su zauna a hannunka ba" Ya ce."
" Ki fahimce ni Amina, ban za'bi bangare daya na ajiye daya ba.

Ni kaina lamarin ya sanya ni a rud'ani ba kad'an ba.

Shirun kuma da na yi ba ina nufin na goyi da bayan maganar Salim ba.

Ina bincike ne da kuma hanyar da zan kawo gyara.

Akwai nauyi mutuka da gaske na tunkareki da maganar nan.

Akwai kunya na titsiye yaron nan Kamalu ina neman hujja akan maganar Salim.

Kada ki zarge ni bayan ba ki san menene a zuciyata ba.

"Na gaya maka wallahil-azim ba zan yarda da kanzon kurge ba.

A wannan ga'bar ko ni ko kai, Kamalu da Yusi fa ba su rasa madogara ba.

Sannan Ubansu ba makwad'aici ba ne, ba mazinaci ba ne, sannan ba b'arawo ba ne.

Banga dalilin da zai sanya a dinga jingina musu manya manyan sharri ba.

Ban nemi ka rike mini yara ba.

Haka zalika ma ban nemi matarka ta ri'ke mini yarana ba.

A ba ni kayana mana dole ne, zan iya rikesu mu rayu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali."
"To ni kuma muddin a karkashin ikona ki ke yaran nan babu inda za su je muna tare har abada, tunda ina tare dake ni ba zan iya rabuwa dake ba."
Na dube shi ina gyada kaina na ce." Haka ka ce ko?''
"Kwarai kuwa, haka na ce, sai ki yi duk abinda za ki yi tunda ke ba za ki rarrasu ba.

"Zan kuwa yi, ai ba kai ka haifar mini su, baka da wani ji'bi dasu don haka baka da hujjar da zakace dole sai ka rikesu anan zan nuna maka karfin ikona."
Ya ce." Sai ki nuna din ina jiranki..'' Daga haka ya cika ni tare da jan tsaki ya juya ya fita yana fad'in." Sakarai kawai kullum kina girma kina cin tasono."
Silalewa na yi a k'asan d'akin na yi zaman dirshan na dinga tikar kuka.

An dake ni an hana ni kuka kuma an bi ni da bakar magana.

Wace irin masifa ce wannan mutum bai haifi yara ba ya ce lallai sai ya rike su.

Ina cikin wannan yanayin Hauwa ta shigo sanye da hijabi a jikinta idonta jawur!

Na tashi tsaye da sauri Ina kallonta gabana na fad'uwa.

Minal ta dire mini a gabana tana fad'in.'' Ga takwararki nan Amina ubanta ya ce na tafi gidanmu."
Cikin kad'uwa da muguwar fargaba na ce." Ki tafi gidanku akan wane dalili Hauwa?"
"Saboda na gaya miki abinda yake faruwa." Ta fad'a tana juyawa da niyyar fita.

Na bita da sauri yayin da Minal din ta tawo kataf katafi ta rike gefan hijabinta tana kuka.

Na ce." Shine kuma ke sai ki tafi."
"To dama ai kamar akan 'kaya nake wallahi na gaya miki a gajiye nake." Na ce." Ita Minal din mai tayi miki to?"
"Cewa ya yi na ajiye masa yarinya."
Wani takaici ya yun'kuro mini lallai Alhaji Amadu ya mutu ya bar baya da k'ura.

Iyalinsa na nema su tarwatsawa aminin nasa rayuwa.

Na tabbatar da cewa ba kowane ya janyo wannan hayaniyar ba sai Salim.

Na ce." Yana ina maigidan?"
"Shi ya sani.'' Ta fad'a a takaice tare da sake nufar hanyar fita.

Na ri'ke hannunta ina fad'in." Babu fa inda za ki je Hauwa."
Dariya ta yi irin ta takaici ta ce." Ai ba ke ki ke aurena ba Amina, maigida ya ce na fitar masa daga gida zaman me zan yi."
Jan hannunta na yi muka zauna kan gado na dau'ki Minal na d'ora mata a cinyarta sannan na d'auki wayata.

Kiransa na yi bugun farko ya d'aga kamar yana jira.

Littafin nan na kudi ne Hajiya kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba
Na ce." Yanzu kai don girman Allah ba ka ji kunya ba, tsofai tsofai da kai kake aikata irin abun yara?"
"Mai na yi kuma?

Ke ba kya jin nauyin furta mini maganar da duk ranki ya so ko Amina?''
Na ce." Hauwa dai ko babu aure tana da 'yancin zama na dindindin a gidanka, to balle bayan wannan alakar akwai ta aure da zuria a tsakaninku, da ka ce ta tafi gida kai ba ka ji nauyi ba?"
"Bata da wani 'yancin zama a gidana sai na so, tunda ba ta ji nauyin shure maganata ba, ni ma babu wani nauyinta da zan ji, kuma ina ruwanki matarki ce?"
'Dan sassautawa na yi domin kuwa ba zan so a ce dalilina sun samu matsala ba.

Na ce." Idan saboda ta gaya mini wannan maganar nan ya sanya har ka yanke mata wannan hukuncin ka yi hakuri ka ji."
Shiru ya yi bai ce uffan ba.

Na ce." Ka janye abinda ka kudirta akanta domin kuwa sam bai dace ba."
"Kin yarda ta yi ba daidai ba yanzu?"
Shiru na yi ban ce komai ba.

Ya sake maimaita maganarsa nan ma ban ce masa komai ba.

Ya ce." To tunda bakinku daya kin ga kuwa babu amfanin zama da macan da bata buk'atar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Chapter 124 · 0% Book details