← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 229 OF 276

Sashe 229

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba ni buk'atar Hauwa gabad'aya a rayuwata bana tsammanin zan iya sake sakin jikina da ita domin bata daga cikin mutanan da Ubangiji ya ce idan sun tuba ku yafe musu Hauwa bana jin za ta yi taubatun nusu'a akan zamantakewa ta tsakani da Allah."
Ya dube ni yana fad'in." Hajja ta ce ta zo cikinmu gabad'aya tunda yaran sun dage anan wajanki za su kwana can kuma ita kadai za ta kasance, amma ni ma na fi buk'atar su zauna a can gidan Hajja saboda ba ni son fitina fa na gaji idan ba so kuke na mutu ba."
Na ce." Ai ita kanta Hajjan ta san gidan ya yi mana kad'an ni wallahi tallahi na gaji da wannan rashin adalci da son zuciya ba ni son had'a numfashina da matar nan domin zahirin k'iyayya ta nuna mini na bar mata can gidan na zo nan na zauna domin zuciyata ta samu nutsuwa ta sake biyo ni ko sai ta yi wa rayuwata illah tukkuna za a gane abinda nake nufi."
Ya 'bata ransa ainun yana duba tsabar idona ya ce." Rashin kunyar ta tashi daga kaina Amina ta yi tsalle ta tafi kan mahaifiyata kenan ko, gidan ki ko nawa da za ki yi mini iko da abinda nake da iko da shi, ki gaya mini gidanki ne ko nawa na ce?"
Ya fad'a cikin 'karaji har yana dukan hannun kujerar da yake zaune.

Duk da na tsorata daga ganin yadda ya burkice na dake sosai ban sarayar da mutuncina ba na ce." Gidanka ne ai dama ban ce gidana ba ne amma dai ni ce yanzu a cikinsa kuma na ce ba ni buk'atar zama da wata a cikinsa.

Idan lallai sai ka zauna dani a irin hukuncin da na yankewa kaina na rayu ni kadai da yarana a waje daya babu wata bagidajiya da za ta d'aga mini hankali ko ta nemi halakar da rayuwata.

Kuma kada ka sake ka yi mini k'azafi akan maganar da na fad'a domin ni ban ga ta inda na kausasa harshe akan mahaifiyarka ba."
Ya sake hasalowa yana fad'in." A ciki nake dake domin kin jima kina yi mini rashin kunya kala-kala saboda kin samu dama akaina ko kin lura ina sonki da yawa za ki samu damar taka ni yadda ranki yake so kin zo geji muddin ki ka ce za ki sanyo mahaifiyata cikin wannan rashin mutuncin naki wallahi ranki idan ya yi dubu sai ya 'baci."
Na sake aro jarumuta da jajurcewa domin dai duk wannan hargitsin da yake yi bai karya mini lagona ba ko na tsorata na furta ." Kada fa ka yi mini sharri akan abinda ban yi ba babu cin mutunci balle rashin kunyar da kake magana a tsakanina da Hajja wannan alkawari ne na daukarwa kaina."
Ya ce." Idan ba rashin kunya da rashin arziki ba mai yasa za ta bata da umarni ki ce ba daidai ba ne har kina fad'in ita kanta wannan ai wulakanci ne da nuna mutum bai isa ba."
Na girgiza kaina cikin ko'karin nuna masa ba haka nake nufi ba na ce." Idan wannan maganar dana furta akan Hajja ta hasala maka zuciya Allah Ya baka ha'kuri amma zan fita yanzu tunda da sauran dare a gidanmu zan kwana nan gidan Hauwa ne da yaranta kamar yadda wancen ma ya zama nata.

Na yun'kura na tashi a hankali yaran dake cikina suna naushin marata duk da ciwon da nake ji na yi azamar kama hanyar fita.

Ya cimma ni dalili da kyar nake iya cire 'kafa.

Ya tari gabana da b'acin rai a fuskarsa ya furta." Ba za ki bari mu huta ba ko Amina, ba ki duba nauyin da ki ka yi, kin ki ki bari mu fahimci juna har mu raini yaran dake cikinki kin dusashe mini farinciki da annashuwata kina nema ki dasa mini b'akinciki me na yi miki ne?"
Na daga kaina na dube shi a hankali na ce." Ka bar ni na huta ni ma?"
Ya yi shiru bai ce komai ba da akwai alamar sasaauci a fuskarsa.

Ya rike hannuna daya na fizge tare da ratse shi zan wuce ya san janyo ni da sauri tare da sanya ni a jikinsa.

Na sake cirewa rik'on karfi ya yi wa hannuna.

Yana jana ina turjewa so yake mu je mu zauna a gefan gado.

Na ce." Ai babu buk'atar wani zama na samun maslaha da daidaito a tsakaninmu tunda har yanzu baka fi karfin gidanka ba.

Zaman sulhu da samun mafita ba za a yi shi da ni ba a yanzu zaman 'yanci zan yi da kare kaina."
Ya ce." Na gaya miki tuntuni Hauwa ta gyara ta daina duk wasu abubuwa na rashin kyautawa kada ki manta da irin yadda na fifitaki a kanta na nuna miki kulawa da k'auna a kanta ki ka fitar da hannu ki ka tsinka mata mari a gabana.

Na hana ta d'auka mataki ta kuma hanu.

Wannan bai isheki ba Amina."
Na ce." Ai baka burge ni ba daka sani ka bari ta rama marinta ko kai ka rama mata tunda ka ji mata haushi.

