← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 276

Sashe 160

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan ki ka karanta ba ki biya ni hakkina ba ina bin ki bashi.

Sai wajan takwas da rabi ya kira ni a waya yana gaya mini suna airport saukarsu kenan.

Cike da kulawa na ce." To, shikkenan Allah Ya kawo ku gida lafiya."
Ya amsa da kulawa kafin ya datse kiran.

Na ajiye wayata ni ma na fita falon shiru Baba na dakinta.

Zamana a fa
lon da kamar minti goma ta fito har yanzu yaron yana goye a bayanta na ce." Wai Baba har sallah ma da yaron nan ki ke yi a goye?"
Tana ko'karin zama kusa da ni take fad'in." Wataran ba, amma dai idan na ga baccinsa ya yi nisa ina sauke shi sai dai fa kafin na idar da sallar ya tashi, ai ya tsani kwanciya sai dai goyo."
Ina dariya na ce." Dama ai duk abinda aka sabawa da yaro shikkenan sai ya tasirantu da shi ki dinga kwantar da shi ko zai saba."
Ta furta." Ai rik'on hannu ga yaro irin wannan shine matsala Hajiya amma goyo daidai kenan, kuma idan dare ya yi sosai na kwantar da shi baccin mu muke sosai sai da asuba yake farkawa.

Aikuwa kamar yana ji sai ya fara motsi ta ce." Af kin ji shi ko? shi fa baya so a goya shi a zauna zai kama tsalla ihu."
Na ce."Sakko shi mu gaisa." Ta kwanto shi daga bayanta tsaf dashi a cikin kayan sanyi masu d'umi yana ta k'amshi ni kaina sheda ce yaron yana samun kulawa wurin Baba Tabawa tamkar yana rayuwa a hannun uwarshi.

Na kar'be shi Ina d'an jijjigashi da fad'in." Yau za ka ga babanka yaro."
Ta mike tare da fad'in."Bari na d'auko masa abincinsa." Ta nufi dakinta da saurin gaske.

A kafadata na sanya shi ina d'an jijjigashi maigidan ya shigo tare da Sukairaju a bayanshi.

Yana cikin suit ya zanzare sosai ya yi kyau da kayan dukda bai fiye tu'ammuli da su ba amma duk ranar da ya sanya irinsu ni kaina yana burge ni.

Farin gilashinsa na ka'ida yana sakaye da idanuwansa na mike tsaye da yaron a kafadata yayin da shi kuma ya juya yana kar'bar yar wasu takardu daga hannun Sukairajun ya ba shi umarnin tafiya.

Baba Tabawa ta fito hannunta ri'ke da fida cike da madara ta washe bakinta tana fad'in." Sannu da zuwa sannu da hanya ranka ya dad'e fatan an dawo lafiya?"
Ya amsa da kulawa. yana fad'in." Lafiya lau Baba mun same ku lafiya?

Ya kokari kuma na gode sosai Allah Ya saka da miki da alheri."
Ta d'an sunkuyar da kanta tana fad'in ." Babu komai wallahi, ai babu buk'atar godiya Alhaji."
Bai ce komai ba ya dubi wurin da nake tsaye na saki fuskata sosai Ina fad'in." Barka da zuwa."
"Barkanmu dai Allah Ya taimake ki." Ya fadi hakan cikin sigar tsokana kafin ya fara ko'karin haurawa samansa.

Na kar'bi fidar yaron dake hannun Baba Tabawa na bi bayansa.

Na same shi yana ta ko'karin cire safar dake kafafunshi.

Ya dago yana kallona kafin ya furta." Amarya."
Ban ce komai ba na zauna gefanshi ya miko mini hannu yana fad'in.

Ba ni abokina mu gaisa."
Na mika masa yaron ya kar'ba ya tsira masa ido sosai kafin ya gyad'a kansa yana fad'in." Wallahi Amina Hauwa ba ta da imani ko kad'an."
Na yi shiru Ina kallonsa ya sanya bakinsa a kunnan yaron hagu da dama ya jima a haka kafin ya sake duban fuskarsa ya ce." Amadu shine sunanka, ina ro'kon wanda ya ba ni kai ya rayaka tafarkin addinin Islama, ya raya mini ku bakidaya."
Na amsa da "Amin Ya Allah."
Ya miko mini shi yana fad'in." Ina can hankalina yana nan Amina Amma alhamdulillahi na ji dadin ganinku cikin nutsuwa da kwanciyar hankali lallai Allah Ya azurtani da matar rufin asiri kuma Mar'atussaliha, na godewa Allah na kuma gode mini bisa abinda ki ka yi mini."
Maganganunsa sun sanya mini mutuwar jiki, na dube shi karon farko da na ji tausayinsa ya tsirga mini.

