← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 236 OF 276

Sashe 236

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daidai lokacin da ya fito kira ya shiga wayarsa ya zo ya zauna da babban towel a jikinsa ya d'auki wayar sai da ya kalle ni kafin ya d'aga a sake ya amsa sallama.

Sai kuma ya yi shiru na wani lokaci kafin ya ce." To Allah Ya sawwa'ke ki samu bacci sosai ciwon kan zai yi sau'ki maganar masu aikin nan kuma ki ajiyeta yanzu abinda za a yi shine zan yi magana da Hajja anan Dambatta ba za a rasa wadda za ta taimaka miki ba, da safe idan Allah ya kai mu zamu tattaunar maganar sosai, ki kula da kan ki, Allah Ya sawwa'ke."
na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Shiru na d'an wani lokaci yana sauraranta kafin ya sauke ajiyar zuciya ya furta ." To babu damuwa sai na dawo." Daga haka sai ya kashe wayar ya ajiye saman dirowar gefan gado...

Ya sake tashi dai ya je ya d'auko basiline ya zauna da shi a hannunsa yana fad'in." Hauwa ce bata jin dadi tana mura da ciwon kai na dai fi tunanin ciki ta samu itama haka take zargi." Ya fad'i maganar yana d'an kallona.

A takaice na ce." Allah Ya sawwa'ke." Ya amsa daga haka sai d'akin ya d'auki shiru Ina kallonsa ya gama shafa basiline din ya shirya cikin jallabiya mai yankakken hannu ya dube ni yana fad'in." Wane aikin zan yi miki a kicin Hajiya."
Da mamaki nake kallonsa ya gyad'a kansa yana cewa." Menene a ciki manzon rahama ma ya taimakawa iyalinsa ni kuma wanene ko dakan sakwara ki ka ce na yi miki a wannan dare na shirya ke ce fa."
Murmushi na yi a hankali na girgiza kaina tare da cewa." A a ka huta kawai to wai ma ka iya girkin ne?"
Ya furta." K'warai kuwa mu je kicin din naki ki ga yadda ake yi wani abin ma zan koya miki wanda ba ki iya ba."
Na ce." Lallai naga alama amma mu je din indomi kacal za ka dafa mini."
Ya ce." Ai ni ba ni cin indomi Amina da gaske kuma yunwa nake ji na d'auka zan samu abinci."
Jin ya fadi haka sai na gazgata gaskiyarsa babban abinda ya tsana zuwa gidan abinci ya jima yana fad'in tozarta kai ne ga maigidancin da yake sayan abinci a waje.

Na tashi tsaye da kyar ina fad'in." To me za ka ci sai na yi maka yanzu.'' Ya riko hannuna yana cewa." A a mu je dai kicin din tare sai mu yi aikin ko?"
Na gyad'a kaina ban sake cewa komai ba muka sauka kasan tare yana yi mini labarin yara da yadda suke hira kullum da masu aiki su Baba Tabawa.

Na gama gane so yake yi mu yi maganar komawata can amma ya'ki yarda ya fito kai tsaye ya fad'a sai kame-kame yake yi.

Muka tsaya akan dafa jallof din taliya na kunna masa gas din ya d'auki tunkuya zai tari ruwa ni kuma na d'ebo kaya
n miya domin marka'dawa ya ciko tukunyar taf da ruwa ya d'ora kan gas din.

Ina kallonsa ya rufe da murfi yana fad'in." Sai me za a yi?"
Na ce." Da wannan kurmemen ruwan za a dafa rabin taliya?

Ya ce." Ya yi yawa ne?"
"Sosai kuwa kuma mai ake fara soyayya tukkuna a zuba kayan miya a soya tunda za mu yi amfani da busashen kifi idan mun gyara shi mun wanke sai mu zuba mu d'an soya tare da kayan miya nan sannan mu tsayar da ruwan sanwa."
Ya sauke tukunuwar tare da zubar da ruwan da ya mayar da ita kan gas din ya d'auki mai ya tsiya mai mugun yawa don wanda ya zuba zai yi gwangwani biyu ko fiye da haka."
Na ce." Kenan da mai za mu tsayar da ruwan taliyar ko soyayyiya za mu yi ne Allah Ya taimake ka."
Ya ce." Ana yin soyayyiya ne dama?"
Ina dariya na ce." E, amma ba ita za mu yi yanzu ba kuma mangyad'ar da ka zuba ya yi yawa.

Gabagad'i kuwa ya kai hannunsa zai sauke tukunyar da ta d'auki zafi man yana suyuwa.

Ya cire a zabure ya matsa har sai da murfin tukunyar ya fadi kasan k'afafunsa.

Ya rikice sosai yana duba yatsunsa.

Dariya kamar cikina zai yi ciwo na kashe gas din na jingina jikin wardrobe Ina kallonsa ina dariya sai zare ido yake yi.

