← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 276

Sashe 50

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kayan sari kona miliyon nawa kike da bu
ata zasu iso hannunki a cikin kwana biyu da izinin Allah*
*Ni Badiat Ibrahim Mrs Bukhari
awar Sabuwan maigogul, Aminiyar Iyabo, uwar
akin Tani Shanono na gwada na san amfaninshi, kema
ar uwa ki kwada zaki bani labari siyan nagari maida ku
i gida.*
*Mun sani yanzu yana da kyau duk abinda zamu siya musan ingancinshi da nagartarshi bawai muita siyan magungunan mata kara zube ba.*
*Wannan kamfanin kayansu babu algus ko almundahana a ciki, da tsoron Allah da
warewa gami da gogewa ta sanin* *yadda ake sarrafa magunguna suke aikinsu, cikin nagarta da gangariyar tsabta.*
*Abu mafi sha'awa komai a cikin kwali yake a rufe kirib*
*ga ka
an daga cikin abubuwan da kamfanin yake samarwa*
*Tsumin dadi har Madiga tareda gunbarshi*
*Tsumin no excuse mela
abin bita zaizai*
*Gumbar dare daya wanka goma, dana gari da zumarta da tsuminta duk muna dashi*
*Zumar hana bacci gumbarta da garinta*
*Munada Arabian sabaya tare d Sudanese sabaya*
*Da zumarta*
*Sabaya ce dake cuko da
a mace duk ramarta, da
anjamewarta*
*Itama da zumarta*
*muna da mummuna da aiki*
*Akwai tsumi da gumbar ta da zaune tsaye*
*muna da kogin da
*Abangaren sanyi sun samar ma mata maganin matsolilinsu*
*muna da fitattun maganin sanyin da yake fata_fata d sanyi yayi mishi korar kare*
*Khanzur Rahman herbal formular*
*Sanyi clear syrup*
*7 days for chronic infections flusher*
*Sannan kuma muna da* *Package amarya*
*Package Uwargida*
*Package irin na zawarawan da suke shirin sabon aure*
*Bugu da
ari wannan kamfani yana sarrafa magungunan maza ba a iya na mata ya tsaya ba, wannan kamfani magungunan da yake samarwa suna da yawa wannan tsakurene daga cikin kayansu*
*Da sauransu da sauransu wanda bamu ambata ba.*
*Ba fa a iya haka muka tsaya ba muna d cancada cancadan zannuwan Gado da carpet*
*Domin neman
arin bayani ku tuntu
eta a kan lambar wayarta kai tsaye*
+2348032089456
*27*
Kafin ma ya kammala wayar Sukairaju ya shigo, ya d'an tsaya daga gefe bayan ya gaishe mu.

Sai da ya bari ya gama tukkuna ya risina tare da mika masa wayar hannunsa.

Ya kar'ba kimanin minti biyar ya gama dubawa ya mika masa wayarsa a nutse ya ce." Kada ku damu in sha Allahu alheri ne, gobe za mu tattauna da gidan jarigar Amana daily trust zan wanke kaina bisa zargin da jama'a suke yi mini.,
Sukairaju ya sake risinawa yana fad'in." Ranka ya dad'e lamarin ne ya karad'a gari mussaman social media jama'a sai maganganu marasa dad'i suke yi akanka, dalilin da ya sanya hankalinmu ya tashi kenan"
Ya furta." No kada ku damu zai wuce an riski kalubale iri iri, an cimma nasara kuma, wannan ba komai ba ne, zan dai yi bincike akai sosai."
Hajja ta ce." Amma dai Alhaji Sammani bai kyautawa rayuwarsa ba wallahi, yanzu wanene ya san iya adadin mutanan da ya takewa hakki."
Ya ce." Sai Allah Hajja domin wad'anda suka rasu a 'karkashin ayyukana suna da yawa wallahi, kuma duk wanda na tabbatar da mutuwarsa zan fitar da hakkinsa na bayar, shi Sammanin shine ya zalince ni."
Sukairaju ya k'ara shigowa a karo na biyu da sauri ya nufo shi da waya, kafin ya k'arasa ya dakatar dashi yana cewa." Sukairaju na gaji da magana daya don Allah kada ka k'araso nan, na san inda matsalar take zan kuma yi maganinta."
Ya tsaya bai k
rasa ba kamar yadda aka umarce shi amma bai fita ba ya sake sunkuyar da kansa da ladabi ya ce." Sir lamarin ne ya sake yin tsamari ne wannan yana da kyau ka duba domin daga gida abin ya sake fitowa."
Shiru ya yi bai ce masa komai ba, sai hakan ya bashi damar isa wajensa ya mik'a masa wayar tare da nuna masa abinda yake zo ya gani.

Da sauri na ga ya d'ago kansa yana kallona da mamaki mai yawa a tare dashi.

Ban kawo komai ba balle na zargi abin ya shafe ni.

Ko da ya gama karantawa bai ce komai ba ya bashi umarnin fita.

Numfashi ya fesar kafin ya yun'kura ya tashi ya nufi samansa ba tare da ya sake wata magana ba.

Gabad'aya hankalinmu ya tashi har mahaifiyartasa, ta ma manta wadda take dashi fadi take yi Amina tashi ki bi shi maza domin yana buk'atar wani a kusa dashi.

