Sashe 266
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk abinda yake yi yana sane yana kuma yin aiki da ilimi da koyarwar Annabi domin yin adalci cikin ni da ita babu wadda ta sanya shi ba mu wani abu daga cikin dukiyarsa shi ya yi ra'ayi a lokacin ya jaddadawa Hajjan cewa plaza kad'an ya yi mini a madadin kamfanin da ya bata sauran shagunan da take tunanin shi ya bud'e mini ba shi da hannu tun kafin ya aure ni nake neman kudi ita kanta Hajjan ta san da haka tunda da farko ganin yadda Hauwa ta yi bala'in shiga damuwa ta ce a samu sulhu kawai ya kar'bi kamfanin tunda ita din macace zai wahala ta iya kawo masa cigaba sai ya yi mata yadda take so.
Amma jin haka sai jikinta ya kara yin sanyi tuntuni ta fahimceta zafin kishinta da ganin Ido shine zai kai ta ya baro.
Kwanansa biyu a kano suna buga artabu Hajja ta ce a sayar da kamfanin a bata kudin shi kuma ya ce bai gina shi don ya sayar ba.
Adalci d'aya da zai yi mata zai cigaba da kula mata da shi domin ganin ya sake yin shura yanzu ma ba wai aiki ne ba ya yi ba, kawai dai yawaitar massarafuwar kamfanin sabulun da suka yi yawa ya sanya kasuwarsa ta kwanta dama amma a rana akan iya fitar da kwali dubu ko fiye da haka ina lefi.
Hajja ta ji dad'in hakan domin sai take ganin ba wani abun bane a ganinta ma wanda aka bawa kamfani guda ai ya fi morewa ta sallame shi ta ce ita Hauwan ta kwana biyu a wurinta domin a ganinta cikin kwanakin da za ta yi zata iya tausarta ta rarrrasheta ta ha'kura amma ina Hauwa ta wuce da tunaninta washe garin ranar da ya tashi Hajja na dyakinta da safe misalin goma da kwata tana sallar walha Hauwa ta bar gidan cikin matsanaciyar damuwa da tashin hankali bauci ta nufa zuciyarta cike da bakinciki da kuma neman hanyar da zata warware damuwarta.......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*174*
To duk yadda ya kai da ko'karin ganin ya b'oye abinda yake damunsa sai da na hankalta cewa lallai a cikin matsanaciyar damuwa yake wadda ma take ko'karin ganin ta ta'ba wasu muhimmanan al'amuransa mussaman da ya d'auki dabi'ar shiru da nazari.
Hankalina sai ya rabu biyu daya a kansa daya kuma akan harkokina da suka fara kafuwa wanda shi din ne ya zama sila kuma ma'kasudi domin dai ya taka muhimmiyar rawa wadda ta zama tushe kuma matakin nasara shaguna har mun tsayar da ranar bud'e su wadda muke sanya ran cewa a cikinta za mu yi promo ga customers dinmu na farko mun tallata daga can kano zuwa abujan da sauran jahohi bisa jagorancin mutumin da ya had'a ni dashi Lawan wanda na tabbatar da cewar shi din za'kwakuri ne tuntuni sun yi masayar lambobin waya da su Hamusu.
Kuma mun gama magana da Baban Saude kan cewa zai ba ni yaransa biyu duk da acan suna sana'ar huluna da sayar da yaduka mabambamta mussaman na hijabai da ro'ko da magiya ya amince mini domin duk wad'anda suka nemi samun gurbin zama duk da cikin family dinmu suke Ya Falmata ta ce a a daya muka d'auka daga cikinsu Halifa karamin k'aninsu Banandi sai Abahuraira da kaninsa Saifullahi yaran Baban Saude daga can kano kuma gidanmu na ce idan Hamusu da Usaini za su taho sai Ashiru ya biyo su shima tunda shi Saminu suna tare da Yusi a shago daya wanda koyaushe yake sake bunkasa dalilin kokari da cigaban da suke kawo masa a zamanance.
Wannan yanayin nasa gabad'aya sai ya dakusar mini da karsashin jikina hidimar dai kawai nake yi amma gabad'aya bana yin ta cikin dadi dalili ko bai gaya mini cewar akwai matsala tsakaninsa da Hauwa ba dole na gane tunda ya fi sati daya yana kwana a gidana sau d'aya da na yi masa magana ya 'bata ransa yana ba ni amsa kamar ba ya so sai ban sake ce masa komai ba na zura masa ido amma dai yau na yi niyyar takureshi akan sanin abinda yake faruwa yanzu abinda na gama fahimta a game dashi Hauwa ce matsalarsa tunda zahiri da bad'ini Allah Ya riga ya gama yi masa komai
Ilai kuwa ita din ce domin dana matsananta masa da tambaya abinda yake zuciyarsa ya furta mini Kai tsaye Amina zan saki Hauwa.
Zahiri na ji fad'uwar gaba da tashin hankali lokacin da maganar ta fito daga bakinsa ban kuma yi mamaki ba domin tsananin tunani da nazarin da yake yi akan lamarin ne shin ya aikata ko kada ya aikata tsayin shekarun zamana da shi na fahimci mutum ne mai nisan tunani kuma bai fiye yanke hukunci cikin fushi ba yakan ta jujjuya lamari yana nazari a kansa kafin ya yi hukunci ga misali nan akan matarsa Hajiya Maryam da ta rasu kafin ya amince da abinda ake magana a kanta sai da aka kai ruwa rana har ya gani da idonsa ya kuma tabbatar.
