Sashe 215
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya juya da sauri ya tura ni na zauna d'abas a saman gado zuciyata na harbawa.
Ban yi tsammanin zan iya yin cacar baki da kishiya ba sai gashi yau tsananin bacin rai da takaici na nema ya sanya ni na hada jikina da Hauwa da zumar kokawa so nake yi kawai na dake ta sosai mu fitar da raini tunda na gama gane irin sharrin da take so ta la'kaba mini.
Ya rike ta da kyau ya hana ta zuwa wajen da nake zagi kuwa sai auno mini shi take tana fad'in sai ta rama marin da na yi mata wallahi."
Ya furta." Yana da kyau ni ma naga hujjar nan Hauwa sai na gazgata maganarki kada ki ga na goyi da bayanta ki sanar da ni abinda ki ka sani a kanta.
Ta yi shiru tana huci! wannan karon hawaye bai fita ba.
Ya riko hannunta suka zauna gefan gado yana tsakiyarmu yana fad'in." Ba ki fa da gaskiya Hajiya akan wannan maganar ni ma ba zan iya barinki ba domin kina ko'karin mini 'bata mini sunan matata, lallai ya zama dole na ga sheda Amina ta ga sheda ko kuma ki bata ha'kuri a ciki biyu za ki yi daya.
Idan na ga shedar abinda ki ka fada a kanta ni ma za gazgata muddin kuwa ki ka gagara kawo sheda dole ki bata ha'kuri ki kuma nemi afuwarta amma ki sani ba zan iya hana ta ta bibiyi hakkinta ba."
D'akin ya d'auki shiru na wani lokaci kafin ya ce." Ya kuke so a yi muku yanzu na kwanta na fad'i na mutu shine burinku ashe da raina zan ga wannan masifar."
Ta ce." Abinda ya fi haka ma za ka ga ni wallahi mutukar ba ka d'auki mataki akan dukan fuskata da ta yi ba idan ba haka ba zan d'auka da kaina duk abinda ya faru a gidan nan ka yi kuka da kan ka."
Ya ce." Babu abinda zai faru sai alheri Hauwa idan kin kashe Amina ko kin yi mata wata illar sai dai na taya ki da addu'a domin kuwa da hannuna zan d'ankawa hukuma ke."
Ta ja hanci ba ta ce komai ba.
Na fara ko'karin tashi domin barin wajen ya rike hannuna tamau ya d'an kalle ni kafin ya sauke ajiyar zuciya ya kamo hannunta yana fad'in." Ku shirya don Allah ba don ni ba kada ku yi gaba ko ku illatar da juna."
Na dube shi da mamaki wai yau shine yake yi wa wani wa'azin kada ya yi gaba.
Abar da ta zame masa d'abiaa.
Na zame hannuna daga cikin nata tunda ya hade mana yatsu ne ya rintse da nasa gabad'aya.
Ya furta." Haka zan kawo yarinyar mutane cikinku da girmanku da shekarunku kuna a matsayin iyayenta masu yi mata gyara ta same ku kuna nuna kiyayyar juna.
Wani bala'in haushinsa ya kama ni.
Hannuna na cire daga cikin nasu na tashi tsaye ya dago yana kallona bai ce komai ba na kama hanyar fita raina a b'ace.
Ita Hauwa shirin take nema domin tunda ta ji ya riketa har yana rarrashinta ta yi lakwas kuma ko lokacin da ya had'a hannunmu waje daya ba ta yi yun'kurin cire nata ba.
Ba ni tsammanin zan sake zama da Hauwa a inuwa daya idan lallai sai na cigaba da zaman aure da shi ya zama tilas ya yi abu daya daga cikin biyun nan ko na koma gidana na kano ko kuma ita ya canza mata gida......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*145*
Wannan shine abinda na yankewa kaina sanadin da ya janyo mana rikici mai tsanani tsakanina da shi domin na rantse masa da Allah ba ni sake zama da Hauwa a gida d'aya kuma wannan dalilin ya sanya shi kai ni 'kara abinda zai biyo bayan haka ba zai yi mana kyau gabad'aya ba.
Bai d'auki ga'barar kaini karar ba da ya yi iya yin sa domin ganin ya tankawari ni na ha'kura ya kasa sai ya kyale ni ya fara neman shiri da Hauwa duk domin na ji haushi da farko ina zaman falon ganin haka ya sanya na daina zama sai da dalili ita kuma mahaukaciyar sai ta d'auka tsoronta nake ji ina gudun ta rama marin da na yi mata.
Daga lokacin da ta fahimci akwai 'yar tsama a tsakaninmu ta dage sosai wajan ganin ta kara juyar masa da tunani wanda gabad'aya rashin nutsuwa da ficewar hayyaci ya ya gigitar masa da rayuwa yana daurewa ne kawai saboda yana so ya nuna mini ba ni kad'ai ba ce matarsa a banza domin duk abinda suke yi shi da ita bai dame ni ba abinda da dai na yanke a cikin raina yana nan ban janye ba akwai wa'adin da d'iba muddin bai yanke shawara ba zan fita na bar gidan.
rashin sakewa da walwala ta ya assasawa yaran da masu aikin damuwa da farko su Baba Tabawa sun d'auka ba ni da lafiya suka dinga shigowa daya bayan d'aya suna duba ni.
