← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 247 OF 276

Sashe 247

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan fitarsa Ya Falmata ta kwashe ragowar kaf katon kwalin da suka shirya kayansu a ciki ta watsa atamfofin tana fad'in." Ke ma kina dangi idan mun je gida za a ba su ke da haihuwa wata da iko da kayanki idan haihuwar biyu banza ne ta yi zuciya ta yi."
Sahura ta dinga dariya tana fad'in." Wallahi baiwar Allah nan Hajja tana burgeni suruka ce tagari babu ruwanta da sa ido akan duk abinda yake faruwa ki ga dai uban naman da a ka bata ta dibi kad'an ta bayar da shi.

Hauwa da mamanta sai ka ce mayu ita tsabar rashin yarda ma d'anye ta sanya a ka kai mata gida kamar ita ta haihu."
Anti Yagana ta ce." Abu dai ya wuce alhamdulillahi an tashi lafiya wata matsala dai ba ta faru ba ni na gaji ma da zaman nan wallahi Ya Falmata tunda mun had'a kaya an jima muna yin wanka mu kama hanya."
Na ce." Sai dai gobe tunda ya fita kuma har yanzu bai shigo ba ai ba za ku tafi ba tare da kun yi masa sallama ba."
Ta ce." Bashi muke bin sa da sai mun jira ya dawo Amina."
Na ce." Duk da haka dai anti Yagana a bari ya dawo din ya fi mutunci."
Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba.

Itama Ya Falmata din ba ta tanka ba maganar dai da take ta jaddada mini shine kada na yarda ya auri Nabila domin babu haske a cikin al'amarin.

Yadda ta zafafa sosai abin har mamaki yake ba ni, kishi take taya ni sosai Hauwa ma don dai tana ciki ne muna tare da yaranta babu yadda za a yi da ita.

Ba su tafin ba kuwa sai da gari ya waye tara na safe sun fito lokacin Masa'udu ya kwashe kayansu tsaf ya kai mota su Hajja na d'aki ba su fito ba muka shiga tare muka same su ashe inna Uwani a gidan ta kwana duka muka gaisa cikin mutunci da raha.

Ya Falmata tana fad'in." Bako zai yi halinsa Hajja mun yi shirin tafiya, mun gode sosai Allah Ya kara girma yara kuma Allah Ya raya su."
Ta dinga amsa da "Amin mune da godiya Allah Ya saka da alheri."
Tare da ni su gabad'aya muka yi musu rakiya bakin mota suka shiga Ya Falmata da anti Yagana ita Sahura sai gobe yadda muka yi da ita za su tafi.
****
To sati uku da haihuwa gidan na mu ya daidaita kamar ba a yi wata dabdala ba kowa ya watse an bar ni da yara da masu aiki kamar yadda muke a da.

Hassan da Usaini basa zuwa hannuna sai idan yunwa ta kawo su suna can wurin Baba Tabawa da taburni da daddare ne kawai nake kwana tare da su, shima maigidan muddin ranar girkina ne sai dai ya sakko kasa ya same ni a d'akina.

A tsukin suka tafi saudiya umara shi da Khalil kamar yadda ya fadi ranar dana haihu.

Sati biyu suka dawo a cikin satin kuma ya sabunta mini komai na gidan tun daga kasa har zuwa sama komai sabo da sabbin kayan kicin abin dai kamar wata sabuwar amarya.

Hatta da kayan da yara suke sanyawa sai da aka fitar da su aka yi musu sabbi Taburni da Mairo sune masu iyali a kauye Kuma sune masu wahala da yarab na ce su kwashe suka kuwa cika manyan bacco suka ajiye da jiran lokacin ziyara tunda sun ce sai sallah za su ganin gida yanzu muna daf da shiga wataran Ramadan kuma a watan dai za su tafi umara in sha Allahu rabbi.

Tun bayan watsewar kowa Hauwa ma ta d'auke kafarta tun ma dai washe garin ranar da muka yi walima ba ta sake shigowa ba, hakan bai wani dame ni ba dalili nasan dama abin ba d'orarre ba ne.

Na ma yi mamaki sosai da ta iya jurewa a yadda na santa da tayar da fitina har aka gama wannan kacaniyar ba ta ce ga abinda aka yi mata ba.

Shi kuma daga nasa bangaran babu yabo babu fallasa ya ce muna damunsa da maganar Nabila zai fita daga harkar kowacce domin da akwai abubuwan da suke gabansa ba mu isa mu raba masa hankali ba.

Da gasken ne sabgogi sun yi masa yawa domin tunda suka dawo daga umara shi da Khalil bai fiye zama a gida ba.

Ya je Kano kusan sau uku a kasa da sati hud'u.

