← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 253 OF 276

Sashe 253

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da na sake maimaita maganar tukkuna ya dube ni yana fadin." Don Allah kada ki k'ara mini wani b'acin ran Amina a bar ni cikin wanda nake a yanzu."
Na ce." A a ban gane kada na bata maka rai ba, zuwa duba jikin Gwaggo shine abin b'acin rai kuma?"
Ya shiru bai tanka mini ba."
Na ce." Ka dai duba don Allah babu rashin dacewa fa kuma ciwo ake dubawa."
Ya ce." To zan duba idan zai yiwu ."
Na ji wani takaici ya yun'kuro mini amma sai na danne na yi masa uzuri saboda yanayin da yake ciki na damuwa.

Haka muka wayi gari zuciyoyi babu dad'i da safe kafin na sauka kasa ta kira shi a waya aikuwa ya fashe tunda dama ya kumbura sumtum! jira yake yi a zungure shi ita in banda abinta tasan abinda ta yi kuma ai sai ta ja gefe ta yi zaman saurare.

Fadi yake yi "Ban yi niyyar sakinki ba Hauwa ku kaini 'kara kotu mara mutunci masu mance alheri.

Ni za ki yi wa wannan iskancin duk abinda nake yi miki ba ki ga ni ba sai kin had'a ni da uwata tuntuni na gaya muku ba ni son abinda zai d'agawa mahaifiyata hankali da girmana ku dinga yi mini terere babu wadda za ta rufa mini asiri ba ni da sirri a gidana.

Kin cire kunya kin gaya mata karya da gaskiya ba ni baki hakkinki ni za ki yi wa sharri Hauwa wato duk ko'karin da nake yi miki ba ki gani ko?

Ga ni ki ke yi yawan kwanciyar aure shi yake kawo haihuwa kina ganin daga 'bangarena ne haihuwar biyu da Amina take yi ba baiwa ba ce da rabo daga wurin Allah.

Shikkenan kin buk'aci rabuwa ni kuma ba zan yi rabuwar a lokacin da kuka buk'ata ba.

Na ji cikin rawar murya tana fad'in." Ni wallahi ban ce mu rabu ba, cewa na yi ka gyara kuskuranka ni ma na gyara kuskurena mu zauna lafiya ai kowa ya sani ka fi buk'atar haihuwa da Amina kuma soyayyar da kake yi wa yaranta ya fi wanda kake yi mini da abinda na haifa."
Na cika da mamaki kwarai jin yadda take fad'in ita ba tace su rabu ba kenan k'aryata Hajja za ta yi bayan su suka fad'i haka.

Ya ce." Kina nufin Hajja ta fad'i hakan ne kawai domin ta ji dadin bakinta kenan, so ki ke na lalace a gadonki na dingi jima'i dake saboda ki tara yara kin d'auka sakarai ne ni da ban san abinda nake yi ba, ko kin yi zaton ban fahimci gasar haihuwa ki ke yi da Amina ba.

Duk abubuwan da kuke gudanarwa a gidan nan daga ke har ita ina sane kuma ina bibiya shiru kawai nake yi muku.

Ba zan sake ki ba, kuma ba zan sake yin cikin da za ki haihun ba sai mu ga yadda za ki yi."
Ya kashe wayarsa yana huci!

Na dinga kallonsa gabana na fad'uwa.

Oh! ikon Allah wata ta kunno bala'i yana nema ya shafe ni Ubangiji Allah Ya sawwa'ke musu wannan masifa.

Na tashi na sauka bai ce mini komai ba ni ma ban yi masa sallama ba.

Bayan kwana biyu da kansa ya ce na shirya da safe sai mu tafi tare gabad'ayanmu zuwa kanon shima zai duba jikin Gwaggon.

Na yi godiya a takaice babu wani sakin fuska domin haushinsa nake ji ganin yadda yake nema ya jingina ni a jikin badakalarsu.

Tare muka nufi kano a washe gari wanda ya yi daidai da saura kwana biyu a d'auki azimi a ranar da daddare ni da shi muka je har gida duba Gwaggo da sauki za a ce amma dai da kyar ta gane ni.

Hamusu kuwa ya sha fad'a a wajensa ganin haka ya sanya ban yi masa nawa fad'an ba tunda an had'a gabad'aya an yi masa menene amfanin abinda ya yi wai kada a d'orawa mutane nauyi wannan maganar ta yi bala'in bata mini rai.

Da sassafe a ka d'auketa a kai kaita asibitin Malam tunda dama tana file Dr Iliyas da abokanan aikinsa suka shiga bata taimakon gaggawa.

Kwana daya ya yi ya juya ya ce yana da uzuri amma da shara'din na biyo bayansa da kwana biyu na ce masa to kawai ba ni kuma tsammanin bin sa sai na yi sati gidan Hajja na zauna bangaranmu na gidan.

Ban zo da mai aiki ko daya ba tunda tafiyarsu a cikin satin nan ne azimi da kwana uku ko hudu yaran kuma sun dan yi wayo ni da iyami mai aikin Hajja muke kula da su.

Da daddare ma da zan sake zuwa duba jikin Gwaggon a gida na bar su wajanta Magaji ya d'auke ni a mota zuwa asibitin Malam din.

Wani ikon Allah wai ana tunanin samun sau'ki da rangwami a wajan da aka kaita domin kula da lafiyarta sai abin ya kara rikicewa jikin ya'ki dad'i yadda ake buk'ata Gwaggo ta kai ta kawo sai da aka sanya mata abin numfashi a hanci saboda bata iya yi da kanta.

