Sashe 119
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni dai kawai na zama kamar mutum mutumi tare da zubawa sarautar Allah ido, ita da mijinta suka yi duk yadda za su yi wurin mayar dashi makaranta domin ya samu shedar kammala secondary tunda wannan da ya gama sun fi karfi akan al'kur'ani da sauran littafan addini.
Ban ce musu komai tunda bai sanya ni a ciki ba kawai dai na yi masa shiru har sai da yaron ya fara zuwa makarantar tukkuna watarana da daddare yake sanar da ni a takaice na ce ." Allah Ya taimaka." Daga haka ban sake magana ba.
Na gyara kwanciyata ina lumshe ido.
Na ji maganarsa yana cewa." Tashi zaune ina so na yi magana dake."
Na tashi kamar yadda ya buk'ata din ban ce komai illa Ido dana zuba masa."
Ya sassauta sosai kafin ya furta." Kina ganin kamar ba a kyauta miki ba ko Amina."
Na ce." Da aka yi me?"
Ya nisa kafin a hankali ya furta." Kin san akan abinda nake magana ai."
Sai na gyada kaina a tsanake na ce." Ai kai ma kasan ba a yi mini adalci ba, ni ban iya gori akan komai ba balle akan 'ya'ya, amma itama ai ta haihu me yasa take ko'karin ta karfi sai ta raba ni da yarana.
Wannan wata hanya ce da ta 'bullo da ita mai wahalar ganewa domin ni har ga Allah tunda ka auri matar nan ba zan ce maka ga abinda tayi mini na rashin kyautawa ba, idan har ma na fadi wani aibunta na yi mata sharri.
Amma ta bullo da wani lamari da zai sanya mini shakku akanta ya za a yi ta k'wace mini yarana kai kuma ka dinga goyuwa da bayanta a ganinka kun yi mini adalci ko kuma dangin Babansu."
Ya yi shiru d'an wani lokaci kafin ya furta." Ki yi hakuri giwa ba wai ina goyuwa da bayanta ba ne a a Ina so na nuna mike cewa duk wanda ya nuna k'auna ga abinka kai yake so, Maryam bata da mummunan nufi akan ku balle yaranku.
Ai na d'auka abinki abina ne, ban haifi yaran ba amma tunda ta tsatsonki suka fito wallahi tallahi ji nake yi kamar ni ne ubansu.
Ki yi hakuri idan har hakan lefi ne, kuma kin ji hakan bai kwanta miki a rai ba yaranki za su dawo hannunki."
Yadda yake magana cikin kulawa da taushin harshe sai ya d'an ba ni tausayi kuma na tabbatar da cewa abinda ya fad'a akan yaran gaskiya ne domin ya nuna a aikace.
Na goge kwallar da ta ciko idona na furta." Ai ban isa ba, idan har ka dawo mini da su za ka iya kiran Baban Saude ko anti Yagana ka gaya musu abinda ban yi ba.
Ku ri'ke su kawai kai da ita Allah Ya kula mini da su."
Ya furta." Saboda ni mak'aryaci ne ko? ai magana za mu yi dake anan domin mu samu matsaya ba na so ki yi ta kallona da Maryam a matsayin masu son zuciya na ce idan hankalinki bai kwanta ba zan kawo miki yaranki kalas."
Girgiza kaina na yi tare da cewa." A a fa na bar muku wallahi Allah Ya raya su."
Ya yi shiru yana ta kallona ina goge hawayen da suka kasa tsayuwa.
Sai ya matso kusa da ni yana fad'in." Maryam son yarana ne da ita Amina idan na gaya miki yadda take hidima da gidan marayu sai kin yi mamaki ko'ina hannunta yana zuwa ba zata cutar da su ba."
Hanci na ja na ce." To." Sai ya rungume ni tsam a jikinsa yana fad'in." Yi shiru Giwata daina kuka ai nasan kin yi mini sadaukarwa na gode miki Allah Ya yi mini albarka.'' Ya fad'a yana dan shafa bayana.
Shiru d'akin na dan wani lokaci kafin ya ce.'' Kamalu zan yi alfahari da shi ga dukkanin alamu domin zamanshi gidan Momi ya fara wanzar da alheri koyaushe cikin koyar da 'yan uwansa hukunce-hukuncen addini yake yi, wannan dalilin ne ma ya sanya ni da ita Maryam din muka yanke shawarar kai shi makaranta ya samu takardar secondary kafin mu tura shi can makarantar da Salim yake karatu.
Sannan akwai massalacin dana gina yanzu haka ma mukkulin yana hannunsa domin wancan satin aka yi addu'ar bud'e shi ko ba na gari shine zai cigaba da jan ragamar massalacin kwanaki uku kenan mun fara bin bayansa sallah."
Na daga kai ina kallonsa da sauri na ce." Kamalun kuke bi sallah guda nawa yake ?"
Sai ya yi murmushi yana fad'in." E, ai ya kai munzali kuma ya ilimantu a mu'amula da aikinsa sannan ya balaga uwa uba ya fi da yawa wad'anda suka bin bayansa a sallah ilimi da sanin al'kur'ani yaron da yake da haddar izzu sittin a kansa a malami ne, ko dai kin raina ilimin nasa ne?"
