← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 240 OF 276

Sashe 240

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na daure zuciyata ina fad'in." Hauwa aka ce shimfidar fuska tafi ta tabarma tunda na zauna ban ga kin yi mini duban mutunci ba to me zai sanya ni shiga sabgarki, magana akan katse mini waya kin san dai babu yaro a cikinmu ko, menene amfanin abinda ki ka yi, ko ni ina hana shi amsa wayarki ne?"
Ya daga mini hannu yana fad'in." Na ce ya isa haka ko, kada wadda na sake jin ta yi magana."
Ban sake cewa komai ba naja bakina na yi shiru itama ta yi shiru cikin kunyar abinda ta aikata tunda ta fahimci ni dashi duka mun gane ita ta katse mini waya..

Na yun'kura na tashi ina fad'in." Za mu tafi Baba Allah Ya kara sau'ki." Yaran suka tashi gabad'aya Khalil ya d'auki Sultan suka yi gaba k'ananun kuma suka tsaya ni har muka gama sallama da shi, na dube ta babu yabo babu fallasa na ce." Allah Ya ba mu alheri Hauwa."
Ta amsa kanta a kasa domin ta kasa yarda ta dago ta kalle ni.

Biyo bayanmu ya yi wai sai ya rakamu gida muka kuwa jero muna tafiya tare har bakin gate din gidana har da shi muka shiga ciki ya tsaya yana magana da masu gadi.

Amma bai biyo mu ciki ba anan dai muka bar shi muka shige ciki ni da yaran gabad'aya.

Washe gari kuwa gari yana yin haske na kira shi bugun farko ya daga na ji muryarsa ta fara bud'ewa ba kamar jiya ba muka gaisa yana gaya mini ya warware tarin ma da yake yi ya sassauta masa sosai.

Ita ya ba ni wai mu gaisa duk a kokarinsa na ganin lallai sai mun samu daidaito ban yi jayayya ba na ce to na ji maganarta a dan sake tana fad'in." Ina kwana ya yaran?"
Na amsa da lafiya lou muke suna can suna shirin makaranta." Ta furta." Allah Ya yi musu albarka."
Na amsa da Amin a tak'aice."
Daga haka ba ta sake cewa komai ba ta bashi wayarsa.

Muka dan yi magana kad'an ya kashe tunda a ranar zai dawo gidana.
****
Sati biyu da faruwar hakan.

Kawai na ga kiranta na yi mamaki sosai yaushe rabon da mu yi waya ta arziki da Hauwa tun lokacin da ta ajiye Sultan ta tafi garinsu.

Haka kawai sai na tsinci kaina cikin fad'uwar gaba domin kuwa zahiri zuciyata ta kasa aminta da ita tun bayan abubuwan da suka shud'e ba ni tunanin zan sake sakin jikina da ita tunda ta gama fito da aninhin abinda yake cikin ranta game da ni.

Na daga cike da tarin zullumi muka gaisa ta yi shiru ba ta ce komai ba na ce." Ina fatan lafiya ko Khalil din za a turo miki ne?." Da yake wasu lukutan takan turo mai yi mata wanki da guga ya kira Khalil ban san sai dalilin da ya sanya take kiransa ba wannan tsakanin d'a da mahaifi ne shima yaron yanzu yana sakewa da ita ba kamar da ba.

Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce." Amina tun ranar da ku ka zo duba maigidan hankalina ya kasa kwanciya g
anin Nabila ba ki tunanin akwai wata dangantaka ta soyayya a tsakaninsu kuwa? ko ba ki ji lokacin da yake tambayarta ta dawo ba, hakan na nufin suna da wata ala'ka tunda har yana da masaniyar shige da ficen da take yi kan harkokinta."
Na yi kasa'ke da waya a kunne ina sauraranta har ta kammala maganarta.

Zuciyata kwata-kwata bata ta'ba yi mini wannan tunanin ba a ganina shi kuwa me zai yi da Nabila duk nagartattun matan da suke wannan duniya.

Kai gaskiya ba na tunanin zai yi soyayya da ita ko ya yi zawarcinta.

Ta ce." Kin yi shiru ba ki ce komai ba, kin ga dacewar ko aure zai kara ya yi da ita.

Bayan bada'kalar da ta faru da yayarta."
Na furta." Ki daina wannan maganar don Allah Hauwa, ba ni tunanin haka gaskiya Nabila dai kamar yadda ya gaya mini tana zaune ne domin ta zama garkuwa ga yaran 'yar uwarta, cikinsu babu wanda ya ta'ba kawo korafi a kanta hakan ya nuna suna buk'atar zamanta a tare da su.

Maganar kuma mijinki yana zawarcinta ai shi ba mahaukaci ba ne a zahiri da suffa Nabila ba macen da ta kamace shi bace balle ga abubuwan da suka faru a baya.

Dole za su gaisa watarana kuma suna da lambar juna hakan kuma ba zai sanya mu ce soyayya suke yi ba."
Ta ce." Jikina ne yake ba ni akwai matsala Amina wallahi ko shi baya sonta to ita tana zawarcinsa ai akace idan kaga kare yana shanshana takalmi d'auka zai yi.

Sun gaji asiri fa wallahi kada ta juyar masa da tunani mu rasa gane kansa kamar yadda 'yar uwarta ta yi.''
Na ce." Ki daina tunanin haka don Allah." Abinda na iya ce mata kenan domin ni lokacin ma wani matsanancin ciwon kwankwanso ne ya ri'ke ni.