Ka daure mata gindi tunda baka musanta abinda ta fad'a ba a kaina kawai ka mayar da abin wasa.

Mataki ma ban gama d'auka a kanta ba wallahi muddin ba ta fita daga rayuwata ba."
Ya rungumo kafada jikinsa yana dan rawa har yana gyara mini sar'kar wuyana ya ce." Ni ban d'auki maganganunta da muhimmanci ba saboda nasan wacece ke, nasan ta fadi haka ne domin ta 'bata miki rai da kishi irin naku na mata me yasa maganarta za ta dame ni tunda na fi kowa sanin da baiwar da Allah ya yi mini na rabauta dake giwar mata shige mu zauna mu yi magana wadda za ta kawo mana sasanci.......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700...VIA 0542382124....

BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*154*
Ganin yana neman wuce makad'i da rawa ya sanya na tankwa'be hannunsa ya sake mayarwa tare da tarairayoni jikinsa sosai na yi 'kokari wajan 'kin barin abinda yake yi mini ya yi tasiri a tare da ni muka zauna gefan gado a tare yana ta sauke wata irin ajiyar zuciya wadda na kasa tantance ko ta mecece.

Raina a b'ace na zura masa ido domin sauraran abinda zai fad'a abinda na sake kud'irewa a raina shine ko sama da 'kasa za ta had'e ba zan zauna da Hauwa ba tunda ba tare a ka hallice mu ba.

A wannan karon na shirya sosai koda Hajja za ta sanya bakinta ba ni tsammanin za ta sake samun wannan alfarmar.

Sai da ya daidaita kansa sosai ya furta." Za mu yi kwana biyu da Hauwa anan zuwa jibi zamu tafi tare da ita da yaran gabad'aya ba dai akan maganar raba gida kike magana." Ya fad'a yana kallona.

Na gyad'a kaina ba tare da na ce komai ba.

Ya sake sauke ajiyar zuciya yana ce wa." Za a yi yadda ki ke so amma ya zama dole kema ki bi umarnina tunda kin san bai zai yiwu ki zauna anan ba mu muna can
kuma duk wasu d'abiu da ki ke yi a yanzu ki ajiye a gefe ba zai yuwu ki dinga juya ni ba Amina kin san dai ba ki isa ki kafa mini doka na bi ba ko?"
Ta'be bakina na yi tare da juyar da kaina gefe wai ban isa na kafa doka ya bi ba.

Ita din yake bi ai a yanzu na tu'ke tunda bai san alheri ba.

Dole ne aka ce na zauna da wata Allah Ya gama hore masa ta ko'ina idan ya'ki raba ma mazauni bai shirya kashe rikici ba.

Ya juyo da fuskata yana fad'in." Ki kalle ni mu yi magana domin fahimtar juna nake so mu yi ni dake saboda na gaji da wannan halin da ki ke yi mini ina ce akan an bani auran wannan yarinyar ne Hajara ki ka canza gabad'aya ni fa ba yaro ba ne giwa na baki shekaru sama da goma sha biyar duk yadda ki ka kai ga gogewa na fi ki kuma bai wai ina tsoronki ba ne."
Na dube shi sosai ina cewa." Ni dama na ce ka ji tsorona ne?

Wallahi ka ji tsoron Allah a cikin dukkanin lamarinka ka dinga gaskiya yanzu ba ka ji kunyar duban idona ka dinga fad'a mini irin haka ba me yasa ka ke da mance alheri ."
Ya ce." Ni kin d'auke ni mak'aryaci kenan."
Can k'asa na ce." Iyi."
Ya sake sanya hannunsa ya juyo da fuskata yana ta'ba le'bena kafin ya furta." Ni ki ke yi wa Allah Ya isa Amina."
Na cire hannunsa ganin kamar yana so ya shagaltar da ni, na ce." Don Allah ni ka rabu da ni babu fa wani kalami da za ka yi mini na ji dad'i tunda ka rasa Hajara sai ka nemi wata ba yanzu na ji kana waya da abokinka ba ya baka kanwar amaryarsa sai ku yi anko ina ruwana."
Ya girgiza kansa yana cewa." Ko zan yi aure anan gaba sai da amincewarki ke za ki duba mini wadda ta dace."
Na kalle shi a sakarce wai shi dole sai ya yaudareni da kalaman bakinsa.

Na ce." Ya ake ciki ne za ka d'auki Hauwa ka mayar da ita can gidan Hajja ne domin fa hakan shine samun nutsuwarmu da ni da kai da ita gabad'aya."
Ya yi d'an shiru kafin ya matso ni sosai yana fad'in." Dambatta fa aka ce Amina da tafiya sosai ki bar ta ta kwana na ce miki."
Ya fad'a yana d'ora fuskarsa tsakanin wuyana.

Gabad'aya ya rikice kuma na gane abinda yake so.

Na cire jikina ina fad'in." Shikkenan ta kwana daya zan mata wannan alfarmar amma wallahi daga wannan kwanan ba za ta sake yi mini wani ba."
Can k'asa ya ce." Na ji abinda ki ka ce."
Ya sanya hannuwansa ya kewaye 'kuguna jikinsa na rawa.

Tsaki na ja wanda ban san lokacin da ya fito ba.

Ya dago yana kallona idonsa ya canza gabad'aya ya ce." Kin san na tsani wannan dabi'ar ko.
Chapter 229 · 0% Book details