Amma da suka fahimci akwai damuwa sai duka jikinsu ya yi sanyi mussaman da suka lura da yadda Hauwa ta saki jikinta take yin annashuwa a gidan kamar ba itace mai matsiyacin 'kuncin rai ba.
Baba Tabawa tun da can ma muka dan yi maganganu na fahimta don haka ta zame kanta ta same ni a d'aki tana ce mini sai na dage da addu'a da neman tsarin jikina domin dai ta gama fahimtar Hauwa ba ta kaunata kuma idan ta samu dama za ta iya aikata komai a kaina.
A tunaninta wannan k'uncin da nake ciki Hauwa ce ta yi mini asiri domin shiga tsakanina da maigidan.
To ba a 'kin ta mutum na amsa mata da to kawai ina kara jaddada mata addu'a kullum a cikin yin ta nake.
Ana haka Fadila ta haihu anti Yagana ta kira ni tana gaya mini ta samu 'ya mace na ce mata ina tafe.
A daran ranar duk da ba girkina ba ne na hau saman da na fi sati daya rabon da k'afata ta taka shi sai dai shi ya biyo ni d'akina yawan sa'in da muke yi a tsakaninmu ya sanya ya daina shigowa domin baya jin sukari a duk lokacin da zan mayar masa da martani magana ce mai zafi wadda za ta yi masa ciwo a raina.
Cikin jallabiya na same shi a can wurin da yake zama da Loptop din sa a gabansa.
Ita kuma ta ci gayu da k'ananun kaya matsatsen wando iya gwiwa da wata riga mai hannun shimi breast dinta duk ya ta'be ta d'auki wata hular gashi ta sanya sai kace irin tsotstsun arnar nan. kan sa yana kasa yana ta aiki ita kuma tana motsa masa shayin da ta had'a masa.
Na yi sallama cikin gaggawa ya dago kansa ya kallo bakin kofar.
Ido ya zura mini yana amsa sallamar ita kuma ta sai ta had'e ranta ta yi kasa da kanta can ciki ta amsa sallamar.
Gabad'aya kafatanin hankalinsa yana kaina har na zauna kujerar da take fuskantarsa a nutse amma babu walwala a fuskata na ce." Barka da dare."
A tak'aice ya amsa da "Barka dai ya kike?"
Ban bashi amsa ba na cigaba da cewa." Fadila ce ta haihu jiya gobe zan je maiduguri in sha Allahu.''
Kai tsaye ya ce.
" To shikkenan sai a shirya tafiyar ko?"
Kasa na yi da kaina ban ce komai ba mamaki dai nake yi yadda ya amince nan da nan bai yi jayayya ba can kasan zuciyata na gaya mini hanyar shiri yake nema shine dalili.
Na yun'kura na tashi da niyyar fita daga d'akin ya dubi Hauwa yana fad'in." Ban ji kun gaisa ba kuma kin yi mini alkawari kan cewa za ki gyara kuskuranki haka dai ki ka gaya mini kwana biyu da suka wuce ban ga ni a aikace ba ."
Na yi gaba ban tsaya jin abinda za ta ce ba.
Ai wanda ya ce baya sonka da farko daga baya ko ya zo ya ce yana sonka to k'arya yake yi ya fadi hakan ne domin cimma wata manufa tasa Hauwa ba zata ta'ba k'aunata ba dalilin da ya sanya kenan nake so na nisanta kaina da ita.
Idan da gaske zuciyarta babu damuwa mai zai sanya daga na shigo ta 'bata rai jikinta ya mutu saboda ganina.
Na shige na yi tafiyata ina jin sa yana magana ban juyo ba.
Sai da na leka d'akin yaran na same su duk sun kwanta Mairo na ta gyaran wardrobe dinsu aikin kenan ta yi tsifar kai ta wanke da yake Taburni ta iya kitson hannu itace take yi musu idan an kawo wankin kayansu ta goge ta shirya musu ta ba ni tausayi sosai ita kadai a zaune duk sun kwanta dole a rage mata wani aikin mussaman gugar kaya mai wankin idan ya wanke ya goge ta samu hutu ga tashin asuba haka suke ta fama.
Na ja musu kofar na nufi nawa d'akin da sau'kin zuciya domin Ina so na d'an matsa daga wajan da nake zaune ko zuciyata za ta yi sanyi na tsani na bud'e idona na kalleshi ko na ji muryarsa saboda tsabar haushin da yake ba ni a yanzu.
Har ni zai yi wa burga to Ina abin yake Hauwa dai macace amma a rashin mata domin dai da gabad'aya ta sullunce babu wata komad'a a tattare da ita idan har yana so ya tsorata ni ko kuma ya sanya mini kunci ya auro wadda ta fi ni komai shine zan daga hankali don yana soyayya da Hauwa a banza nasan duk buge ne.
don Allah kada ki karanta mini littafi ba tare da kin biya ni hakkina b.
Wanka na yi na sanya kayan bacci na yi kwanciyata a gado ina Kiran sunan Allah.
Na ji ya turo kofar d'akin ya shigo.