Sashe 203
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amma ni da ta yi shawara da ni zan ce mata ta yi zamanta anan ta cigaba da sana'arta kamar zai fi alheri."
Ta ce." To ta dai ce shekara uku kacal za ta yi ta dawo sai dai mu yi mata fatan alheri kawai."
Na ce." Ubangiji Allah Ya taimake mu bakidaya anti Yagana ke kuma me ki ke sayarwa?" Na tambayeta cikin sigar tsokana."
Ta ce." Babu komai hankalinta a kwance har sai da na yi dariya na furta.'' Babansu Fadila ne ya tsaya miki anti Yagana shiyasa kike wanke goma ki tsoma biyar ba ki da matsala."
Ta ja tsaki tana fad'in." Amina ai sai mutum ma ya rasa wace sana'ar zai yi wallahi maza daga waje duk sun k'wace mana abin yi."
Na kudi ne littafin don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Na ce." Anti Yagana ba ni so ki kasance daya daga cikin matan nan da barmani coge take yi wa wa'ka (Sakarai baki da wayo) na yi dariya ina fad'in." Ki yi nazarin abinda za ki sayar na baki jari don Allah."
A tak'aice ta furta."Aikuwa na gode sosai ai ba ki ga yadda Fadila take cinikin ruwan sanyi ba cikin nan da take d'auke da shi ya hanata fara zuwa koyan d'inki don har mijin nata ya sayo mata form na makarantar."
Na ce." Ai ni ya burge ni sosai da ya ke so ta yi Sana'a dalili kuwa rayuwa juyawa take yi ga kuma yadda duniyar ta zama komai ya yi tsada tunda karamin ma'aikaci ne za su taimake ki kan su anan gaba"
Ta ce." K'warai kuwa hakane ni ma in sha Allahu zan yi nazarin abinda zan sayar idan na yanke shawara zan sanar da ke."
Da jin dad'i sosai na furta.'' Yawwa anti Yaganata ko ke fa" Dariya ta yi kawai muka yi sallama cike da barkwanci da k'aunar juna irin ta jini.
Wayar mu da anti Yagana ta kara mini karsashi da kuzari na tashi na je na dauro alwalar la'asar ganin uku da rabi har da minti biyar jim kad'an bayan idar da sallata Dr Sailuba ta kira ni ta iso tana falo na ce mata ta shigo d'aki ta same ni mun saba sosai da ita tuntuni.
Ta shigo kamar yadda na buk'ata ta zauna can kujerar dake gefe a d'akin.
Na tashi na same ta muka gaisa cikin kulawa na ji dad'i kuwa da ta zo da abin gwajin bf ta yi mini jinina normal bayan ta gama kai tsaye ta tambaye ni ina da ciki na ce mata eh.
Cikin raina ina tunanin fa ranar da Hajiya Maryam ta rasu na same shi tunda mun yi kwanciyar aure a daran ranar idan kuwa hasashena daidai ne bai fi kwana arba'in ba tunda itama gobe za ta cika arba'in da rasuwa.
Bayan magriba ta aiko mana da magungu
ana kamar yadda ta fad'a mini kafin ta tafi muka sake yin waya tana yi mini bayanin yadda zan yi amfani da nawa maganin da kuma bayanin na Sultan tunda shi ma ta duba shi kafin ta tafi zazza'bin hak'ori ne yake damunsa magungu
a ta had'a masa masu kyau tana fad'in daga zarar an bashi maganin zazzabin zai sauka don haka muka yin sallama a wayar na tashi na fita da ledar maganin nasa hannuna.
Suna kicin ba su fito ba tunda na duba d'akin babu kowa har ita Nusaiban na same a kacame suna ta aikin kwa'ba fulawa har da Mairo dama yaran gabad'aya ganin Nusaiba ya sanyasu zuwa wajenta tunda akwai sabo kuma yadda take hira da yaran ya tabbatar mini da cewa ko a can baya da suke tare da mahaifiyarta bata tsangwame su ba hakan ya nuna sun yi sabo domin da babu kulawa da ja a jiki nasan babu yadda za a yi su je wajenta za su guje ta ne da kallon rashin sani kamar yadda suke yi wa Hauwa.
Da yake kicin ne mai girma mai d'auke da na'urorin sarrafe-sarrafe hakan bai sanya sun takura ba.
Baba Tabawa da Taburni suna ta aikin towon dare kamar yadda na umarta.
Mairo da Nusaiba suna kwa'be-kwaben fulawa.
Na saki fuskata sosai Ina kallonsu suna cikin nishadi lallai d'an adam rahama ne a ko'ina sai na rasa ma gaisuwar wanda zan amsa manyan na yi haka zalika ma yaran na yi na bi duka na amsa ina fad'in." Nusaiba wannan funkason zai yi dad'i har miyau na ya tsinke."
Ta kuwa sanya dariya tana fad'in." Kai anti."
Na dubi Baba Tabawa ina fad'in.
" Ga maganin Sultan Dr Sailuba ta aiko da shi a bashi abincinsa sai ba shi yanzu."
Rufe bakina ke wuya Hauwa ta shigo kicin din ta fara bin ko'ina da kallo babu wanda ya yi yun'kurin gaisheta Baba Tabawa ta zo zata kar'bi maganin tana fad'in." Jikin nasa da zafi har yanzu." Ta juya da sauri tana fad'in ko dai bari na fara dama masa kamun nasa.
Da yake kamu ake yi masa na nikakkiyar gyad'a ya fi son sa akan duk sauran abubuwan da ake bashi kuma shine yake kara masa kuzari da lafiya babu kuma rama a tare da shi.
