← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 198 OF 276

Sashe 198

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda twins din suka yi mini.

Sai da na shirya tukkuna na tashe ta muka fita a tare babu kowa a falon.

Kai tsaye d'akin ya yaran na nufa Mairo tana ta fama da su Khali na can gefe yana rubutu a littafi.

Ta burni kuma tana gyara musu wardrobe.

Na ce." Mairo a bawa Minal abinci." Da sauri ta ce." To ta janyo hannunta zuwa ciki.

Usai ta biyo bayana muka zaune kujera a tare jim kad'an itama Hassanar ta fito na daga kai na dube su a nutse tare da fad'in." Kun yi sallah ko?"
Suka daga mini kai a tare na ce." Abi
ci fa?''
Girgiza kansu suka yi.

Na d'an 'bata fuska ina fad'in.'' Bebaye ne ku?''
Usai ta ce." Menene Bebaye Mama?"
Sai na fara gwada mata maganar kurame da hannuna da bakina." Aikuwa sai dariya gabad'ayansu suna kallon bakina yadda nake yi.

Ni ma na kama dariyar ina fad'in." Bebaye ne masu magana da hannu da kuma gyada kai, ku kam ai kuna da baki ko?"
Da sauri Hassana ta ce." E, wanda muke magana da shi muna cin abinci."
Na ce." K'warai kuwa daga yau idan na yi muku magana ku daina yi mini ta kurame ku bude baki ku ba ni amsa."
Suka ce "to Mama."
Na ce." Aje a ci abinci idan da aikin gida na makaranta a d'auko a yi."
Suka ce "To" a tare da sauri suka ruke hannun juna.

Na sauke ajiyar zuciya tare da fad'in." Hassana duba d'akina ki d'auko mini wayata saman gado."
A tare suka nufi d'akin jim kad'an suka fito na kar'bi wayar suke wuce dakinsu.

Ina dubawa na ga miss call Hamusu ya kira ni jim kad'an da fitowa daga d'akin.

Na kira shi bugun farko ya daga muka gaisa yana fad'in." Anti Amina Gwaggo tana ta fad'a wai ba ki sanar da ita cewa Yallabai bashi da lafiya ba.

Yau a gidan Hajja ta yini ta sanya ni na kaita muka je muka tarar kun tafi."
Na ce." Wallahi Hamusu ku yi mini uzuri ka bawa Gwaggo hakuri ko kuma idan ka je gidan sai ka kira ni a waya abubuwan ne sai a hankali amma ka ce mata ya ji sau'ki sosai ya warware."
Ya furta." In sha Allahu rabbi."
Muna yin sallama na hangi Hauwa na saukowa daga benansa.

Na yi gaggawar janye idona daga hanyar har ta sauko ta iso tsakiyar falon na daga kaina na kalleta duk yadda take ko'karin kalato annashuwa ta ya'ba a fuskarta sai da na gane karfin hali ne kawai ta kira sunana na amsa za ta shiga d'akinta na ce." Ni kuwa akawai maganin maigidan da ake yi masa kullum da daddare Hauwa bari na d'auko miki shi zai yi miki bayani yadda ake yi masa."
Ta ce." To tare da tsayawa na tashi na shiga d'akina na d'auko mata sauran maganin da ya yi ragowa da rubutun ina fad'in zai gaya miki yadda za a yi."
Ta sake cewa ." To." Kamar mai koyon magana ta kar'ba ta shige d'akinta.

Baba Tabawa ta fito da Sultan a hannunta ya yi wayo sosai yana ta furzar da yawu alamun hak'ori na kar'be shi Ina dariya tare da cewa" Yaro ya sake wayo duka bai fi sati biyu ba rabona da ku amma kowa ya canza mini a gidan na ji dadin ganinku cikin koshin lafiya."
Ta zaune tana fad'in." Alhamdulillahi kam sai godiyar Allah."
'Daga shi sama na yi na cafe ya dinga b'angala baki yana d'igo mini da yawu a fuska.

Baba na murmushi ta ce." Ai ya yi wa uwarsa yankan k'auna a gidan nan Hajiya wallahi kamar al'amara ko wanda aka rad'awa a kunne koda ta dawo ya ga 'bakuwar fuska idan ya kalleta sai ya tsalla ihu duk ya sheda fuskokinmu amma ban da tata 'kiri-'kiri ya'ki yarda ta d'auke shi, da ta tsananta a washe garin ranar da ta dawo don kuka sai da ya kusan shid'iwa ya yini yana baccin wahala daga lokacin tace kada a kara fitowa falo da shi falo.

Idan kuma ana canza uwa sai ya canza.

