← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 276

Sashe 136

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*TALLAH*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BieW3hHvRNIJLFNloG2CDl
Momyn Hajara GHT supplements
Muna da kayan gyara jiki na maza da mata munada magungunan matsalolin ma'aurata munada magungunan kowacce irin matsala in sha Allah
Hadin Amare
Hadin Ango
Hadin jego
Hadin uwar gida
Hadin babbar mace
Hadin maida tsohuwa yarinya
Muna da Maganin sanyi kowanne iri
Muna da maganin ulcer
Muna da maganin Asthma
Muna da maganin ciwon zuciya
Muna da maganin ciwon Hanta
Muna da Maganin hawan jini
Muna da Maganin ciwon Ido
Muna da Maganin rashin haihuwa
Muna da Maganin skeler
Muna da Maganin kowacce irin cuta da yardar Allah
Sannan kowa zai iyayin register da campanynmu maitarin albarka kasari kaya kasiyar kaci riba sannan Kuma campany yadunga biyanka albashi Duk watan da kayi aiki
Saida kaya shine aikin da zakayi campany ya biya
07012621175
Register 8000 n
*93*
"Maganar
Hauwa ai bata shafe ki ba Amina don haka babu ruwanki wannan tsakanina da ita ne kawai tunda ta ce ba ta ji to sai mu zuba ni da ita shege ka fasa."
Ya fad'a yayin da yake sake janyo ni jikinsa.

Na janye a hankali na ce."Ya zaka ce babu ruwana bayan kai ma kasan a saboda ni da abinda ya shafe ni kuka samu sa'ba ni har da rabuwa ai gaskiya ba zan iya yin shiru ba domin abinda ka yi bai dace ba.

Kamar yadda take ha'kuri da kai ya kamata ace kaima ka yi hakuri da halayenta ai zaman auran kenan."
"To yanzu ya ki ke so ayi?"
Ya fadi hakan cikin 'kosawa da maganar domin gabad'aya yanayinsa ya nuna ba itace a gabansa ba.

Na ce." Ka mayar da ita tunda ciki ne da ita sanin kanka ne a musulunci babu kyau sakin mace da ciki, kuma idan Hajja ta ji hakan ranta ba zai yi mata dad'i ba gaskiya."
"Ai ita Hauwa ba ta duba haka ba Amina, kuma cikinku wallahi kada wadda ta kuskura ta gayawa Mahaifiyata akan hakan rai zai 'baci."
"Ai kai zaka gyara matsalar gidanka kafin ta fita waje idan ba ka so Hajja ta ji abinda ka yi sai ka yi gaggawar gyara kwabar da ka yi."
Ya 'bata rai yana fad'in." Kina so ki ba ni umarni kenan?"
"Ba umarni ba ne ban isa ba, shawara ce nake ba."
"To ba zan d'auka ba har sai kun je ke da ita kun bawa Maryam da 'yar uwarta ha'kuri akan abinda ku ka yi musu.

Na rashin kyautawa."
Ido na zuba masa ina kallonsa da mugun takaici.

Na gyada kaina tare da janye idona daga kansa ban ce komai ba..

Sai ya cigaba da ce wa." Wannan shine kawai, ki ja ta tunda tare kuke kulle-kullenku sai ku je ku ba su ha'kuri domin mun yi magana da Nabila ce wa gobe za ta koma jos, to kafin ta tafi din sai ku gyara kuskuranku, ni kuma sai na mayar da ita dakinta."
Na juyo fuskata a d'aure " Wannan kuma shine ba zai yiwu ba, idan hakurin da ka ba su bai isa ba, shikkenan don Allah ka cikashewa Hauwa sauran igiyoyinta da suka rage, idan hakan ma bai yi maka ba sai ka had'a har da ni gabad'aya."
Ya ce." To kada ki sake yi mini magana akan abinda ya shafi tsakanina da Hauwa, ba ke ki ke auranta ba, ni ne babu ruwanki wannan shine maganarmu dake ta k'arshe akanta."
Na dinga kallonsa zuciyata na sake suyuwa da kutun takaici da b'akinciki.

Wannan wani abu ne da zai yi masifar wahala a ce Hauwa ta je ta bawa Momi da Nabila ha'kuri saboda iya zaman da na yi da ita na gane cewa macace mai mugun girman kai da kifad'i, ga taurin kan tsiya, bai shirya kwantar da rikicin ba, domin da ya shirya mutuwar matsalar ba zai 'bullu da wannan abinda ya san lallai da wahala ya yiwu.

Jin an kira shi a waya ya sanya na tashi na fita daga d'akin ba tare da na sake cewa komai ba, matsalarsu ce can ta family iyakacina shawara, kuma ni ban tura Hauwa cewa ta yi abinda take yi ba, akan kanta take yi saboda wata manufa tata da kuma masifar kishi, duk wanda zai zarge ni da hannu akai ya d'auki hakkina.

Ba zan sake cewa masa komai ba.

Bai kwana a gidan ba a ranar sai washe gari wajen daya da rabi ya shigo cikin kayan shan iska da cazbaha a hannunsa ga dukkanin alamu daga massalaci ya fito mabiyin sunnah ne sosai da zazzafar akida da rashin son bidi'a da yawa.

Bai fad'a ba amma tuntuni na gane ce wa mugun dan izala ne tunda yawanci abokanshi larabawan nan na madina duka 'yan ahalissuna ne.

Muna falo duka a zaune ya shigo ya d'an tsaya ana gaisawa ya amshi ta kowa a d'an sake.

Ina kallon Hauwa bayan sun gaisa ta tashi a sanyaye ta shige daki.

