← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 276 OF 276

Sashe 276

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hamusu kuma yana da mata biyu yanzu yaransa hud'u ya sake gina gida mai girma rayuwa ta yi kyau kwarai da gaske babu wanda nake yi wa mugunta kaf cikin yarana na bud'awa kowa ya samu Turzumi ma yana tare da su a kasuwa na ce a sama masa gurbin zama ya fara kasuwanci domin kula da yan uwansa tunda shine namiji babba a gidansu.

Shi kuma Adam idan an yi magana ina budurwarsa sai ya nuna Usaina ta yi ta zum'bura baki tana jin haushi yanzu suna da 16years suna ajin karshe a secondary school.

Shekaru biyu da suka wuce suka sauke al'kur'ani mai girma
Minal kuma tana da 14years da yake tana da girman jiki har ta so ta fi su girma da 'barage k'irjinta ma ya fi nasu fitowa uban yana fad'in daga ya kalleta gabansa yake fad'uwa aure zai yi mata da wuri idan yana fad'in haka na yi ta dariya yanzu ta yi hankali ta daina wannan rawar kan ta nutsu karatu kawai suka sanya a gaba.

Nakan ce duk saurinsa sai ya bari mijin ya fito ya ce ai shi tuntuni ya yi mata miji da na matsananta kuwa Ina fad'in ba da yawuna ba don amanace a hannuna kafin rasuwar Hajja duka yaran sai da ta d'amka mini amanarsu na ce ya bari ba gaggawa ake yi ba don ni ban gaji ba idan har zai dubeta saboda ga'barar jikinta gabansa yana faduwa to ba zai yiwu ya aura mata wanda bata so ba kamar yadda ya tambayi Usaina akan Adamu ta amince tana sonsa itama ya zauna ya tambayeta bud'ar bakinsa ya ce mini ba kowane mijin da ya zab'a mata ba face Yusi.

Tun daga lokacin bakina ya mutu ban sake yi masa wata magana ba a duk lokacin da ya tayar da maganar sai na rasa abinda zan ce.

Haka kawai ma sai na dawo jin nauyin yarinyar duk da cewa ba ta san wainar da ake toyawa ba sabgarta take yi amma sai na tsinci kaina da 'kin barin mu hada ido a hankali na rage biye mata idan tana yi mini shirme da sangarta abinda ya zame mata jiki a gare ni tun tana yarinya domin da ta tabbatar da cewar Mufida ta 'kwace mata kujerarta wurin Babansu sai ta dawo wajena ni kuma na kar'beta tare da cigaba da lelenta Twins na fad'in su babu mai yinsu a gidan duk lokacin da kishinsu ya tashi.

Khalil kuwa yana can Madina karatu makarantar da Kamalu ya yi koyaushe uban na sha'awar Kamalu yana kuma bada misali a kansa da burin Khalil ya yi koyi da shi wajan jajurcewa.

Yusi dama fannin kasuwanci ya karanta don haka tun bayan kammala kararunsa kasuwancinmu ya b'unkasa dalili shine a yanzu ke fita waje yi mana order dubai chaina India da oman zamansa a najeria yakan zama ta'kaitacce dalilin wannan zurga zurgar shi da Saminu tuni sun kammala gidajensu a rijiyar zaki wajan d'ambare don shi Saminu ma har an kai kud'in aure da sanya rana.

Jikin gidajen da suka gina na sanya su yi mini bhole guda biyu hadiya ga mahaifiyata na kuma gina madaidaitan masallatai uku hubusi duk a gareta Babanmu na bashi za'bi sabon gida ko kuma a sabunta masa wanda yake ciki a yanzu ya ce a sabunta masa gidansa na gado iyaye da kakkani.

Gabad'aya aka rushe shi aka yi sabon gini na zamani kowacce aka sanya mata sabbin kayan d'aki.

Addu'a muna shanta da ni da shi daga bakuna mabambamta dalilin hannunmu da yake zaga ko'ina.

Ban san abinda yake tsakanin Abahuraira da Hassana ba katsam Baban Saude ya kira ni a waya yana tambayata menene a tsakaninsu domin kuwa da suka je ganin gida saifullahi ya gaya masa wata magana a kansu.

Na ce da shi ban san komai ba amma ya tambayi Babansu ya ce shikkenan zai neme shi.

A daran kuwa suka yi waya shima dai bai san suna soyayya ba sai da ya kira yarinyar muka titsiyata ta fara kame-kame daga karshe dai ta bada amsar da muke so mu ji daga gare ta tana dariya uban na taya kamar wasu shashashai haka na tsaya ina kallonsu shi da ita idan yana wata shiriritar da yaran ya yi ta ba ni haushi shiyasa gashinan sun mayar dashi kakansu tunda tsakani da Allah a ganina wannan mas'alar ai ta jin kunya ce amma babu ita shi da yarinyar yana tsokanarta tana k'yalkyala dariya.

Ya sanar da Baban Saude ya bawa Abahuraira Hassana a duk lokacin da ya kintsa Baban Saude ya ce a kintse suke son samu a had'a duka dana Kamalu da Usai da Adamu.