Na ja kafafu na zauna gefan gado ina jin ta sama-sama a haka muka yi sallama.

Tunda na ji ciwon ya tsananta sosai na tabbatar da cewa haihuwa ce.

Wannan karon kuma abin ya canza mini kenan ba ni haihuwa tara sai na goma ya kama amma watannan kwanansa goma sha bakwai Allah Ya kawo mini ita.

Na tashi na fito da duk abinda ya kamata mussaman kayan baby ina da su akwati guda manyan set na kayan sanyi da towels Na kira
Dr Sailuba lokacin da sauran k'warina bayan ita ko shi ban gayawa ba balle masu aikin yara kuma duka suna skull minti talatin ta iso lokacin ciwon ya sake k'arfi da kayan aikinta ta taho ta gyara wajen tare da shimfid'a mini wata leda babba ta yi mini shimfid'a a kai na kwanta ta duba ni.

Da saura haka na cigaba da fafatawa sai da na k'ara minti talatin da zuwanta tukkuna Allah Ya kawo ta da gaggawa babu jinkiri na farkon
yana fitowa d'an uwansa ya biyo shi jim kad'an mahaifarsu ta biyo baya.

Ina kiran sunan Allah itama tana yi bakinta ya k'i rufuwa.

Da yake gwanace ta yi komai cikin k'warewa kowanne ta nad'e shi cikin towol fadi take kin iya haihuwa wallahi dubi yara 'kosassu na jima ban ga biyu masu wannan girman ba alhamdulillahi."
Ta shiga toilet dina ta had'a mini ruwan d'umi lokacin na tashi da kaina don ba ni jin komai na canza zani na sanya audiga na kuma tafi da wata toilet din.

Ina fitowa na tarar ta tattare kayan dana haihu a kai babu abinda ya 'baci a d'akin kamar ma ba a yi wata sabga ta jini ba.

Na fito da kayana da kaina na sanya da kanta ta wanke yaran suna ta kusur-kusur kuka wannan idan ya dire sai wannan ya d'auka.

Muka fara jin bugu muryar Baba Tabawa tana kiran sunana.

Hajiya Amina.

Taburni tana fad'in." Haihuwa ta yi wallahi tallahi ga kukan jariri nan.

Na tashi ina murmushi a nutse na je na bud'e musu d'akin suka shigo gabad'aya su uku har da Mairo.

Dr dai sai dariya take yi musu tana aikinta.

Baba Tabawa fadi take yi." Ba ku kyauta mana ba amma."
Gabad'aya bakinsu ya'ki rufuwa.

Mairo tana dariya take ce wa." Shikkenan biyu sun samu 'yan uwa Allah mun gode maka, Ubangiji Allah Ya yara mana."
Taburni ta d'an zauna gefena tana fad'in." Sannu Ubangiji Allah Ya kara lafiya Hajiya Allah Ya hore miki arziki domin wannan baiwa ce daga wurin Ubangiji Allah Ya inganta lafiya."
Na amsa da Amin suma Amin."
Baba Tabawa ta kwashi kayan da suka 'baci ta fita da su.

Ta burni ta bi bayanta da sauri.

Ita kuma Mairo muna tare tana zubar da ruwan wankan yaran tare da had'a wani a haka Dr Sailuba ta shiryasu tsaf cikin kayan sanyi kowane da towel dinsa abin dai gwanin burgewa, ni kam tunda na zauna gefan gado nake tasbihi tare da jaddada godiyata ga Allah ganin yadda ya yi mini wannan baiwa ta haihuwa lafiya ba ni jin komai a jikina ina kuma addu'a a gare shi ya sanya ko da an auna yaran a tabbatar mana da sahihancin lafiyarsu.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*160*
Wannan haihuwa ta yi silar wanke zuk'atan bayin Allah da yawa.

Tun daga kan masu gadin gidansa da yaransa na jiki irinsu Sukairaju da masu hidima da kai kawo na gidan muka kasance gabad'aya da su cikin
murna tamkar a daran sallah.

Ita dai Dr Sailuba ta samu tukwicin kujarar umara da mota.

Masu aikin kuwa Baba Tabawa Mairo Taburni kowacce da alk'awarin zuwa umara ta azimi kuma tunda daf muke da shiga watan.

Ya rasa inda zai sanya ransa ya ji dad'i da ya dawo ya same ni da yaran lafiya lau kuma Dr Sailuba tana gaya masa cewa ita dai a yadda take ganin yanayin kuzarin yaran bata tsammanin suna d'auke da wani ciwo mai karya garkuwar jiki mussaman irin wanda muke hasashe amma domin dai a sake tabbatar da lafiyarsu lau ya ce mata za mu je asibitinsu tare da ni dashi wajan Dr Iliyas a bincikesu sosai don mu sake samun nutsuwa da kwanciyar hankali.

Sujudur Shakur ya yi a gabana ya jima kuwa goshinsa a kasa da ya d'ago sai ya kama ni
ya rungume ni tsam-tsam a jikinsa yana ta furta mini kalmar godiya tare da jadadda mini so da k'aunar da bata da abin misali.

Yara suka dawo daga makaranta tsalle suke yi Mama ta haihu abinda suke ta fad'i kenan sun kewayemu da Babansu.

Ya ce su je su cire uniform suka 'ki lallai sai an ba su sun d'auka.

Kowacce ta tan'kwashe k'afa ya dinga bin su d'aya bayan d'aya yana dora musu a cinya.
Chapter 240 · 0% Book details