← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 231 OF 276

Sashe 231

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na d'auki kusan minti ashirin kafin na fito cikin shiri na same su still a falon suna shan tea har da bread tare da dankalin da ta soya musu.

Minal ta ta so a guje ta rike ni tunda ta ga alamar fita zan yi.

Twins din suka biyota.

Ba ni son d'aukar musu yarinya nawa biyu kadai zan yi gaba da su ba kuma zan dawo cikin gidan ba muddin Hauwa na cikinsa.

Ya yi mana shiru bai ce komai ba.

Na ce da Minal din ta je ta d'auko mini bread din da take ci.

Wayo na yi mata ta kuwa juya baya da sauri nan na ri'ke hannun Usai Hassana ta biyo bayana muka fita na ja kofar da k'arfi daidai lokacin da na ji ta fasa ihu da karfin gaske.

Ayuba ya fito da mota muna ko'karin shiga ya fito da yarinyar ta yi wurjajan da kuka da majina yana goge mata da tissue.

Kamar kurma ya saka ta a cikin mota kusa da 'yan uwanta ya juya bai ce mini komai ba.

Sai da na shiga motar tukkuna na tuna da wayata a hannunsa na ce Hassana ta je ta kar'bo mini jim kad'an sai ga ta da wayar a hannunta, ta shigo ta zauna suna cike da murna za su fita Ayuba ya ja motar muka fita daga gate din gidan.

Ashiru k'aramin kaninmu yana ko'karin bud'e kwantenarsa ya tsaya yana kallon fitowarmu daga mota da yake har kofar gida Ayuba ya ajiyemu
Ya taho daa sauri kuwa yana washe baki "anti Amina sannu da zuwa."
Na amsa a tak'aice ina bawa Ayuba amsa yana tambayata da kamar k'arfe nawa zai dawo ya dauke ni na ce." Ya bari zan kira shi tukkuna.

Muka nufi gidan tare da shi yana ri'ke da hannun Usaina yana fad'in." Anti sun girma sosai ban taba ganinsu ba sai a hoto."
Na ce." Kai ma ai ka girma Ashiru ka zama saurayi ina rigimar abincin hantsi.?"
Da yake yana yaro dan rigima ne idan an sha koko da safe wajan goma zai dasa rigima abinci ka'ida ne ko ba a ajiyewa kowa dumame ba shi sai an ajiye masa idan ma ba su dashi ni nake bashi ko na yi masa sabo.

Idan sun dawo daga makarantar allo ba a gama na rana ba ya yi ta kuka har sai an sauke na rana sannan gidan za a samu lafiya.

Ya yi ta dariya kuwa domin ko ya mance wasu abubuwan da ya dinga yi tabbas ba zai mance wasu ba.

Ya bude mini kwantenar tasa cike da kayan masarufi awo ne kadai ba ya yi ina ta dubawa ina jin dadi ganin yadda yaro ya zama manemi shi bai yi fitinar su Kamalu da Saminu ba sai da kukan kuruciya.

Na ce." Aikuwa ni ma zan sanya hannuna a ciki Ashiru ya kamata a ce harkar nan an fad'ad'ata."
Ya dinga washe baki yana fad'in." Wallahi kuwa anti Amina Babanmu ne ya fara ba ni dubu dari da hamsin na fara a hankali a hankali Yayanmu Usaini ya sake ba ni dubu dari." Na ce." Ya yi daidai Hakan ni ma zan bada gudumuwata in sha Allahu."
Muka shiga ciki shiru Ina ta sallama.

Can Ummansu ta amsa ya ce." Ummansu Hadiza wata'kila bacci take yi domin kwana biyu ta yi fama da mura da zazza'bi.

Ta dago labule ganina sai ta kama dariya.

Na sauke ajiyar zuciya ganin yadda ta marabceta ni dama ina ta tararrabin kada ta kawo mana tangard'a a cikin lamarin nan amma yanzu yadda na hangi sukuni da annashuwa a fuskarta ya sanya na kori shakkun da nake yi.

Ta fara fadin." Maraba lale Hajiya Amina sannu da zuwa ashe tare kike tafe da yaran bakid'aya yanzu nan mutumin naki ya fita kasuwa amma ya ce idan ya gama d'aure wasu kayan da zai tura Ghana zai dawo ."
Na ce." Allah sarki babu damuwa dama ai zuwan na ki ne bari na shiga mu gaisa da Ummansu Hadiza na fito."
Tana cike da matsanancin farinciki ta ce." To shikkenan."
Na same ta a kwance a katifa shiru kamar ta rushe da ihu domin yanayin fuskata kadai ka duba za ka gane a cikin damuwa da take da b'acin rai.

Ta tashi zaune tana yar dariya "Amina maraba lale marhabun ai jiya babanku yake gaya mana kina tafe maraba." Ta sake fad'in haka tana janyo hannun Usaina tana cewa." Biyu sun girma sun zama 'yan mata."
Na zauna saman daddumar da ta shimfida mini ita kuma ta janyo yaran suka hau katifar da take zaune suna jereran gaisheta.

Ta dubi Minal tana cewa " 'Kanwarsu ce wanann ko don na ga hangi kama."
Na ce." Eh mai sunana ba Amina ce muna kiranta da Minal."
Ta ce." Ma sha Allah duka gasunan sun yi wayo sosai wallahi."
Na yi murmushi ina nazartata ta d'an rame gaskiya ba kamar lokacin da suka je gaisuwar Hajiya Maryam ba ramar da ta yi yanzu ta fi muni domin kallo daya na yi mata da na shigo na tabbatar da cewa." depression yana damunta.......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700...0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*155*
Ta ba ni tausayi sosai to ya za a yi ne shiyasa ake fad'in idan kasan farkon ka baka san karshenka ba.