Na janye idona daga kansa can kasan zuciyata ina ji tana fad'in cewa ba matausaya ba ne ba fa.

Na danne dai tare da furta." Ya mai jikin, koda yake alamar karfi tana ga mai 'kiba wai ka gan ka kuwa yadda ka wani zanzare wai kuma jinyya ka tafi gaskiya ka fi kama da wanda ya tafi yawon sha'katawa."
A sakarce ya kalleni yana ko'karin cire gilashin idonsa ya ce." Wane sha'katawa bayan babu babbar sha'katawata a kusa da ni, ai ke ce karshen sha'katawa Amina."
Murmushi na yi ina kallonsa.

Ya ce "Da gaske nake gaya miki kece sha'katawata, na ga kin yi kama da amarya yau tunda na kalle ki nake ganin kamar sabuwar amarya na yi."
A gajarce na ce." Wani Abu ya canza a jikina ne?"
Ya furta." Kwarai kuwa ga lalle an ranga'da mini, an yi mini kwalliya na yaba sosai sai a fadi nawa ne kudin lallan na biya."
Na furta." Ai ba zaka iya biya ba."
"Me yasa?" Ya fad'a yana ko'karin mi'kewa tsaye.''
Ban ce komai ba ni ma na tashi ina fad'in." Bari na mik'a yaron nan wurin Baba ta goyo shi bacci zai koma."
Ya furta." Ya yi, zan yi wanka yanzu na sauko cin abinci sai mu sake gaisawa ko."
Na ce." To shikkenan sai ka sauko." Hanyar fita na nufa ina d'an jijjigashi yana ta motsin kuka.

A falon ya same ni muka nufi wurin cin abincin tare yana fad'in." Hauwa ta kai k'arata wurin Hajja Amina, don Allah tsakanin ni da ita wanene mai gaskiya."
Na gyara masa kujera ya zauna yana ta kallona.

Ban tanka masa ba wai don ba ni da abin fad'a kawai maganar ce ta ishe ni haka, na ma daina sanya musu baki abinda ya shafe su ne wannan tunda shi har yanzu gani yake yi yafi ta gaskiya.

Duk yadda ya so da mu yi maganar Hauwa akan abinda ta yi ban biye masa ba, ya gaji da takalo maganar ya bari ya shiga wata ina d'an taya shi kafin a kira wayarsa.

Momi ce ban san me ta gaya masa ba na ji dai yana fad'in." Subahanallahi, bari gani nan zuwa kada ki sake tashi tunda jiri na dibanki bari na zo yanzu."
Ya kashe wayar yana kallona ni ma shi din nake kallo da 'yar damuwa yake fad'in." Bari na sake dubo mai jiki na dawo Amina." A tak'aice na ce." A ce ina yi mata sannu.

Ya mike ba tare da ya kwashi wayoyinsa ba ya nufi hanyar fita yana fad'in." Yanzu zan dawo in sha Allahu."
Ban ce masa komai ba illa ido da na bi shi da shi har ya fice, ina d'an mamaki jiri kuma?

Allah dai ya kawo mata sau'ki shine abinda za a ce.

Dama kusan tare muka ci abincin don haka ko minti biyar ban kara a wurin ba ni ma na tashi tare da diban wayoyinsa da ya bari na
shige d'aki wanka na sake yi na shirya da kayan bacci na zauna jiran sa.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*2K Complete a TALGRAM WHAT'S APP GRUOP 1K VIA 0542382124....

BINTA UMAR GTBANK.*
*V-VIP AREWA PEN*
*07084653262*
*111*
Wayata na d'auka ina dubawa amma hankalina gabad'aya yana wani wuri.

A k'alla yanzu da fitarsa kimanin minti talatin kenan, a ganina idan ba wata gagarimar matsalar ba ce ya ci ace ya dawo kuma idan kuma ba acan din zai kwana ba.

Zuciyata ta dinga yi mini sake-sake abubuwa da yawa ina dojewa ba ni so na aminta da sashenta ya zamana kuma ba hakan ba ne, uzuri akan ciwo abu ne mai kyau wanda hakan yake da tabbacin kai ma ba ka wuce a jarrabe ka ba.

Amma tabbas zai dawo komai dare tunda duka ga wayoyinsa a hannuna.

Sahura na ga ta turo mini voice note na shiga da sauri na kunna ina saurara.

Ni sai abin ma ya ba ni dariya wallahi..
Chapter 160 · 0% Book details