← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 276

Sashe 152

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya gyada kansa "Wallahi ni kaina na kad'u Amina na tausaya mata k'warai da aniya yanzu haka za mu yi booking domin zuwa india akwai kwararrun likitoci a can da za su caje mini ita sosai."
Jiki a masifar sanyaye na furta." Tabbas Ubangiji shi yake saukar da ciwo ya kuma saukar da maganinsa, ina yi mata fatan alheri tare da addu'ar samun lafiya madawamiya, kai kuma Allah Ya baka ladan jinya."
Ya sake amsa da "Amin Ya Allah." D'akin ya d'auki shiru har yanzu hannunsa na saman kirjina yana dan tattabawa.

Ban hana shi ba kawai dai ina mamakinsa ne a ganina yanayin alhinin da yake ciki da damuwa akan rashin lafiyar maid'akinsa bai kamata a ce wani abu na jin dad'in duniya yana bijiro masa ba, to mai ma zai fahimta bayan yana cikin tashin hankali a haukana fa kenan
Na dube shi yana lumshe idonsa kamar wanda ya samu audiga na dan ture hannun nasa muka kalli juna a sa'rke na ce." Dama ina son magana da kai."
Kai tsaye ya furta." Idan har akan zuwa maiduguri ne to kada ki bata bakinki babu inda zakije....

Na kudi ne littafin don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Na ce." To saboda me, kafi kowa sanin matsayin anti Yagana a wurina ko?"
Ya gyad'a kansa a tsanake ya ce." Da dai ban rantse ba ne sai na bari ki je, amma wallahi na riga na rantse ki
yi hakuri bayan bikin sai ki je ki ga d'akin amarya."
Zuciyata ta dinga tiriri na dinga danne abinda yake yun'kuro mini domin ba ni son na nuna masa damuwata a kan haka a gaba ya samu abinda zai k'untata mini idan wata matsalar ta faru a tsakaninmu.

Na gyada kaina tare da furta." Shikkenan mu ajiye wannan maganar ina so ka gaya mini matsayin zamanka da Hauwa a gidan nan, domin ni har yanzu na kasa gane abinda kuke nufi da kai da ita."
Ya dube ni sosai kafin ya ce." Ke ina ruwanki kuma?"
Na ce." Ni ce kuwa nake da ruwa tunda duk wata mas'ala da kuka samu da kai da ita a kaina ne, yanzu a matsayinka na babba mai hankali da jagoranci abinda kuke aikatawa daidai ne."
Ya ce." Ai taki ta amince da cewar ta yi lefi, sannan taki ta bi umarinina idan tana so magana ta shige mai yasa bata biyo ki zuwa duba Momi ba.

Ta cigaba da zama a haka duk ranar da ta gaji sai ta nemawa kanta mafita."
"Gaskiya hakan ba daidai ba."
Ya 'bata rai yana fad'in." To nuna mini daidai Amina."
Shiru na yi ban sake magana ba.

Ya ja tsaki yana fad'in." Na yabe ki sallah za ki kasa alwala, Hauwa ai ba yarinya ba ce idan tana son zama da ni ta ba ni ha'kuri ta kuma bi umarina."
Na ce." To ai kaine babba ha'kurinka shine zai fi rinjaye."
"Na yi iya wanda naga zan iya yi a kanta Amina, wannan ya zama na farko ya kuma zama na karshe, kada ki sake titsiyeni akan lamarin Hauwa ko ni din sa'anki ne?"
Shiru kawai na yi Ina kallonsa.

Ya cigaba da ce wa." Dangane da maganar kwanan aure kin ga Momi bata da lafiya ya kike ganin za a yi?"
Na ce." Yadda muke yi mana."
Sai ya yi shiru yana tunani kafin daga bisani ya furta." Shikkenan sai a cigaba da tafiya a hakan, zan kwana biyu ban koma legos ba, domin idan na kai ta asibitin na dawo zan dan jinyaceta."
Uffan ban ce masa ba, ya tashi tsaye yana kallona cikin sigar kulawa ya furta." Ki same ni a sama zan shiga in yi wanka." Ban iya ce masa komai ba har ya fita daga d'akin Ina zaune zuciyata ta kasa tsayuwa wuri d'aya.

A daran na gurzu a hannunsa k'warai da gaske kamar wata sabuwar amarya sai da na yi ruwan d'umi domin kusan sau uku ya yi mu'amula da ni.

Farkon dare da asuba bayan ya dawo daga sallah.

Still Yana gama breakfast nan ma ya sake yin wani haka na sauko daga saman a galabaice.

Na yini ciye ciyen kayan da zasu saukar mini da ni'ima domin na tabbatar da cewar a wannan daran ma ba zai daga mini kafa ba..

Bayan kwana biyu da misalin biyar na yammar ranar talata muka yi ba'kuwa a gidan.

Hajiya Aziza sunanta matar abokinsu ce Alhaji Sulaiman duk dai abotar tafi karfi tsakaninsa da Alhaji Amadu mai rasuwa dalili shi da girmansu suka hadu ba abotar kuruciya ba ce.

Sai bayan rasuwarsa tukkuna abotar ta maye gurbi akan shi da yake ba ni labari.

Uwargidansa ce kuma tare suke da maigidan sun zo duba jikin Momi ne tunda ko bayan rasuwar Alhaji Amadun suna yin zumunci dalilin da ya sanya ma kenan Alhaji Sulaiman din yake binbinin abotartasu ta yi karko kamar yadda ta yi da Alhaji Amadun.

