← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 276

Sashe 3

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda nake daga lokacin kuruciya har kawo yanzu da nake da shekaru sama da talatin a duniya babu wani mahalu'kin da ya ta'ba yi mini maganar banza irin wannan.

Abu na biyu kuma sai mamakin yadda wannan furucin ya fito daga bakin babban mutumin da jama'a da yawa suka bada sheda cewar shi din mutumin arziki.

"Ina so ki zama yarinyata za ki dinga d'ebe mini kewa a duk lokacin da sha'awata ta tashi."
Maganar nake ta maimatawa a zuciyata ina mamakin ya aka yi har ya samu sararin yi mini ita.

Shin ko yana yi mini kallon mutuniyar banza ne, ko kuma dan na zo neman alfarma a wurinsa ne zai fake da haka.

Shiyasa kenan da farko yake tambayata ina da aure ko ba ni dashi.

Menene dalilin da ya sanya ake yi wa zawarawa kallon lalatattu ne?

Me yasa a ka mayar da zunubin zina 'karamin alhaki a wannan zamanin.

Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! wai ni yau wani namiji yake yi wa tayin zina.

Kafin na yi aune na ji maganarsa a kusa da ni.

Na daga kaina Ina kallonsa yana tsaye daf da ni, ya yi mini rumfa hannuwansa zube a cikin aljihunsa.

Table din da yake gabana na buga da karfi na tashi tsaye tare da nuna shi da yatsa.

Sai ya d'an matsa daga kusa da ni fuskarsa d'auke da mamakin yadda yatsana yake daf da karan hancinsa.

Ammafa babu nadama a tattare dashi.

"Idan har sai ka yi fasikanci da ni tukkuna za ka bada umarnin sakin yaranmu to dan girman Allah ka sanya a rataye su, gobe a kawo mana gawarsu.

Ina so ka sani neman mazan banza ba dabi'a'ata ba ce, kuma ba zan yi ba ko duk duniyar nan za ka ba ni.

Wallahi tallahi ka ji kunya, dattijo da kai kana yin wannan harkar ka tozartar da kanka, ka wulakanta nasabarka, sannan kuma ka yi wa Allah butulci wanda ya daga darajarka, ya d'aukaka, ya azurtaka da dukiya wanda nake da tabbacin cewa kai kanka ba kasan iyakarta ba.

Ka cuce ni wallahi sai Allah Ya saka mini." Hawayen da nake dannewa suka zubo nasa hannu na goge.

"Ka matsa ka ba ni hanya na fice domin had'a numfashi dakai zunubi ne.

Yana tsaye turmin danya bai matsa ba, kuma bai ce komai ba.

Naja tsaki mai k'arfi da sauri na bi ta d'aya gefan zan wuce ya yi gaggawar tare mini hanya.

"Idan kin so abinda ya faru ni dake ki yi dogon rubutu kisa a fege d'inki na fece book. bai dame ni ba, idan kuma kin lullube to kamar kin haka rami ne kin binne mutuncinki.

Dan haka ga hanya nan fice mini daga ofis."
Hanci na ja tsabar takaici da bakinciki ban iya mayar masa da raddi ba da sauri na murd'a kofa na fice zuciyata na wani irin ciwo dan wani kutittiran abu ne ya tokare mini a wuya.

Ganin yadda na fito a ki'dime ya sanya Sahura da Yusi tashi tsaye.

Ita tana tambayata abinda ya faru.

Shi kuma ya rike hannuna yana tambayata ina Kamalu.

Da 'kyar na iya furta sunanta." Sahura mu je kawai."
"Sis me ya faru ne?

Ya kuka yi dashi?"
Cikin tsawar da ban san lokacin da na yi ba na ce." Don Allah ki wuce mu tafi na ce miki."
Yusi ya rushe da kuka Yana fad'in." Mama kin ce zaki taho da Yayana to yana ina?"
Yaron kuka yake tu'kuru yana daddagewa, haushi ya sake kama ni.

Bud'ewa kofarsa ya yi daidai da lokacin dana gaura masa mari wanda tunda ya zo duniya ban ta'ba yi masa irinsa ba.

Sai ya gigice! ya kidime domin abin ya zo masa a bazata! ya rasa Ina zai nufa kawai sai ya nufe shi a guje ya rirrike hannuwansa yana rusa kuka na fitar hankali.

Kawar da kaina gefe guda na yi zuciyata in banda za'babbaka babu abinda take yi.

Ya k'araso wurin da muke tsaye ni da Sahura wadda take ta faman yi mini fad'a akan marin yaron da na yi.

Sai da ya iso tukkuna ta ta dan risina tana gaisheshi.

