← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 212 OF 276

Sashe 212

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun jima ba su miyar taushe a gidan ba wannan dalilin ya sanya mini mugun mararin son cin towon.

Ina ci muna hira da su jefi-jefi Hauwa ta sakko kai tsaye dakinta ta nufa sai ta d'an tsaya tana kallona kafin ta ce." Maigidan fa baya jin dad'i Amina."
Gabana ya buga da k'arfi a take a lokacin na ji abincin ya fitar mini daga rai Allah ma dai ya sa na ci da yawa.

Na daidaita yanayina sosai kafin na ce." Mai yake damunsa?"
Ta d'an ta'be bakinta tana fad'in." Ciwon kai na ji yana gayawa likitansa yanzu tun rana da shi dai ya yini na yanzu ya yi tsanani ko 'daga kansa baya iya yi yana kwance."
Na yi 'kasa da kaina abin har ya kai ga kwanciya irin haka wace irin matsala ce take damunsa da har zai ajiyeta a ransa ta haddasa masa ciwo.

Ta shige dakinta ba ta sake yi wata magana ba.

Kafin na haura saman sai da na sanyo hijabi jin cewa likitansa yana kan hanya
Yana kwance shar'be a gado ya dafe kansa da hannunsa.

Na zauna gefansa jiki a mace ina fad'in." Baba baka da lafiya ashe?"
Ya dube ni da gefan ido ya furta." Ciwon kai ne Amina yanzu nan ya sake tsananta."
Na ce." Kana jin sa ashe a hankali a hankali ba ka yi magana ba sai yanzu da ya kwantar da kai an ta'ba wasa da lafiya ashe."
Ya yi shiru bai ce komai ba.

Na gyad'a kaina ina fad'in." Ni ba yarinya ba ce duk yanayin da kake ciki ina hankalce ban buk'aci dole ka gaya mini sirrinka ba wata'kila baka son kowa ya sani shiyasa ka yi shiru abin yana cin ranka ya kamata a ce ka sassautawa kanka dalilin gudun faruwar mummunar abu akwai shekaran girma a tare dake kuma idan ban manta ba kana da hawan jini bai kamata a ce ka dinga ajiye wani abu a cikin ranka ba.

Amma ina so na gaya maka cewa ko ka fad'a ko baka fad'a lallai kana cikin damuwa domin gabad'aya al'amuranka sun canza a tsukin lokacin nan."
Ya yun'kura ya tashi zaune yana kallona da wani irin yanayi ya ce." Lallai ina cikin damuwa Amina amma ban san yadda zan yi na fitar da kaina daga cikinta ba."
Na ce." Duk abinda ya yi tsanani ai maganinsa Allah kaine ka ke da hanyar fitar da kanka daga cikinta idan ka sanya hakan a ranka."
Ya gyad'a kansa yana kallona amma bai ce komai ba.

Jikina ya sake yin sanyi na d'an riko hannuna a hankali na ce." Idan babu takurawa ka gaya mini damuwar da take damunka ko Allah zai sanya ina da shawarar da zan baka."
na kudi ne w
nnan littafin Yar uwa don Allah a duk inda za ki gan shi kada ki karanta sai kin biya ni hakkina.

Ya furta." Malam 'Daha ne ya ba ni 'yarsa amma ban san ko wacece daga ciki ba, kin san dai gidansa cike yake da yara ko?''
Kunnena ne ya yi dumm! kamar irin kumfar sabulu ta shiga ciki na ji ya sake rintse hannuna yana fad'in." Ban zan iya bijire masa ba Amina wallahil-azim ba zan 'ki 'karbar tayinsa ba."
Na zuba masa ido kawai ina kallo bakina ya yi nauyi na rasa ma abinda zan ce saboda zahiri na 'kadu da jin maganar nan gidan Malam D'aha babu wata cikakkiyar budurwa duk matasa ne kuma mafi akasari daga sassan gidan suke fitowa alamu sun nuna wasu daga ciki 'ya'yan yaransa ne irinsu malam Rabi'u.

Jikokinsa kenan
Hajara ita ce kadai 'yar budurwar da ta fara tasawa tunda ta fara 'kirgar dangi sun yi cibir-cibir a cikin riga ba ma su kai a sanya musu rigar mama ba.

Na daure na ce." Ai duk babu wata budurwa cikakkiya a gidan Malam D'aha."
Ya ce." Akwai uku da bai aurar da su ba sauran jikokinsa ne a cikin ukun ya ba ni d'aya ban santa ba ni ma."
"Hajara ce abinda zuciyata take raya mini kenan.

Muka yi shiru ni dashi muna duban juna Hauwa ta shigo sanye da hijabi a jikinta ta same mu a haka mun k'urawa juna ido ga hannuwanmu a ri'ke
ta kasa jurewa muryarta tana rawa ta ce." Ka ce baka da lafiya maganar duniya na yi maka baka tanka mini ba kana kwance kana jina yanzu gashi kuma yanzu na shigo na gan ku ma'kale da juna wallahi Amina ku ji tsoron Allah hakkina ba zai bar ku ba ba zan ta'ba sahale muku ba a ranar lahira."
Na juya da mataccen jiki ina kallonta.

Wata gaud'iya da ita ana ga gabas tana ga yamma.

Karamin tsaki kawai na ja ban ce komai ba na cire hannuna daga cikin nasa.