Ba ma shi da lokaci sosai idan ya dawo da daddare ya ci abinci ya dinga lissafi kenan yaran ba kasafai yake zama da su sosai ba, na yi wankan tsarki tuntuni amma bai lura ba saboda abubuwan da suka sha kansa a tunaninsa har yanzu ina cikin jinin 'biki bai ta'ba nema na ba sai dai 'yan ta'be-ta'be kafin a kwanta.

Order na yi daga kano wurin GARKUWAR MATA 08089965176 package irin na masu jego na ce ta had'a mini na aminta kuma na gazgata sahihancin maganinta shiyasa ba ni shakka da shakku a ko'ina zan yi mata TALLAH da k'umaji da karsashi.

Ta kuwa yi mini delivery har garin Abuja na sanya Masa'udu ya je ya kar'bo komai cikin girma da arziki nannad'e da salatif.

Na durfafi gyara jikina domin bahaushe ya ce wai idan kana da kyau ka kara da wanka.

Yau da yake girkina ne baya gari ya tafi kano Amma ya ce lallai a gida zai kwana.

Na yi tatul ta ko'ina kuma buk'ata na ke ji.

Sosai yau kwana hamsin da shida da haihuwa na dawo Amina sosai
Ado da kwalliya na yi mai kayatarwa don an sake yi mini wani sabon lallen ma baya wanda aka yi mini na bikin suna ba.

Sai yanzu na sake gazgata alfanun raba gida hankalina a kwance yake sosai a yanzu Hauwa na can gidanta ni ma ina nawa duk ta ta zame mini jiki amma wallahi watarana har mancewa nake yi da ita mussaman yanzu da muka sake yaiwata a gidan ko ta ina babu kad'aici akwai kuma fahimta mai kyau da masu aikina muna girmama juna
Na kudi ne littafin nan kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
mutuntawa tabbas da maza da yawa za su gane jin dadin da kwanciyar hankalin da yake tattare da rabawa iyali mazauni da dayawa ba a sa samu rikici da rabuwar kai ba.

Khalil ne yakan d'an je gidan jefi-jefi wataran kuma idan babu makaranta ya ja 'yan uwan su je su d'an zauna mata babu kuma wata matsala da ta ta'ba faruwa dalilin zuwansu nasu domin yadda na fahimta so take itama ta ja su a jiki ta samu irin soyayyar da suke mini har sultan yanzu ya daina tsoronta da shi suke zuwa idan za su tafi hakan yana yi mini dadi sosai yaro ne Khalil amma mara mantuwa shiyasa ake cewa idan za ka yi sharri ko wani abu na rashin kyautawa kada ka yi a gaban yaro dalili baya mance abu.

Yanzu da ya fara girma ya gane cewa mamansa itace matsalar gidansu gashi a aikace cikin hikima yana ta ko'karin ganin ta gyara ta dawo mutuniyar kirki tunda ba zai mance abubuwan da suka dinga faruwa ba.

A bakin yaran nake jin Ladidi suna yawan kiran sunanta sai da na tambayi yaron wacece ita yake gaya mini mai aiki ce da ta zo daga bauchi sunanta Ladidi take wasa da su tare da yi musu tatsuniya ashe kenan an kawo mata mai aiki wata'kila ma ta jima domin lokacin da ta jibgi danyen naman nan na yi ta mamakin yadda za ta yi dashi Ashe tana da mai yi mata hidima ko tare suka zo da inna Uwani Allah ne ya sani.

Sai dare ya dawo bayan ya yi wanka ya ci abinci ya bukaci ganin yara har saman suka same shi ya kuwa kasance da su na tsayin mintina talatin ana ta gaisuwa masu hawa jikinsa na yi masu tsokanarsa na yi Usaina ce me jan gemunsa tana fad'in ya yi fari furfurar ce bata iya fadi ba har tana nuna masa sabon kitson hannu da Taburni ta yi musu tana cewa." Ka ga nawa ba'ki naka kuwa fari baba ka goge ya dawo irin nawa." Tana ta jan gemun yana dariya kallonsu kawai nake yi har suka gama ya ce su sauka k'asa zai huta da suka fita d'akin ya rage mu biyu ya ce." Na ga lokacin da zan huta Amina, wallahi jikina ciwo yake mini ga shekaru ga wahalhalun rayuwa."
A takaice na ce." Sai sai shekarun amma kai yanzu har wata wahala kake Sha?"
Ya d'an harareni yana fad'in." A a ba na sha a kwance nake samun kudin tunda mafia nake yi."
Dariya maganarsa ta ba ni na yi a takaice ban ce komai ba sai kallonsa da nake yi masa
Ya yi kwafa yana cewa." Yarinyar nan Nabila nema take yi ta matsanta mini fa wai zuwa ta yi can wajan Hajiya Ayya mahaifiyar Alhaji Ahmadu akan na aureta."
Ban ce komai ba sai Ido mu je dai zuwa.
Chapter 247 · 0% Book details