Ya ce." Ashe tare kuke?"
"E, ranka ya dad'e don Allah ka yi hakuri.

"Me kuka yi mini?" Ya fad'a yana kallonta.

Shiru ta yi ba tace komai ba.

"Wannan yaronta ne?"
Ya yi maganar cikin 'bacin rai."
Da sauri ta ce." E, kanin Kamalu ne."
Abin mamaki sai yasa hannu ya d'auki Yusin din yasa a kafadarsa yana d'an jijjigashi kamar yaron goye.

Ya dube ni.

"Idan ba kya so ni ki bar mini shi.

Wannan marin da ki ka galla masa ko ni ki ka yi wa irinsa sai na gigice, ke fa ki ka haifi abinki."
Kallonsa na yi muka had'a ido.

Yanayin yadda yake maganar shine ya tabbatar da ransa ya baci.

Ya nisa kafin ya cigaba da cewa." Ki dubi yadda yake ajiyar zuciya mugunta ce wannan tsagwaronta.

Ko ba haka ba ne?" Ya fad'a yana kallon Sahura.

Da sauri ta ce." Ni ma fad'an da nake yi mata kenan.

Ya juya da yaron a kafad'arsa.

Ofis d'insa ya shige dashi.

Sahura ta kalleni jiki a mace ta ce." Wai don Allah me ya faru ne na ga kin fito a fusace!

Ni fa jikina duk ya mutu wallahi."
Sahura ki bari kawai wannan mutumin bashi da hali wallahi.

Mutumin banza ne.

Cikin zare Ido ta ce." Mutumin banza kamar Yaya?"
"Ki bar maganar kawai Sahura amma Allah sai ya saka mini."
Ina rufe baki suka fito daga ofis din.
kudi da wani irin biscuits ne a hannun Yusi.

Ya dubi Sahura cikin nutsuwa ya furta." In sha Allahu ranar litinin jibi kenan zan sa a kawo muku yaronku har gida, Allah Ya kiyaye faruwar haka anan gaba."
Cikin tsananin farinciki ta fara godiya.

Bai tsaya amsawa ba ya bar wurin.

Ganin haka ya sanya ni ma na kama hanyar fita ina mamakin abinda ya yi babu wanda zai yarda da cewa shine mai neman keta mini haddi.

Ta biyo bayana hannunta ri'ke dana Yusi har tana had'awa da dan gudu domin na yi masu nisa daf nake da fita daga wurin.

Ta iske ni tana dan sauke ajiyar zuciya.

Ban dubeta ba hankalina yana kan tsayar mana da abin hawa.

Zuciyata a takure, gabad'aya sai duniyar ta fice mini daga rai ganin yadda rayuwar ke gararanba da ni.

Har muka shiga adaidaita sahu tana ta tambayata abinda ya faru a tsakanina dashi.

Na yi shiru ban ce mata komai ba.

Sai ta ajiye maganar ta fara kwarzanta kyawun hali da nagartar da ya nuna mana.

Nan ma ban ce mata komai ba, tana gaya mini kudin da ya bawa Yusi har da dala irin ta amarica biyu a ciki bayan naira dubu sha bakwai data lissafa.

Na dubeta tare da furta." Za ki wuce gidanki ne, ko za ki je ku gaisa da su mama.

"Mu je can gidanku Amina akwai maganar da zamu tattauna."
D'auke kaina na yi ban sake magana ba har aka sauke mu, ita ta bada kudin motar muka wuce kamar wasu kurame, yanayi na gabad'aya ya sagar mata da guiwa.

Sai satar kallon fuskata take yi.

Muna shiga gidan Yusi ya ruga d'akin Ummansu Hadiza da gudu yana gaya mata ranar litinin Kamalu zai dawo.

Sai gasu gabad'aya sun fito tsakar gidan da murna a tare dasu.

Sahura ta tsaya tana yi musu bayani.

Ni kuma na bude d'aki na shiga ina jinsu suna ta fad'in." Dama ai an shedi mutumin yana da kirki kwarai da gaske, suna ta gode masa.

Na nemi wuri na zauna, har yanzu kafafuna ba su daina rawa ba.

Duk lokacin dana tuna k'azamar maganar da mutumin nan ya yi mini sai na ji kamar na rushe da kuka.

Na dinga duban jikina, wai ko zan ga alamar karuwanci a tare da ni.

Babu ko daya domin dai shigar mutunci nayi mayafina mai kauri da fadi ya rufe mini kaf ilahirin jikina.

D'inkina kuwa riga da zani ne na atamfa.

Babu wata alama ta 'karanta ko rashin kamun kai a tattare da ni.....
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne 1k akan telegram hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.
Chapter 3 · 0% Book details