Ya sake kamowa yana fad'in." Kin ce akwai shawarar da za ki ba ni ko Amina wallahi ba ni son auran da ake ko'karin ma'kala mini abinda yake zuciyata na gaya miki tunda kin matsanta ki ji kada ki d'auki maganata a matsayin dad'in baki a yanzu dai babu ajandar aure a tare budurwa ko bazawara kin san matsayin Malam D'aha a wajen mahaifina da ni kaina da irin gudumuwar da ya ba ni a rayuwa abu ne mai wahala na yi ja'in'ja akan wannan umarin nasa Amina
ba ni da mafita ne dole na gaya muku halin da ake ciki daga yau zuwa ko wane lokaci za ku iya jin labarin d'aurin aurena domin gidan Malam D'aha ba'a bida'a idan an d'aura aure yarinyar zan je kawai na d'auko."
Abin ya daki Hauwa k'warai da aniya ta zuba masa ido cikin k'aduwa tana fad'in." Aure da gaske za ka yi to kai yaro ne da za ka ce an ma'kala maka daman can kana so akwai wanda ya isa ya yi maka dole ne? ashe kana da lafiya ta mazantaka da kuzari irin na maza tunda har zaka iya 'karbar auran budurwa 'kan'kanuwar yarinya.

Ya 'kankance ido yana fad'in." Ba ni son hauka da rashin hankali Hauwa ki kiyaye ni wallahi kada ki sake ki fusata ni."
Ta ja tsaki ba ta sake cewa komai ba ta kad'a kanta ta kama hanyar fita.

Ya ja tsaki tare da sake juyowa gare ni yana fad'in." Ya za mu yi ne Amina ta ina kike ganin zan warware wannan mas'alar da na shiga.

Ajiyar zuciya na sauke a nutse na furta." To ai ni ban isa na hana umarinin Ubangiji ba.

Na d'auka wata matsalar ce ta daban shiyasa ka ji na ce maka ka gaya mini zan baka shawara.

Lamarin aure kuma ai yin Allah ne Amina bata da hurumi anan sai addu'a da fatan alheri."
Ya ri'ke hannuna sosai yana fad'in.

" Kin amince a yi? kina ganin babu komai idan an yi din?"
Na gyara kaina gabana na dokawa na ce." Idan ma da matsala ai ban isa na sani ba tunda ni hallitar Allah ce a karan kaina ban san abinda zai same ni daga yanzu zuwa gobe ba kaga kuwa ba ni da abinda zan ce anan kamar yadda na fad'a da farko Allah Ya sanya alheri yasa abokiyar arzikinka ce.

Wannan shine kawai addu'ar da zan yi."
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta.'' Ban za ci zan samu ha'din kanki cikin d'an'kankanin lokaci ba Amina.

Lallai na yi sa'ar samun mace tagari mai ko'karin ganin ta samar mini da nutsuwa cikin kowane yanayi na gode sosai Allah Ya yi miki albarka."
A tak'aice na amsa da amin ina ta kallonsa ganin ya wartsake idan ma da ciwon kan to a kashi dari hamsin ya sauka sai abinda ba za a rasa ba.

A haka likitansa ya zo ya dudduba shi yana fad'in jininsa ya hau kad'an shine kuma ya haddasa masa tsananin ciwon kai da jirin da yake ji ya zama dole ya daina tsanantawa kansa damuwa.

Ya tashi ya fita minti talatin a tsakani ya dawo da magungu
a a leda ya yi bayanin yadda ya kamata a ce an yi amfani da su daga yanzu.

Ban sauka ba sai da na tabbatar da cewar ya ci abinci sosai sannan ya sha maganin a gabana tukkuna na yi masa sallama na sauka gwiwata kamar an rad'e da gora saboda mugun sanyin da jikina ya yi jin wannan batu......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124.....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*143*
Ni jin wannan batu gabad'aya ya kassara mini dukkanin karsashin jikina.

Na yi shiru zuciyata na harbawa tare da tariyo maganganunsa akan auran da yake yi wa lak'abi dana cushe.

Ba ni fargabar ya yi aure a gidan nan saboda na riga na san matsayina a zuciyarsa idan ma yana amfani da kalaman yaudare wajen nuna mini soyayya tabbas to akwaita a zuciyarsa ko da kuwa da akwai matsugunin wata.

Matsalar dai anan 'kankanuwar yarinyar da zai auro ya kawota cikinmu shine tashin hankali tun lokacin da yake gaya mini zuciyata take hasaso mini Hajara ce domin kaf yaran da suke gidan Malam D'aha itace a samansu ba su kaita girma ba ita zamu kira da budurwa amma a rashinta domin yadda take a tsamure a tsuke sai uban tsayi bana tsammanin ta fara jinin al'ada.

Lallai wannan babban lamari ne da ya tunkaro mu gabad'aya domin idan har Allah Ya kaddara auran nan to sai da ya rainin yarinyar nan duk da matarsa ce ba zan yarda ya haye musu kan d'iya ta had'u da lalaruba.

Malamai suna ta wa'azi kan cewa iyaye su daina irin wannan auran na cutarwa to da haka za mu kira shi ma a wannan zamanin domin dai muddin a fake da cewa sunnar manzon rahama ce yin haka to akan jefe yara cikin halin damuwa a gaba.

Dalili zamanin Annabi Muhammadu S.a.w daban yake da wanda muke ciki a yanzu idan an fake da cewa za a yi koyi da shi akan abinda ya wanzar lokacin zamaninsa ana samun matsala dalili shi daban yake cikin duk wata hallita.
Chapter 212 · 0% Book details