Wanda za a yi shi bayan dawowarmu daga aikin hajji kamar yadda suka tsayar da lokaci.

Wanda ya yi daidai da lokacin da za su kammala secondary amma da shara'din barinsu cigaba da karatu koda an yi auran
Suka tsayar da magana a haka bayan wasu kwanaki kuma yake gaya mini za a had'a da Minal kawai duk da ajinta biyar ita yanzu na ce a a ba za a tsinke mata karatu ba bayan haka kuma ba ta yi k'warinsu ba, sannan kuma shi yake sabgarsa shi kad'ai babu wanda ya gayawa a cikin yaran balle su san halin da ake ciki ba a yin haka.

Ya ce ya gayawa Yusi a waya kuma ya amince.

Na ce to itama a gaya mata ya dinga dawurwura alamu sun nuna yana jin tsoron rigimarta abin mamaki ko da ya gaya mata ya yi mata miji da farko zum'bura baki ta dinga yi da k'ananun hawaye amma yana gaya mata wanda ya zab'a mata ta sinne kanta tana murmushi nan ma ya dinga kyakyata dariya kamar wani sabon kamu abin ya dinga ba ni haushi da mamaki.

Ta tashi ta sauka 'kasa da sauri yadda ta nuna alamu ta amshi tayin da aka yi mata kuma Yusi ya samu gurbi a cikin zuciyarta.

A wannan shekaran rabon kujerar hajji ya yi anti Yagana da Ya Falmata sun rabauta da ta su.

Baban Saude da kuma babamu suma sun samu tasu.

Sai iyalinsa gabad'aya ni da shi da yaranmu har da Mufida da kuma Adam da Sukairaju muka d'unguma zuwa kasa mai tsarki domin yin aikin Hajji.

Masu aiki muka bari a gidan.

A can muka riski Khalil kamar yadda muke hasashe ya yi wata iriyar kamala ta ban mamaki kamar dai yadda Kamalu ya yi dama yaro ne mai son girma da manyance sai abinda ya k'aru balle yanzu da ilimin addini ya fara huda shi tare da shi muka yi Hajjin ya d'auki Mufida ya sa a kafad'arsa sosai na tsananta da ro'ko da addu'a akan Allah Ya tabbatar da alheri bisa wannan had'aka ta auratayya da za mu yi wa yaranmu addu'ata gabad'aya ta ta'allaka ne akan hakan tare da fatan cikawa da imani da kuma samun zuri'ar da duniya za ta yi alfahari da ita......
*ALHAMDULILLAHI!*
*ALHAMDULILLAHI*
*ALHAMDULILLAHI!*
Lefin dad'i k'arewa ga dai yadda 'karshen wannan labari ya zo.

Ina ro'kon Ubangiji Allah Ya yafe mini abinda na rubuta bisa kuskure wanda na rubuta daidai kuma ina ro'kansa da ya ba ni lada tare da wad'anda suka bibiyeni.

Godiyata bata da iyaka akan masoyana na gode na sake godewa wad'anda nasa ni da wad'anda ban sani ba.

Comments section na gudun aure lallai kun yi bajinta kuma kun kara mini kwarin gwiwa wajan ganin na isar da sa'kon dana d'auko ba tare da na gaza ba.

Na sake fadi kun yi bajinta k'warai ban cire kowa ba.

Masu k'orafi kuma ban ji komai ba wannan ma cikin kulawa ne Allah Ya saka da alheri.

Za mu cigaba da zumunci da gaisawa cikin comments section kafin zuwan sabon littafi idan Allah Ya sa muna raye.

Ina fatan wanda zai zo anan gaba ya fiye muku wannan da muka kammala dad'i da wa'azantarwa.

A yi bikin sallah lafiya aka kuma yi mini tallah a gruops na kammala a arewapen ga masu jiran karanta complete din littafin....

ALLAH YA SADA MU DA ALHERI.
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
L N
R!T!
# $"$
+<,>,
1,2.2
3d4f4
6B7D7
8D9F9
:J;L;
=l>n>
Times New Roman
Times New Roman
Calibri
Calibri
!%),.:;>?]}
$([{
a nan ba, muna
SummaryInformation
duk mutumin (
zina ba zaka raba
DocumentSummaryInformation
na k8
afin ya nisa.

Ya d
kaWpsCustomData
ad'in." Ai aure ba
sa ba ne, ni ba mu
kiXX
ne, kuma ba zan fara a kan w
nan karamin dalilin ba.

Ni ya
20380f1c253741569ab9efe77260fd14
a buga da karfi na tashi tsaye tare da nuna shi da yatsa.

Sai ya d'an matsa daga kusa da ni fuskarsa d'auke da mamakin yadda yatsana yake daf da karan hancinsa.

Ammafa babu nadama a tattare dashi.

"Idan har sai ka yi fasikanci da ni tukkuna za ka bada u
TECNO LD7
WPS Office
a buga da karfi na tashi tsaye
20380f1c253741569ab9efe77260fd14
skarsa d'auke da mamakin yadda yatsana yake daf da karan hancinsa.

Ammafa babu nadama a tattare dashi.

"Idan har sai ka yi fasikanci da ni tukkuna za ka bada u
Chapter 276 · 0% Book details