Sashe 172
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jikina na kyarma na furta." Anti Yagana Hajiya Maryam ta mutu sanadiyar lalure-laluren da suka yi mata hijabi, ina tsoron kada 'yan uwanta da jama'a su jinginta rasuwarta da ni da Hauwa, ai kin ji abinda daya daga cikin 'yan uwanta take fad'a ko?"
" 'Karamin tsaki ta yi kafin ta ce."Amina duk wanda zai alak'anta rasuwar matar nan daku to dama can ba masoyinta ba ne.
Su kansu 'yan uwan nata da suke ko'karin tashin husuma ba kaunarta suke yi ba tunda har suke jingina rasuwarta da wani abu daban.
Kishi halak ne kuma duk gidan da aka had'a mace fiye da biyu ana samun irin wad'annan matsaltsalun.
A ganina wannan ba wani abun damuwa ba ne, rigima ce suke nema kuma in sha Allah rabbi har a share makoki ba za mu tanka musu ba.
Ni gidan ma ba zan sake shiga ba tunda na lura duk yawansu babu mai dattako a cikinsu.
Rashi kam ba su kadai suka yi ba mutane da yawa ne domin Hajiya Maryam bango ce majingina kuma uwar marayu har ma da masu uban.
Don haka iyakacin k'aunar da za su nuna mata su bita da addu'a tare da rungumar abinda ta bari shine kawai sakamakon da za su yi mata bayan rayuwarta.
Don haka ki samu nutsuwa ki kuma daina tunanin kina da hannu lokacinta ne kawai ya yi kuma babu wanda ya isa ya tsalle rana da sa'in komawarsa ga Allah."
Maganganun anti Yagana sun d'an sanya ni mini nutsuwa kad'an amma har yanzu zuciyata ba ta daina yin tsalle akan abinda na ji yana fitowa daga bakin 'yar uwar marigayiyar ba.
Babanmu suka iso tare da baba Sule da Ummansu Hadiza kamar yadda ya fad'a.
Baban Saude ne har yanzu bai shigo inda nake ba, anti Yagana kuma ta gaya mini tare suke da Babansu Fadila har da Baba Madu wanda ya kasance babban yayansu Mamanmu, mahaifin Babandi.
Kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Sai wajan biyar saura tukkuna suka shigo da d'an yawansu duk muna zaune a babban falo.
Maigidan tare da iyayenshi biyu 'yan uwan mahaifinsa da kuma Baban Saude Baba Madu da Babansu Fadila.
Falon ya cika da sabuwar gaisuwa tare da yi wa juna ta'aziya.
Ta mussaman suka yi mini gaisuwar na amsa yayin da nake jin cikowar ruwan hawaye idona.
Ina jin Hajja tana tambayar Alhaji Sa'idu Hajiya saratu ya ce tana can gidan mai rasuwar tunda koda suka sauka nan ta shiga ba ta fito ba kuma har yanzu.
Suna ta tattauna hirar marigayiyar yayin da maigidan ke sake basu labarin irin wahalar da ta sha na jinyya farkon zuwansu asibitin a yayin da aka dora ta akan magani an ga sauyi sosai yanayin yadda yake magana da alhini shi yake nuna mutuwar ta dake shi kwarai da gaske kwarmin idonsa ya zurma fatar lebanshi ta bushe kamar wanda ya yi azimin shekara bai sha ruwa ba.
Irin wannan yanayin ya shiga a lokacin rasuwar tsohon mijinta Alhaji Amadu da kyar ya dinga cin abinci.
Yanzu ma ba na raba daya da biyu rabonsa da abinci tun da aka yi rasuwar kwana da yini kenan.
Gabad'aya sun jajanta sosai kuma kafin tafiyarsu sai da Baban Saude ya jagorancemu gabad'aya muka yi mata doguwar addu'a wadda take d'auke da surorin da ake karantawa mamaci.
Yamma likis suka yi mana sallama gabad'ayansu har da Hamusu da Babanmu domin cewa ya yi shi ma ba zai zauna ba tafiya za su yi tunda sun yi abinda ya kawo su.
Shi kansa maigidan ya so su kwana ko daya ne amma gabad'aya suka ki har da kawunan nasa.
Hajiya saratu ce kawai ta zauna ta ce sai an yi sadakar ukku tukkuna.
Yallabai din ya bada umarnin mayar dasu Babanmu gida. su Baban Saude kuma dama a motarsa suke tafe.
Sai bayan sun tafi tukkuna Hajja ta dinga fad'a wai mai yasa anti Yagana ba ta jagoranci Ummansu Hadiza zuwa gidan mai rasuwar ba.
Anti Yagana ta ce mata mantawa ta yi shiyasa ni kuma nasan ba haka ba ne ita da kanta ta gaya mini k'afarta ba zata sake taka gidan ba.
Gaisuwar da ta yi wa maigidan ma ta isa ba sai ta je ta yi wa 'yan uwanta ba tunda dukkaninsu taron tsintsinya ba share ne.
Sai bayan magariba Hajiya Saratu ta shigo.
Ina d'aki lokacin na idar da sallah ban ka ga tashi daga kan daddauma ba ta shigo.
Na saki fuskata sosai Ina fad'in." Mai sunan Mamana ina yini?"
Ta zauna gefan gadona a nutse tana fad'in." Lafiya lau Yayata kuma diyata."
Na yi murmushi a hankali na ce." Ai tun d'azu aka ce kina can gidan marigiyar ina nan ina ta zuba idon ganin Mamana"
Ta dafa kafadata tana fad'in." Ga ni na shigo ai Amina ya muka ji da hakurin Maryam lokaci ya yi Ubangiji Allah Ya gafarta."