Na girgiza kaina a hankali na ce." Ban raina ba smma abin ne da ban mamaki gaskiya."
Ya ce.'' babu mamaki da ikon Allah Amina ki godewa Allah kawai amma yaron nan ya samu horo kwarai wannan dalilin ma ya sanya ni jin sha'awar taimakawa makarantar iyakacin bakin kokarina."
Na yi shiru ban ce komai ba cikin zuciyata dai ina ta tasbihi ga Allah. (Kalubale ga iyaye mussaman wad'anda yaransu suka taso da fitina kada bakinku ya saba da zagin yaro ko aibata shi da jifansa da kalmomi masu muni.
Lallai Allah yakan jarrabi bawa ta hanyar da yaso yakan kuma sanya farinciki da yaye damuwa ta duka hanyar da ya so.
Ubangiji Allah Ya shirya mana zuria.)
To tun bayan rarrashin da ya yi mini akan lamarin da ya sake kutso mini na d'an samu sasaauci a cikin raina.
Na sake samun kwanciyar hankali kwarai a koyaushe idan Kamalu ya shigo mini cikin tsafta da kamala tare da nutsuwa babu wata damuwa ko kaidaici a tare da shi.Sai dai bangaran Hauwa kam kadaran-kadahan bata ce komai ba amma ko hirar Momi a ke yi a gidan har a gama uffan ba za ta ce ba sai dai ta yi ta jan tsaki.
Itama ya d'auke mata Khalil ya mayar da shi can ta dai daure ba ta yi bore ba ban dai sani ba ko sun haura ita dashi kafin faruwar hakan.
Twins ne kawai a gidan muke tare da su tunda suna bakin nono.
Su din ma wasu lukutan sukan jima a gidan har sai sun bukaci nono tukkuna za a dawo mini su.
Haka ni da ita muka cigaba da safara ba mu Legos ba mu abuja muna raba wattani shida ita kuma Momin tana Abuja tare da yaran domin koda na yaye twins ma gidanta suka koma gabad'aya domin nan ne ya zama matattara ta yara, kuma sun yi bala'in sabo da ita da masu aikinta..
Bayan shakara biyu.
Hauwa tana da yara biyu Khalil da mai sunana domin tun ranar da ta haihu uban ya yi mata huduba da Amina sai muke kiranta da Minal.
Ni ma nake samun wani cikin bisa tsautsayi da kaddara ya fita sakamakon wani mugun zazzabi da na yi mai zafin gaske lokacin duka bai fi sati shida ba. amma cikin ikon Allah fitar cikin da wata daya na sake samun wani lokacin ina tare dashi a legos.
Sai ya ce sai na koma abuja Hauwa ta zo.
Dana tambaye shi dalili kawai sai ya ce a gidan Baby Aish ta rasu haka zalika ma a gidan na samu matsalar ciwo mai zafi har cikinsa ya zube hankalinsa bai kwanta ba.
Maganar ma sai ta ba ni dariya amma na daure ban yi ba, saboda Ina gudun ya mayar da abin rigima ina dai ta nazari akan tunaninsa kamar akwai rashin tauhidi a ciki, baby Aish ga abinda ya assasa mutuwarta.
Ciki kuma da na samu ya zube wannan kuma ni dashi ba zamu taba cewa ga musababi ba, iko ne na Allah, kuma a dai gidan ai na samu cikinsu Hassana da Husaina gashi duka watanmu hud'u da zuwa ya Hauwa za ta d'auki lamarin tunda gaskiya yanzu muna zama na fahimtar juna.
Ya ce da kansa zai yi mata bayani dalilinsa.
Jin haka ya sanya na ce masa ba azanci ba ne yin hakan, kenan ita ba mutum ba ce, idan har yana zargin gidansa da matsala sai ya canza ba zai yiwu a ce saboda na samu ciki har ya samu matsala ya ce daga gidan ne idan ba rikici da neman tashin hankali ba.
Ya ce itama tana samun wani cikin sai ta dawo.
Ganin ya'ki fahimtata ya sanya na k'yale shi domin kuwa ko bayan hali akwai girma da nauyin shekaru da suka fara turawa, yanzu nan sai ya rikice mana.
Aka yi sa'a, Hauwa ba ta yi gardama ba. kwananmu biyar da dawowa abuja suka juya tare dashi.
Dama Khalil tuntuni ya bar hannunta da Minal kawai ta tafi tunda tana shan mama.
Bata yaye ta ba tukkuna.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.
Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.
'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.
A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*80*
Ni da baba Tabawa muka cigaba da zama a gidan.
Sa'i da lokaci yaran shigo mussaman a ranakun da babu makaranta su d'an yi mana yini kafin su koma.
Na cigaba da rainon cikin da yake mugun ba ni wahala duk na k'okale laulayi ya tisani a gaba.
Don ma gidan babu wata hidima da yawa ni kuma wani lokacin ba abinci nake iya ci ba.
Baba Tabawa itace ke hidimar yi musu abinci da masu gadin gidan da Masa'udu direbanmu na nan.
Nakan zauna na yi ta mamakin yadda baiwar Allan nan ta had'a kan yara wanda ta haifa da wanda bata haifa ba ta ri'ke duka.