Ni kaina sai bayan na tashi din ne naga kamar rashin dacewar hakan tunda ga amaryarsa a ganina ita ya kamata ta je kusa dashi.

Sai na dan tsaya da tafiya.

Ta sake fad'in." Maza ki je mana, kin san shekaru sun fara hawa kansa kada ya yanke jiki ya fad'i.

Gabana ya buga da karfin gaske dana tuna rashin lafiyar da yayi kwanaki fad'uwa ya yi har sai da aka d'auke shi bai san inda kansa yake ba.

Na nufi saman da sassarfa da fargabar abinda zai biyo baya.
yana zaune a gefan gado ya d'an tallafe ha'barsa da hannu kamar mai nazari na nufe shi yayin da tausayinsa yake tsirga mini, kusa dashi na zauna a nutse na ce." Baba kada tunani ya haddasa maka ciwo, kaifa babba ne, kuma kayi gwagwarmaya menene baka gani ba don Allah kada ka damu akan wannan abin, muna cikin tsananin bukatarka a yanzu."
Ya dube ni a nutse ya furta." Ke da yaranki Kuna buk'atar hakkin tsohon mijinki Aminu Salihi wanda na take bayan rasuwarsa ko?"
Gabana ya wani buga da mugun karfi.

Na zuba masa ido Ina kallo lebana yana rawa tsabar mamaki da tashin hankali.

Ya d'auki wayarsa dake saman dirowa ya farara labule.

Minti uku ya miko mini, babu gardama na kar'ba wani pege ne da ban san me shi ba, akayi tagging dina wanda ya yi rubutun yana magana akan yadda Alhaji Tajo yake amfani da matasa domin tara dukiya har yana bada labarin Yaya Aminu da irin bautar da ya yi masa yana kuma jadaddawa a rubutunsa cewa da yawuna ya fito yake magana akan hakkina dana yarana da aka take.

Cikin wani irin yanayi na tsantsar damuwa da tashin hankali na shiga fece book din ina ta scrolling abinda yake ta trading kenan.

'Cewa jita jitar da ake ji dangane da Alhaji Tajo da ma'aikatansa gaskiya ne, domin kuwa matarsa wadda yake aure a yanzu tsohon mijinta Aminu Salihi kafin rasuwarsa ya yi aiki a karkashinsa wanda kowa shaida ne dangane da yadda ya bautata masa a wata majiyar ma ana cewa sanadiyar aikinsa ne ya kamu da lalura sa'i daya kuma ya kore shi daga aiki domin ya gane bashi da mamora karfinsa ya kare, bayan ya sallameshi daga aiki bai bashi komai ba, a haka Aminu Salihi ya yi ta jiyya har ya rasu da damuwar hakan.

Rahoto ya tabbatar da cewa da yawun Aminu Salisu mai hula wannan 'yar kasuwar nan da ta yi shura wajan fashion designer a kafafan sadarwa da amincewarta wannan rahontan ya fita."
Gidajen jaridu da wanda suka kai da wanda basu kai ba sai posta hoto na da nasa suke yi.

Wasu ma harda hoton yaya Aminu da Kamalu da Yusi.

Kuka ya k'wace mini da k'arfi na sanya hannu na toshe bakina Ina kallonsa hawaye na shatata.

Ya kar'bi wayarsa ya ajiye ya matsa daga kusa da ni, ya ja jikinsa ya jingina da allon gadonsa.

A hankali na matsa kusa dashi ina kuka na ce." Wallahi tallahi Baba ba da yawuna aka fitar da wannan maganar ba, asalima ban san me pege din ba idan ka lura sabon shafi ne ba a jima da bud'e shi ba, wata'kila an shirya mini hakane domin a 'bata ni a wurinka, ba zan ta'ba cin zarafinka a duniya ba Baba idan ban ya'da alherinka ba ai ba zan yad'a sharri a kanka ba, ka yarda da ni wallahi ba ni da masaniya abinda yake faruwa, babu hannuna."
Ya dube ni a yayin da na gama firgicewa domin hankalina ya kai ma'kura wajan tashi jin yadda lamarin yake nema ya sauya salo, hakika duk wanda ya shirya wannan lamarin ya yi mini farin sani.

Na san dai kafin k'addarar aure ta ratsa tsakanina dashi a ko'ina na kan saki bakina na soki sha'aninsa na kushe shi, na nuna ba na daya daga cikin mabiyansa idan aka tambaye ni hujja ba na rufewa fad'a nake yi.

Ban ta'ba tunanin hakan zai janyo mini gagarimar matsala ba tunda ban ta'ba zaton aure zai ratsa tsakaninmu.

Ganin yadda na kanainaiyeshi da ro'ko da magiya ya sanya ya sassauta fuskarsa ya gyara zamansa a tsanake ya dube ni yana ce wa." Me yasa tunda muka yi aure ba ki gaya mini cewa Aminu Salihi ne mahaifin Yusuf ba.

Hannu na sanya na goge hawayen da suke zuba na ce." Ban san ta yadda zan gaya maka ba wallahi, ni dai abinda nake so ka fahimta shine wallahi ba ni da hannu wajan wannan rubutun.
Chapter 50 · 0% Book details