Na amsa da "Amin Ya Allah." Cikin wata iriyar murya.
D'akin ya d'an yi shiru wanda ya yi daidai da lokacin da anti Yagana ta fito daga bandaki daure da alwala.
Ta saki fuska tana fad'in." Hajiya kin shigo kenan?"
Ta ce." E wallahi Yagana ya gida ya yaran, ya muka ji da hakuri?"
Anti Yagana ta ce." Ha'kuri da godiya Hajiya Allah dai ya jikinta da rahama."
Da Amin ta amsa yayin da take sake dora hannunta a kafad'ata.
Anti Yagana ta d'auki daddauma da hijabi ta koma can gefe domin gabatar da sallar magriba.
Ta ce." Ai ni ban fito ba daga gidan ba sai da na gabatar da sallata tukkun." Na yi murmushi kad'an ban ce komai ba.
Sai ta ce." Amina akwai maganganun da nake so mu tattauna dake idan babu damuwa."
Cikin nutsuwa na ce." Babu damuwa Hajiya Ina sauraranki."
Ta sauke ajiyar zuciya a tsanake ta ce." Duk abubuwan da suke faruwa a zamantakewar gidan nan ina da labari.
Da har Ina cewa tunda matsalar ta'ki ta'ki cinyewa zan wanko kafata takasan na zo naji komai daga gare ki nasan ke ba za ki yi mini karya ba, ba kuma za ki goyu da bayan mijinki ko ki goyu da bayan Hauwa ba, idan har kema kina da lefi za ki gaya mini gaskiya sanin da na yi miki tun farkon fari.
Ta nisa kafin ta cigaba da cewa.
Sai gashi kuma
rasuwar Hajiya Maryam ta ratsa hakan sai ya kara ba ni k'warin gwiwar zuwa domin na ji komai daga gare ki, Amina da hankalinki za ki biyewa Hauwa da har yanzu ba ta san rayuwa ba, mai yasa kuka kasa bawa mijinku k'warin gwiwa da taimako wurin ganin ya rike amanar abokinsa.
Jimawata gidan marigayiya Maryam tana da dalili domin 'yan uwanta ne suka zaunar da ni suna wassafa mini irin zaman da kuka yi da ita da irin abubuwan da kuka dinga yi mata na rashin kyautatawa, idan har hakan gaskiya ne Amina ban tsammata daga wurinki ba domin kallon da nake yi miki kin wuce a ce a yanzu an zauna a nuna miki abinda ya dace idan Hauwa ta yi hakan ba zan yi jayayya ba dama na san halinta da na ji sunanki a ciki ne sai hakan bai yi mini dadi ba, mai ake gudu ne a zaman tare irin wannan fa, yanzu ina Maryam din take ta mutu ta bar duniya to mai zai sanya ba za mu yi hakuri da rayuwa ba.
Gashi Hauwa har sai da ta yi sanadin da Tajo ya saketa saboda kuma bata da hankali ta tafi ta bar yaro jinjiri fisabillahi ina hankali da tunaninku yake?"
A nutse na dubeta tare da cewa." Mamana abubuwan da yawa sun faru masu dadi da akasin haka.
Amma zan gaya miki wani abu da ba kowa ya san shi ba sai ni sai Ubangijin da ya hallice ni wallahi tallahi ban ta'ba kin Maryam a cikin raina ba.
Tabbas akwai kishi kuma kowace mace tana da nata daidai gwargwado amma ni Amina ban zafafa shi akan matar nan ba duk sanda zuciyata za ta kitsa mini mummunan abu akan kanta nakan yi tirr da ita da take bijiro mini mugun nufi akan matar da alherinta ya fara riskata kafin wata mu'amula mai karfi ta ratsa tsakaninmu.
Duk abubuwan da suka dinga faruwa yaranmu suka had'a amma ni da ita sa'insa mai muni bata ta'ba hadamu ba, kuma lafiya lau muka yi sallama da juna har ta koma ga Ubangijin talikai.
Har yau har gobe ban k'ulleceta ba ban kuma k'ullaci yaranta ba ina jin tausayinsu kuma ina yi musu kallo irin na uwa." D'akin ya shiru bayan ajiye maganata na ja numfashi cikin bushewar ma'kogwaro na cigaba da cewa." Magana akan Hauwa kuma ni ba zan iya ce miki komai ba, abinda dai na sani shine Hauwa ta yi mini kokari kwarai kuma babu kishi da ganin kyashin juna a tsakanina da ita ni fa a tunanina kenan, domin Hauwa 'yar uwa na dauketa ba kishiya ba.
Duk hanyoyin na bi domin na nuna mata abubuwan da take ba su da kyau na bi, na yi bakin kokarina amma ba ta ji ba.
Dalilin rigimarsu da maigidan tana da ala'ka da ni da ita mai rasuwar da yaranta.
Mun daidaita a wattanin baya har na so ni da ita mu je mu dubata a lokacin da ta kwanta a asibiti amma fafur ta'ki sai tare da Baba Tabawa na tafi mai aikinm kenan.
Wannan shine abinda zan iya gaya miki Mamana bayan hakan ban san abinda yake tsakanin Hauwa da mijinta ba tunda tun kafin ta aikata haka na yi iyakacin bakin kokarina a kansu ita dashi amma babu wanda ya saurareni a cikinsu."
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.
Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.
To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.
Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.