Shigowarta kenan ya kira wayata ya yi mini wannan bayanin wai ta ce za ta shigo ta gaishe mu kafin su tafi yanzu shi suna tare da maigidan nata a can gidan Momin.

Na ce masa in sha Allahu babu matsala.

Sosai na marabceta na sanya Baba Tabawa ta kawo mata abinci tana fad'in a 'koshe take ta ci abinci kafin ta fito nace ta daure ta sanya mini albarka.

Hauwa ta fito suka gaisa sama-sama cikin rashin sakewa ta koma dakinta.

Na kira Baba Tabawa domin ta zo ta kwashe kayan abincin da ta jera wanda kad'an ta ci daga ciki.

Duk da babu sabo a tsakaninmu amma na lura tana da kirki kuma ta girme mu gaskiya zata iya yin sa'a da Momin ina tambayarta yara ta ce suna nan lafiya biyu suna d'akin mazajensu kenan ta auran da yara biyu akwai hud'u a gida uku maza sai 'yar autarsu mace.

Su uku ne a wurin maigidan ita ce Uwargida.

Ta ce." Ai na ga yaran a can gidan Hajiya Maryam twins sun yi wayo sosai sun zama 'yan mata, Ubangiji Allah Ya yi musu albarka."
Na amsa da amin Ya Allah, ai kam duk sun yi wayo."
Ta gyada kanta da d'an murmushi a fuskarta kamar wadda aka tsikara ta ce." Allah dai ya sawwa'ke abinda ba zai shige ba ni Hajiya Aziza."
Kallonta na yi ban ce komai ba.

Ta sake yin murmushi kafin ta ce wani abu kira ya shigo wayarta tana d'agawa na ji tana fad'in." Halisa har na fito ma daga gidan, a alhamdulillahi jikin nata da sauki wallahi, eh na gaya mata sa'konki ta ce ta gode." Ta yi shiru tana sauraranta kafin ta ce." To ya za a yi lalura aka ce fa Halisa kin kyauta ai Allah ma yana son masu wannan zuciyar irin taki Ubangiji Allah Ya sa mu fi karfin zuciyarmu."
Daga can ta amsa da Amin kafin su yi sallama da juna ta dube ni tana fad'in." 'Kanwata ce Halisa.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *2K ON TALGRAM.*
*VIA 0542382124...

BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*104*
*Whasap Gruop 1K*
Na ce."Allah sarki a takaice ina d'an wani nazari a zuciyata sai na ji maganarta tana fad'in." Halisa k'anwata ce cikinmu daya ai da da rabo kuma Allah Ya yi wa Alhaji Amadu tsayin rayuwa suna tare da Maryam din domin kuwa sun yi soyayya k'warai kuma har iyaye suka shiga maganar har da yarjejeniyar aure a tsakani domin sadaki ne kawai bai biya ba lamarin ya rushe.

Shiru na yi ban ce mata komai ba.

Ganin haka ya sanya ta cigaba da ce wa." Alhaji Amadu ya so Halisa sosai kuma ya yi mata hidima k'warai farko a gidana suka had'u ya nuna yana sonta sanin halin tsananin kishin matarsa ya sanya da maigidanmu yake sanar mini da buk'atar abokinsa na ce a a gaskiya dalili na farko Maryam k'awata ce muna zumunci sosai saboda abotar mazajenmu.

Duk da ba mu zaune a gari daya amma muna ziyartar junanmu sa'i da lokaci kuma muna yin zumunci ta waya bayan haka kuma tsaye take a kan yarana kamar yadda ni ma nake tsaye akan yaranta.

Shiyasa ban yi mamakin ganin yaranku a gidanta ba domin zahiri macace mai son yara da gaske da hidima su.

Da yake 'yar kasuwa ce mai zafin nema ba zan manta ba tasha yi mini fad'a sosai idan muka hadu tana fad'in ko ba zan nemi kudi don yarana ba dalilin ubansuya tara musu na tashi na nema domin iyaye da 'yan uwa da kuma gajiyayyu.

A duk lokacin da wani abu ya fito na ya yi muddin ta yi odarsa to kamar yadda za ta d'ibarwa Nusaiba kaya haka zata d'ibarwa Asiya da Madina kaya irin na yarinyarta babu bambamci ko kad'an.

Sosai take yi mini kara akan komai ni kaina na sheda tana da kyauta da kirki daidai gwargwado Maryam duk wanda ya ra'be ta zai dandali arzikinta.

Sai dai kin san an ce d'an Adam tara yake bai cika goma ba nasan dai tuntuni Maryam ba ta son kishiya tasha gaya mini a rayuwarta abinda tafi tsana kenan dalilin da ya sanya lokacin da maigidanmu zai 'kara aure ta dinga ba ni shawarwarin yi masa tutsu da wasu dai shawarwarin da nake ganin za su iya kaini ga halaka.

Lokacin na tsananta da addu'a sosai domin mu gaskiya gidanmu gidan malamai ne Amina ba mu ta so mun ga iyayenmu na yawon bin malamai ba.

Addu'a dai da yin nafilar tsakiyar dare ita iyayenmu suka koya mana tare da azkar a duk lokacin da wata matsala ta tunkaro mana.

Gaskiya ban yarda na bi sharwarin da take ba ni ba na dai dage da addu'a sosai akan idan auran da mijina zai yi akwai alheri ina rokan Allah Ya hada ni da abokiyar zama tagari dalili tunda?a na ta so gidanmu mata hud'u ne a ciki kuma mahaifinmu tsayayye ne da wuya ma a cikinmu wata ta kaso auranta ta dawo masa gida da zumar yin zawarci daidai gwargwado mun samu kula da tarbiya.
Chapter 152 · 0% Book details