Kuka na dinga yi a fakaice saboda tashin hankalin ganin yanayinta wani siririn hawaye na zuba ta gefan idanunta tana daga kwance a gado(tun muna yara Iya kakarmu ta wajan Uba da zata rasu ta dinga yin wannan hawayen na gefan ido aka ce mana wai na sallama da duniya ne) Gwaggo na
mike a gado ana ta cuku-cuku a kanta duka rai ake yi wa wannan fafutukar amma zahiri ciwo ya ci karfinta sosai Gwaggo lokaci take jira domin tun ganin da na yi mata a gida na sare.

Babu wani kuzari muka fito daga d'akin ni da Hamusu ba mu jima muna magana ba muka yi sallama saboda dare ya yi na shiga mota Magaji ya ja muka fita daga asibitin.

Bacci mai cike da mafarkai marasa kyau na yi da asuba na tashi jiki a mace Ina zaune saman dadduma Yusi ya shigo da tsananin tashin hankali.

Ganinsa a hargitse sai gabana ya fadi ya furta.

Mama Allah Ya yi wa Gwaggo rasuwa.

Baba Hamusu ne ya kira ni a waya yana gaya mini wai yana ta kiran wayarki a kashe d'azu da asuba ta rasu.......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*167*
Mutuwa dai itace karshe mai yanke nisha'di da walwala mai jefa zuk'ata cikin firgici a lokacin da aka yi tabbas mutane na shiga cikin hankalinsu tare da tuna yaushe tasu zata riske su kuma a wace rana ne.

Mutuwa ko ta kafiri ce takan sanya tsoro da nadamar duniya to balle mutuwar mumunai daga cikin salihan bayin Allah.

Ha'kika mu da muke ahalinta mun yi rashi kuma mun koka 'kwarai da gaske bisa rashin ta da muka yi amma wani abin mamaki da ikon Allah yadda ma'kota ke kuka wiwi har da yara k'ananu bisa rashinta shine abinda yake bawa kowa mamaki.

Lallai Gwaggo tana d'aya daga cikin wad'anda Ubangiji Allah Ya fadi cewa tundaga mutuwarsu ake gane cewa 'yan aljanna ne.

Sosai ta samu jama'a kwarai da gaske haka zalika duk wanda zai zauna ya tashi sai ya fadi alherin da ta yi masa da jikinta ko kuma da aljihunta.

Gwaggo ta samu sheda daga wurin ma'kotanta da sauran abokanan arziki duk tsayin zamanta a garin kano a kuma cikin unguwar da take aure babu abokin fad'anta tsakaninta da kowa lafiya ta rabu.

Gari yana yin haske kad'an muka tafi ni da Hajja da Yusi lokacin tuni an kawo gawar daga asibiti ma'kota mata sun cika gidanta mazansu a waje da sauran danginsu abbansu Yusi tunda dama ba wani yawa ne da su ba layin cike yake da jama'a yara da manya cikin alhini da tashin hankali.

Sai yamma tukkuna mutanan maiduguri suka iso cikinsu har da Dada kakarmu na dinga mamakin ko'karinta tunda itama bata da wani 'koshin lafiya.

Ta ci kuka kuwa sosai tana fad'in ta so ta zo ta samu gawar aminiyarta ta yi mata addu'a.

Anti Yagana Ya Falmata da kuma iyalin baban Saude dana Babanmu Babagana mahaifinsu babandi tare muka yini da su da magriba Hajja ta ce na kira mata Magaji suka yi waya ta ce ya d'auko babbar motar da za ta d'auke mu gabad'aya mu tafi can gidan nata mu kwana gabad'aya har da su tunda gidan Gwaggo bashi da girman da zai d'auke mu duka.

Haka kuwa aka yi bayan isha'i magaji ya zo a lokacin ne muka yi sallama da Ummansu Hadiza da Fati suka tafi tunda suma tare duk muka yini Babanmu kuwa da shi aka yi jana'izar Gwaggo shine akan gaba.

Ita kuma Ummansu Saminu tana kwance bata jin dadi dalilin da ya hana ta zuwa kenan.

Shi ma Usaini ya yi wa Hamusu kara sosai domin yinin ranar rufe shago aka yi duk suka zauna wajan kar'bar gaisuwa har ya kawo matarsa Hajara muka yini tare da su gabad'aya tana ta fama da d'an cikinta da ya huda zani ya fito kurcici sosai na ji dad'i bisa wannan karar da suka yi mana.

Hajja ta sanya aka gyara musu d'aki a cikin falonta tunda da akwai dakuna hud'u duk kuma a shirye suke gyaran da Iyami ta yi kad'an ne tace su shiga su huta kafin a kawo abinci.

Muna tare da su gabad'aya don sai a lokacin ma iyalin baban Saude ke yi mini barka tunda ba su samu ikon zuwa taron sunan da muka yi ba kamar yadda ya yi mini alkawari saboda rasuwar mahaifin Mamansu Abahuraira amaryarsa kenan.

Na ce da su babu damuwa komai nufin Allah ne.

Sun yi godiya sosai wai ba su zo ba amma sakon turaman atamfofi ya iske su har gida.

Ranar Kamalu muka yi bidiyo call da Kamalu ya yi wa kowa ta'aziyya tare da jajantawa cikin alhini to ya za a yi abinda kowa yake fad'i kenan lokacinta ne ya cika amma abin farincikin rahamar Allah da ake yi mata zato.
Chapter 253 · 0% Book details