Kuma duk wanda ya shuka alheri shi zai gani kuma idan sharri ma ka shuka to tabbas shi za ka girba da wayo na ba zan manta da irin azabar da matar nan ta gana mini ba.

Na ci wahala ainun a hannunta wankin yaranta ni ce girki da cefane shara da wanke-wanke duk ni ce ba ni da sabulun wanka a gidan balle na wanki haka za ta tura Hadiza gidan kisto da kudi a yi mata ni nawa kan ya yi sama da sati hud'u ban tsefe ba idan zan ari kibiya a wajenta na dinga ra'be-ra'be kenan har sai da Gwaggo ta fahimta.

Wando pant da siket kuwa sai da ya kasance biyu gare ni duk sun yayyage haka nake sanyawa a jikina nan ma gwaggon ta ankara ta sayo mini ita da Yaya Aminu da Sahura sun taimaka mini k'warai a wancan lokacin.

Na yi girki da hannuna ta zo ta raba ta cikawa yaranta kwano ni ta bar mini 'kasan tunkuya duk ranar da ta tauna tsakuwa a shinkafa kuwa ina shan zagi a gidan.

Sai da Ummansu Saminu ta zo gidan na fara samun sau'ki amma zahiri Ummansu Hadiza ta wahalar da rayuwata babu abinda yake bibiyarta sai hakki.

Ta dinga kuka haka kawai tana kallona na yi na yi da ita ta yi shiru ta yi mini bayanin abinda yake damunta da kyar cikin dashewar murya ta furta."Hankalina ya'ki kwanciya Amina kullum Hadiza tana raina da wannan zaman da take a wannan waje gwara su yanke mata hukuncin ta san matsayinta, ni ma hankalina zai fi kwanciya.

Da yawa mutane sai su dinga fad'in na kwantar da hankalina wallahi ba zan iya ba domin ko bacci bana iya yi sai ciwon kai."
Na ce." Ai ha'kuri da tawakalli ya zama dole Umma ki bar wa Allah lamarinsa domin Ubangiji yana so ya jarrabeka ka yi hakuri ki dinga yi mata addu'a idan da rabon za ta fito ta sake wata rayuwar sai ki ga dalilin wani lamari ta fito mun cigaba da rayuwa tare.

Idan kin tsananta ciwo zai iya kama ki, kuma yana da kyau mu sake komawa asibiti tunda kin ce kina fama da ciwon kai."
Ta gyad'a kanta tana fad'in." Shine abinda ya fi damuna yanzu."
Na ce." To shikkenan in sha Allahu da kaina ma zan kai ki asibitin."
Ta ce." Na gode sosai Amina."
Shiru ya d'an ratsa wurin na dubi agogon da yake daure a hannuna sha daya saura na yun'kura da kyar na tashi sai a lokacin ta lura da cikin jikina ta ce." Ashe da sai dai mu ji haihuwa Amina haka ki ka yi nauyi."
Yar dariya na yi kawai dama sai mai kurrula ne zai gane akwai ciki a jikina dalili duk ya bi kirjina daga 'kasa ya sake bud'e ni na yi fadi sosai sai dai yayi mini mugun nauyi a mara sosai.

Ta ce."Allah Ya sauke lafiya." Na amsa da Amin a takaice.

Hanyar fita na kama ina fad'in" Bari na shiga wajan Ummansu Saminu.

" Ta yi shiru ba ta ce komai ba yaran suka biyo bayana na ji tana fad'in." Ba za ku zauna anan ba."
Babu wanda ya waiwayeta suka biyo ni.

Ummansu Saminu na zaune cikin annashuwa har da sanya sabon d'inki ta cokala d'aurin d'ankwali tana tauna cigum cike da nishadi.

Mamaki ya kama ni kamar an fara hidimar bikin ita tun yau ta fara kwalliya kenan.

Na zauna ina nazarinta dama d'akin gabad'aya
Rumfarta makad'e da kafet mai taushi da sabbin labulaye da sabon agogon bango sakamakon na Ummansu Hadiza da ba a sabunta shi da komai ba.

Wala'ala ita ta yi gyaranta ko kuma shi Usainin ya yi mata saboda taron bikin da zai gudana.

Jikina ya yi sanyi sosai wato ita duniyar nan juyawa take yi amma kuma ga dukkanin alamu zaman ha'kuri Ummansu Hadiza take yi a gidan alamu sun nuna Ummansu Saminu itace mai hutawa dalilin yaranta duka maza ne kuma sun tashi suna nema ita kuma Ummansu Hadiza ga yadda rayuwa ta juya mata shiyasa ake so mutum ya shuka alheri domin ba a san inda rayuwa za ta juya ba.

Ban yarda mun yi wata magana da ta shafi abinda ya kawo ni ba sai da na kira Ummansu Hadiza domin kada abin ya yi mata yawa kuma lallai idan Usaini ne ya yi wa mahaifiyarsa wannan gyaran bai had'a da Ummansu Hadiza ba to bai kyauta ba.

Gabad'aya ma gidan zan sanya a yi masa fenti da sabon simitin tsakargida a canza musu kofofi da tagogi dole ne abin ya yi mata yawa ta auri zaman d'aki kunci da damuwar yadda rayuwa ta juya mata ya janyo mata ciwon kai.
Chapter 231 · 0% Book details