Jikina ya shika sosai na zuba masa idanuwana shima ya zuba mini nasa ido babu annuri ko kad'an a saman fuskarsa ya cigaba da cewa rabuwata da yarinyar nan shine kwanciyar hankalinmu gabad'aya domin kuwa Hauwa ba ta shirya zama ta gyara mini gidana ba har ta ba ni nutsuwa da kwanciyar hankali irin wadda nake samu a wurinki.
Ni ba sakaran namiji ba ne don haka ban ga dalilin da zai sanya a ce wata mace na raba mini hankali ba.
Abu biyu suke ri'ke da Hauwa a hannuna a yanzu kuma su nake dubawa shiyasa duk abubuwan da take yi nake kawar da kaina a kanta ba wai tsoron rabuwa nake da ita ba kamar yadda take nuna hakan.
Ko yau na rabu da ita gobe ina iya auro wata a madadinta idan har ina da ra'ayin hakan don haka tunda kin nemi da lallai sai kin ji matsalata to wannan ce."
A kasalance na ce." Ko zan iya sanin dalili, ai dai ka san haka kawai ba a sakin mace sai da dalili, gaskiya ka yi hakuri abin kunya ne a tsakaninku dukkaninku kun girma fa."
Ya gyad'a kansa ." Dalili akan ki ne domin duk zargi da tashin hankalin da ta shiga ganin kasuwancinki tana ganin ni na kafa ki na ce mata a a ni ma cikin nema na gan ki muka yi aure kina neman ki, bata yarda ba ta kai kara wurin Hajja wai kamar ni Hauwa ke yawon kaini k'ara saboda ba ta da mutunci tana ganin na fifitaki ina kashe miki kudi ita na bata tsohon kamfani sai dai a canza mata da abinda na yi miki shin a cikinku ko akwai wadda ta sanya ni d'aukar dukiyata na baku, alheri ne kawaii na yi muku ganin tare duka aka nemi dukiyar daku tana ganin abinda na yi miki ya fi wanda na yi mata akan hakan kuwa lallai ranta zai b'aci don ban ga dalilin da zai sanya ta tsananta k'yashi a kan ki ba, kema Allah ne ya yi miki daidai gwargwado kuma kin nema ni hannu kawai nasa miki kuma sai daga karshe ko ba haka ba ne?"
Na gyad'a kaina ina fad'in." Hakane amma akan hakan ka ke cewa za ka saketa ai ba hujja ba ce wannan kuma abinda ta nema ka fi karfinsa don ta tsananta kishi da k'yashi a kaina babu lefi ko ka manta kishi ne a tsakaninmu kowa fa da irin zuciyarsa, wallahi ban ji komai ba amma don girman Allah in dai zan baka shawara ka d'auka to ka yi mata yadda take so tunda kana da iko ka daidaita tsakaninmu itama ka bude mata plazar sai ka kar'bi kamfanin ka kawai tunda dama wahalarsa yawa gareta."
Ya girgiza kansa." Idan na yi mata plaza sauran shops din na kwari market kuma wa zai yi mata? tana cewa ai duk ni na yi miki"
Yar dariya na yi kad'an na ce sai ka yi mata menene a ciki ai Allah Ya hore maka?"
Ya girgiza kansa a nutse ya furta." Babu wanda zai karya mini rantsuwa Giwa ai na ce ta bar shi a hannuna zan a cigaba da aiki da shi a madadinta kuma abinda take han'koro za ta samu rashin yarda ne kawai da ci da zucci.
Ba zan yi wata plaza ba yanzu wannan shine karshen magana."
"To kasan halinta da rashin yarda da kuma taurin kai kenan idan kai da kake matsayin jagora baka yi yun'kurin ganin ka nemo mafita ba lamarin zai lalace ai."
"Ai na nemi mafita tuntuni aiwatarwa zan yi kawai ko kin ga na yi miki kama da namijin da mace za ta juya ne Amina.
Wasu lukatan Kawai ina biye muku ne domin ba na son hayaniya wa za ta gayawa taurin kai ne ni da ita shege ka fasa."
D'akin ya d'auki shiru bayan ajiye maganarsa na sauke numfashi Ina dubansa na ce." Yanzu kasan yadda za a yi tunda abin ya zo da haka me yasa ba za ka kara mata kudi akan kamfanin ba."
Harara ya wurgo mini kafin ya ja tsaki yana fadin.
"Ba zan k'ara mata ko kwabo ba wallahi."
Rantsuwar da ya yi a karon farko sai jikina ya mutu ba wai bashi dashi ba ne bayarwa ne kawai ba zai yi ba Amma ni ina ganin idan har ya k'ara mata kudi akan kamfanin da take ganin darajarsa ba ta kai plazata ba zuciyarta zata yi sanyi ga shi kuma ya rantse da gaggawa.
Na ce." To ni zan k'ara mata amma a madadinka."
Ya dinga shillo mini harara kafin ya yun'kura ya tashi bai ce komai ba ya shige toilet yana tsaki.