Ya nuna mini yatsun yana fad'in sun toye Amina kin ga yadda suka yi jaaa ashe haka abin yake dama?"
Na ce." To kai wanene ya ce ka kama tukunya haka kawai, kuma ka ce ka iya girki ashe baka iya ba."
Ya ce." Idan hakane bayin Allah nan suna aiki Amina wanene yasan iya adadin yadda suka 'kone garin sauke tukunya."
Na d'an 'bata rai cikin shagwaba na ce." Su kadai kenan, ni ma ai ina yi maka girki."
Ya rikice kuwa ganin yanayin yadda na yi masa magana a sangarce da shagwaba ya matso ni yana cewa." Har dake mana kuna kokari gaskiya Allah Ya saka da alheri."
Na amsa da Amin a takaice tare da d'an zame jikina ina cewa." To zo ka ga yadda ake yi ko don gaba.

Ya kuwa taho ya tsaya a bayana yana murmushi na fara gudanar da aikin cikin nutsuwa yana yaba mini har da addu'a da tukwici sumba a wuya da kumatu a haka na yi masa jallof din taliya da dankali da kuma bushshen kifi ya ce a yi masa da manja ta yi kyau sosai tana k'amshi mai dad'i.

Kusan tare muka ci amma dai shine karfin cin kuma yadda ya zage ya ci da yawa ya tabbatar mini da cewa yunwa ce mai yawa a tare da shi.

Ban zaci zai iya d'auke kansa daga kaina ba a daran salin alin muka kwana bai nemi yin wata mu'amula da ni ba.

Sai washe gari da rana gatse-gatse ya fara kame-kame da ya ga na'ki nuna na gane abinda yake nufi ya kamo ni wai na yi masa dabaru ta yadda zai gamsu yana tsoron ya kusance ni a haka na yi nauyi a cewarsa tausayina yake ji.

Ya fad'i hakane kawai don ya kare kansa amma shi kansa ya san babu wata dubara da take kwantar masa da buk'atarsa face sai wannan abin ya faru.
ban ma yi nisa wajan yin dabarun ba ya fice daga hayyacinsa maganar tausayi kuma sai ta kau ya fara ko'karin ganin ya samu hanyar zai mutunta kansa sai da na dinga ankarar da shi halin da nake ciki tukkuna a haka lamarin ya faru kamar wani sabon tuburarran mara hankali......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
*ZA MU KAMMALA A CIKIN SATIN SALLAH IN SHA ALLAHU*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*158*
Haka muka kasance cikin kula da juna mussaman daga b'angaransa wata sabuwar kulawa na dinga samu a wurinsa bini bini sai ya ce tausayina yake ji amma hakan ba ya hana shi da daddare ko kuma dai duk lokacin da lambarin ya bijiro masa ya kwanta da ni, a wannan gefen sai ya manta da tausayi girki kuwa bai sake cewa zai yi ba dalili ya ji babu sugar domin yatsunsa da ya kama tukunya sai da suka ruruce suka ja ruwa.

Sai dai duk lokacin da zan shiga kicin zai bi bayana ina aiki yana damuna da runguma da ta'be-ta'be lamarin nasa dai kamar na sabon ango ko kuma wanda ya koyo wani sabon darasi ai soyayya ya iya babu karya kamar sabuwar balaga ba dattijo mai yawan shekaru ba.

Ranar sadakar uku ya ce na shirya mu je ya kai ni gaisuwa.

Na shirya kamar yadda ya buk'ata din muka nufi dambatta a mota Ade direbansa ya ja mu.

A gidan rasuwar na samu Hajja tare da jama'a tunda shi daga waje ya tsaya sai daga baya tukkuna ya shigo gidan.

Hajja ta dinga nuna ni ga jama'arta wasu sun san fuskata wasu kuma ba su san ni ba dama fadi take itace uwargidan nasa ai Amina sunanta, itace wadda aka dauro auransu a saudiya.

Sai na zama abin kallo na dinga jin nauyi da kunya domin na kasa tantance kallon da yawancin jama'ar wajen ke yi mini.

Da la'asar muka fito daga gidan a kafa muka taka zuwa gidan Hajjan tunda babu nisa.

Ta sanya Iyami mai aikinta yi mini towon shinkafa miyar zogale domin dai ko kad'an na kasa cin abincin da aka ajiye mini a gidan rasuwar dafadukan shinkafa ce amma sun yi amfani da wani irin curry ya yi rabad'au dashi 'kamshin babu dad'i.

Wajan biyar iyami ta gama aiki ta kawo mini sannan Hajja ta ce ta zuba mini wani a fulas sai mu tafi dashi na huta girki.

Na kuwa ji dadin hakan sosai.

Sai da na yi sallar magriba tukkuna ta fito daga cikin dakinta da turaman atamfofi guda uku manya ta miko mini tana fad'in.'' Kada na manta kar'bi wannan Amina bari na nemo leda."
Ya juya da sauri ta koma d'akin ta bar ni ina juya atamfofin tsala-tsala masu tsada.
Chapter 236 · 0% Book details