Na ji maganarta a cushe tana fad'in." Ba shi da lafiya ne?''
Ba tare da na dube ta ba na ce." Eh.'' A takaice na mi'kawa Baba Tabawa ledar magungan kafin ta kar'ba sai ta yi gaggawar warce ledar daga hannuna.
Duka muka bi ta da kallo da mamaki.
Ta fito da magungu
an tana duba su.
Na zura mata ido da tsananin takaicinta kamar na mangareta haka nake ji a raina wai ita likita amma mara tunani da kangado .
Ta gama duba magungu
an tsaf ta miko mini na kar'ba ina girgiza kaina duk abinda zan yi a yanzu wallahi ba don ita nake yi ba.
Baba Tabawa ta kar'bi maganin daga hannuna.
Hauwan ta dube ta tana fad'in." Ba ni shi na duba shi."
Sai ta dan dube ni a tsorace wata'kila tana fargabar ta bata shi ya bude ido ya ga fuskarta tunda ta gaya mini ya ta'ba shid'ewa a kwanakin baya.
Na daga mata kai alamar ta kwanto shi daga bayanta ta bata shi kamar yadda ta buk'ata.
Na ji tsakinta tana fad'in." Sai kin nemi izininta za ki ba ni d'ana na gani Baba Tabawa ko kin manta ni ce na haife shi ne ikon Allah sai kallo ni Hauwa"
Babu wanda ya tanka mata Baba Tabawa ta kwanto yaron daga baya wanda ya yi daidai da lokacin da ya bude ido ya fara kusurkusur sai kuma ya sa kuka.
Nasa hannuna a wuyansa da zafi.
Itama ta mika hannunta domin kar'barsa kukansa ya tsananta kuwa ta rike shi yana fizga irin ta yara yana mika hannu domin komawa wajan Baba Tabawa.
Kukan da yake yi ya tsorata ni sosai ita kuma ta'ki ba bawa Baban shi gashi dai ta fahimci so yake ya koma hannunta.
'Dif!! kamar an yi ruwa an d'auke ya yi shiru jikinsa ya shika lakaf!
Idanunsa suka kakkafe.
Suma ya yi....
Ta gigice ainun da sai ta fashe da kuka tana kallonmu na yi gaggawar kar'bar shi daga hannunta muka yi tiri-tiri a kicin din har muna bangazar juna ni da ita Baba Tabawa kuwa tuni ta fara hawaye tana fad'in.'' Suma ya yi.
Kafin mu yi wani yun'kurin Taburni ta nufi friji ruwa mai sanyi gaske ta d'auko ta gumtsa a bakinta ta fesa masa da karfin a gaske a fuskarsa ya saki nishi!
Numfashinsa ya fara hawa da sauka.
Ya motsa kafafunsa.
Muka fita daga kicin din a gaggauce ni da su gabad'aya rasa inda zan nufa na yi da yaron a hannuna d'akinsu Baba Tabawa na nufa hankalina a tashe yaron nan ya mutu ko ya samu wata matsalar mun shiga uku a gidan nan gabad'aya.....
Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...
BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*137*
"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! wannan kalmar ita na dinga nanatawa a cikin raina ina zaune gefan gadon da Baba Tabawa take kwanciya da yaron hannuna.
Duka sun yi cirko-cirko a kaina yayin da ita Hauwan take bakin kofar d'akin a tsaye ta gagara shigowa amma kallo daya za ka yi mata ka tabbatar da cewa a cikin tashin hankali take.
Numfashinsa yana ta hawa da sauka kafin a hankali ya bud'e idonsa yana juya kansa ya ga Baba Tabawa sai ya fara mik'a mata hannu alamar ta d'auke shi.
Wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke cikin raina ina tasbihi da godiyar Allah.
Ta kar'be shi a gaggauce ta sanya shi a kafadarta tana dan jijjigashi sai lokacin hankalin kowa ya kwanta ganin yadda yanayin yaron ya daidaita na juya babu Hauwa babu dalilinta dama kuma ba ta iya shigowa ba a bakin kofar d'akin ta tsaya.
Minal ta je tana jan zanin baba Tabawa tana fad'in." Mutawa ya yi Sultan din shikkenan ya mutu ko?"
Da sauri na janyota ina girgiza mata kaina alamar a a gabad'aya yaran duk sun yi tsuru-tsuru ganin yadda muka ki'dime don shi Khalil har da yin kuka kuma bai biyo mu d'akin ba.
Na ce Baba Tabawa ta zauna dashi a d'akin ta bashi abincinsa gabad'aya muka fita.
Smma ko da na koma dakina kasa zama na yi minti goma a tsakani na sake fitowa Hauwa na samu a tsaye a jikin kujera ita kad'ai don duk sun koma kicin din domin cigaba da ayyukan da suke yi.
Muka dubi juna na wuce ta ban ce komai ba na ji ta kira sunana cikin damuwa na juya amma ban amsa ba ta zo ta tsaya daf da ni tana fad'in" Don Allah Amina kada ki gayawa maigidan ina neman wannan alfarma a wajenki."
Na zura mata ido cikin nazartar maganarta ashe mara kunyar 'karya ce.
Na ce." To akan me zan gaya masa Hauwa da dai Allah Ya d'auki rayuwarsa ne wannan zama dole ya san dalili yanzu kam tunda Allah Ya sa ya dawo hayyacinsa sai ayi ko'karin kiyaye gaba."
Ta gyad'a kanta tana fad'in na gode.