Sai na ji wani iri a raina, na yi shiru tare da yin k'asa da kaina ina jin suna ta labari da Baba Tabawa kamar yadda suka saba.

Ya jima a tsaye a wurin suna magana ban tofa tawa ba.

Kafin ya haura samansa.

Baba Tabawa ta juyo tana kallona da wani yanayi na alhini da damuwa ta ce." Irin wannan matsalar nake ta guje muku faruwarta Amina, rayuwar nan gabad'ayanta 'yar ha'kuri ce, shi namiji yana fa da wani irin iko da damar da Allah bai bawa mace ba, yakan iya yin komai ya kwana lafiya amma ita mace za ta yi abin ya zame mata matsala gagarima, ita wadda kuke ta ha'kilon akanta tana can hankalinta kwance mijinta ya kar'bar mata rigimar tunda ai kun had'e mata kai, ai ta fi ku wayo ta kuma fi ku shekaru da gogewa ta yaya ko tana da laifi zai gani bayan koyaushe cikin nuna alherinta take.

Ki duba ki gani cikinku babu wanda ya fi kusanci dashi sama da Hauwa amma yau an wayi gari tana wasan 'buya da shi.

Shi kuma ko a jikinsa bai damu ba, ya kamata a ce ku nemi sulhu ita Hauwa ta kar'bi kuskuranta tunda a bayyane yake ta yi ba daidai ba."
Murmushi na yi irin na rashin sukuni na ce." To Baba Tabawa ya za a yi ne, mun jima muna magana dashi jiya da daddare abinda ya tsiro dashi ne nake ganin da wahala ace ya yiwu nasan Hauwa sai dai a rabu akan ta je ta ba su ha'kuri abinda ya ce kenan muddin tana so su daidaita ta je ta bawa Momi ha'kuri da k'anwarta Nabila akan zagi da 'kaharun da ta yi wa iyayensu, ni kuma nasan halin taurin kanta da mugun kifad'i."
Ta gyada kanta cikin damuwa tana ce wa." To ke dai ki yi takatsantsan sosai, amma a shawarce ina ganin ta bi umarinsa kawai domin zahiri mijinku ba irin wanda ake tursasawa ba ne ko kuma mace ta juya shi.

Na ce." Mu dai ba za mu juya shi ba.

Amma ai matarsa da yake tare mata fad'a juya shi take yi kamar waina a tanda idan ba haka ba menene dalilin da zai sanya ya saki matarsa a kanta uwar babban dansa namiji kuma yar uwarsa.

Baba Tabawa ki dubi lamarin nan fa da kyau!"
Baba Tabawa ba ta kai ga magana ba kiransa ya shigo wayata da take ajiye a gefana.

Ina d'agawa ya ce." Ki zo yanzu." Bai bari na ce komai ba ya datse kiran.

Na yun'kura na tashi da wayar a hannuna ina fad'in.'' Baba bari na sauko sai mu cigaba da tattauna maganar da muke yi."
Ta ce." Shikkenan a sauko lafiya."
Ina hawa saman gabana ya fadi ganinshi zaune daga shi sai karamin wando na ciki ya cire kayan dake jikinsa.

Kallo daya na yi masa na d'auke idona domin lokaci guda na fahimci menene a cikin kwayar idanuwansa.

Gabana bai daina bugawa ba har na isa inda yake zaune.

Na zaune zuciyata cike da zullumi da damuwa.

Ya ce." Za mu sake gaisawa ko?" Kallonsa na yi cikin nauyin baki na ce." Ai mun gaisa da ka shigo.

Ya kamo hannuna yana duba yatsun kafin ya rintse da nasa ya hade yatsunmu wuri d'aya a hankali ya ce." Wata kalar gaisuwa na zo miki ta mussaman kamar yadda kike ta mussaman a wurina."
Shiru na yi tare da yin k'asa da kaina.

Wai dadin baki zai yi mini da kalamai saboda yana so ya kwanta da ni
, tun jiya na gama gane inda ya dosa.

Na fara jin cikina yana murd'ewa domin ban san ta yadda zan sanar dashi cewa cikin nan fa ya sake ficewa ba.

"Kuna da abinci ko, domin ina so na cika cikina kafin na wani lamari mai girma ya faru a tsakaninmu."
A hankali na ce." Da abinci Baba Tabawa ta yi sai dai ba irin wanda kake so ba ne jallop din taliya ne da kifi.''
Ya d'an sake rintse hannuna dake cikin nasa a karo na biyu yana shafa mini tsakiyar hannu
ya ce." Gaskiya kam ba irin nawa ba ne, amma in dai da zafi a ba ni zan iya ci a haka."
Na ce." Da zafi mana tunda a kula yake." Hannuna nake ko'karin cirewa daga cikin nasa ya rike yana fad'in." Wai ke ba kya yin irin 'kunshin nan ja da 'baki zai yi mini kyau domin kina da kyawun fata ina so a dinga yi mini."
Shiru na yi.

Ba tun yau ba na fahimci yana son lalle sosai, ni ce dai ban mayar da hankali ba, amma na lura matarsa Momi tana yawan yi.

Amma henna ake yi mata a kafafu da yatsun hannuwanta.

Ya ce" Akwai wata yarinya dake yi wa Maryam zan sanyata ta turo muku ita sai ta yi muku."
A takaice na ce." Sai ta zo.

Ya bi bakina da kallo yana lumshe Ido.

Wani irin yanayi na ji a jikina amma nan da nan na shiga taitayina domin na fi kowa sanin cewa matsala ce kwance-kwance.

Cikin 'yar damuwa na ce." Na kawo maka abinci ne?"
Ya girgiza kansa alamun a'a.
Chapter 136 · 0% Book details