Wai ta ji haushin abinda ya yi mata."
Murmushi kawai na yi ina d'an cire hannunsa da yake janyo mini d'ankunne a takaice na ce." A hankali zai saba da ita dama ai mussaman yaro mai 'kuiya yake." Ba na so maganar ta yi tsayi a tsakaninmu don ban san abinda za ta haifar ba.

Nan falon na zauna na ci abinci muka yi hira ta yaushe gamo da Baba Tabawa wajan yara da arba'in Hauwa tun da ta shiga d'aki bata fito ba shima maigidan tunda ya sauko wajejan Isha'i ya fita bai shigo ba har na yi sallama da Baba ba shige d'aki.

Isha'i na yi kawai na sanya kayan bacci na kwanta amma raina gabad'aya babu dad'i ba na son wannan matsalar ta su ta shafi lafiyarsa Malam D'aha ya jadadda mini cewa kada a tsallake rana d'aya wajan aiki da abinda ya bayar.

Ban hangi wani sasanci da d'okin juna a tsakaninsu ba.

Hauwa ta kar'bi maganin ne kawai domin kada ta nuna mini akwai matsala tunda abinda na karanta kenan a fuskarta amma ai ni ba yarinya ba ce tun saukowarta na karanci tsananin damuwa da tashin hankali.

Yadda na yi wa Hajja alkawarin kawo zaman lafiya a tsakaninmu hakan ne ya sanya ni bata damarta a matsayinta na wadda ta yi kome gidan mijinta dole ita zata shiga turaka idan magana ta gaskiya za a yi.

Na d'auki wayata domin kiransa.

Ko da ta shiga bai yi jinkirin d'agawa ba.

Na ce." Allah Ya taimake zan ce dama sai da safe domin na yi ta jiran ka shigo mu yi magana shiru ragowar maganinka na wajen Malam D'aha na bawa Hauwa na ce sai ka yi mata bayanin yadda ake yi maka ko?"
Ya ce." Akan wane dalili Amina?''
Shiru na d'an yi ina mamakin maganarsa.

Dalili saboda matarsa ce ya yarda ta dawo su cigaba da rayuwa an yi musu sulhu iyaye sun shiga yanzu zaman aure za mu yi babu cin amanar juna da zalintar wani.

Ya sake maimaita maganarsa da b'acin uana fad'in." Sai ki je ki kar'bo mini maganina idan ba za ki zo ki yi yadda ki ke yi kullum ba ki kawo mini na yi abina."
A dan daburce na ce." Ai ba da gangan na'ki zuwa ba sanin da na yi cewa dole ne itama a bata damarta hakkinta ne kuma.....

Ya katse ni
"Ni na ce ta dawo?"
Shiru na yi ina sauraransa.

Ya cigaba da cewa." Ki je ki ce ta baki magani na ki kawo mini ina da lafiya Allah ya hore mini ba ni da nakasa a hannu zan gudanar da komai."
A tak'aice na ce." Gaskiya ba zan iya ba ai na riga na bata."
Ya datse wayar ba tare da ya sake magana ba.

Na kashe na nemi gado na kwanta ina fad'in" Ban da rigima ai da tun a can sai ka gayawa mahaifiyar taka baka amince ba, haba a yi ta abu daya sai kace 'kananun yara."
Jin yawu ya d'an ciko bakina ya sanya ni tashi na bud'e dirowa nan na sanya ledar da Hajara ta aiko mini da ita na ji dad'i sosai kuwa tun a gidan Hajja dana bud'e na gani magarya da kurna taura da aduwa har da tsamiyar biri irin kayan motsa baki na gargajiya.

Aduwa na d'iba na zauna gefan gado ina tsotsa a tsanake ina duba wayata What'sapp na shiga na ga sa'kon Nusaiba ya shigo voice note ko da na bude sai na ji muryarta har tana rawa tana gaishe tana fad'in ta zo gidan ba na nan har sau biyu zuwanta na k'arshe Hauwa ta ce kada ta 'kara zuwa domin ita najasa ce da mahaifiyarsu.

Voice na biyu kuwa kuka take yi tukuru tana fad'in.

Anti Amina don Allah kada kema ki k'yamace mu don Allah kada lefin da mahaifiyarmu ta yi ya shafe mu wallahi tallahi ba mu ta'ba sanin abinda take aikatawa ba kenan, ta rasu ta dasa mana tsangwama da k'yama a wajan mutane ba mu da lefi kada ke ma ki tsane mu antina......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[5/3, 2:50 PM] +234 803 054 1544: https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.
Chapter 198 · 0% Book details