← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 219 OF 276

Sashe 219

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kaina na shiga kicin tunda ya sanya an kawo mini komai na bukata.

Na soya doya da kwai da tea sannan na dafawa kaina indomee.

Nan d'akina muka yi breakfast din babu yabo babu fallasa amma dai na kasa sakin jikina duk zantukan da yake akan auran nan da zai yi kawai ina jinsa ne da kunne dalili nema yake yi ya rainawa mutane hankali tunda yadda yake nunawa ko jininsa dana yarinyar bai daidaita ba zai iya yin jayayya da malamin ba yadda tun farko ya amince masa to abu ne mai wahala daga baya ya je ya ce masa ga matsala wadda daga baya turawa suka bijiro da ita tunda ai ko a zamanin annabawa ba a san da wani gwajin jini kafin aure ba haka kuma duka iyaye da kakanni suka ta so.

Da haka dai ya yi wanka ya kintsa ya fita yana gaya mini ya yi baki daga kamaru idan ya gama dashi da wuri zanje bunkure a takaice na yi masa addu'ar dawowa lafiya
Sai wajan daya da rabi Sahura ta zo lokacin ne ta taso daga aiki.

Sai bayan da muka ci abinci muka yi sallah tukkuna muka fara aikin gyaran gidan wanda kusan zan iya cewa itace karfin aikin ta shasshare mini ko'ina tas aka yi mopping gidan ya dawo hayyacinsa.

Sannan fa muka zauna ina zolayarta ta yi ki'ba tana ta'be baki kuma da gasken ta yi kiba wallahi alamu sun nuna bata da damuwa tana cin gashin kanta.

Idan farko akwai damuwar yanzu makomar auran Idiris ta bayyana ya sanya mata nutsuwa da kwanciyar hankali domin dai alkali ya tilasta shi sakin yarinyar kamar yadda iyayenta suka buk'ata dalili shedu sun shaida babu abinci ingantacce a gidansa sannan kuma alamu na nuna cewa shi din yafi karfinta ta fannin auratayya.

Ya kuma yanke masa kudin da zai dinga aikawa yarinyar na goyon ciki har sai ta haihu ta shayar masa da abinda ta haifa kafin ta yaye ya kar'bi d'ansa a bisa adalci.

A wannan matsayar aka tsaya da shi.

Tana gaya mini da gumu ta yi gumu ya rasa yadda zai yi ya gaya mata halin da ake ciki.

Na ce." To Sahura tunda dai ya yi nadama sai ki yi hakuri don Allah kada dukan ya yi masa yawa ki kaddara cewa rabon haihuwa ne ya sanya shi rakito auran yarinyar nan."
Ta ce." Ai ban hana shi kwana a gidana ba Amina kwanciya da ni ne na ce ba zai yi ba.

Kuma gidan da ki ka ba ni ya balle ni kwado ya sanya matarsa sun kwashe kaya sati biyu da suka wuce na sanya a zuba mini 'yan haya a ciki.

Abincin dai ina ba shi idan na yi ga waje nan ya kwanta ya tashi amma babu mu'amula ta aure.

Na ce." To kin sake bashi lasisin yawon dare kenan?"
Ta'be bakinta ta yi ba tace komai ba.

A daidai lokacin kira ya shigo wayata ina dubawa na ga maigidan ne na ajiye ta katse ya sake kira na d'auka tare da daidaita maganata.

Na ji yana fad'in." Na fasa zuwa bunkuren nan Amina gani nan dawowa gida."
A tak'aice na ce." To.'' na riga shi kashe wayar na ajiye a gefana ina tsaki
Ta bata rai tana fad'in." Menene haka don Allah."
Na ce." Da aka yi me?"
Ta gyad'a kanta tana cewa." Wallahi tallahi ki ji tsoron Allah akan mutumin nan Amina."
Sosai na zuba mata Ido da mamakin maganarta haka kawai ba ta san irin zaman da nake yi dashi ba tana cewa na ji tsoron Allah akan sa.

Ko da yake dama can ita 'yar dakinsa ce bata ta'ba ganin lefinsa.

To mai baka kuma ya ninke munanan halaye ya bayyana kyakykyawan ya za a yi ta fahimci aibunsa tunda ba tare take rayuwa da shi ba.

Ta cigaba da cewa." Menene abin tsaki don ya gaya miki cewa zai dawo gidansa ne fa."
Na ce." Hajiya kamata ya yi ki tambaye ni dalilin dawowata nan ba kawai kai tsaye ki fara tuhumata ba ke matsalata dake kenan ba kya taba ganin lefinsa.

A d'an sanyaye ta ce." Menene to?"
Duk abinda yake faruwa na gaya mata tun daga kan matsaltsalun da yake tsakani na da Hauwa da auran da aka bashi a bunkure.

Ta yi sakato da baki tana kallona gabad'aya bakinta ya mutu da kyar ta ce ni haukan da Hauwa take yi bai dame ni ba Amina sai maganar auran nan da ki ka ce zai yi ai na gane yarinyar da ki ke gaya mini ko ba itace ta kawo mini abinci a lokacin da naje ba."
Na ce." E ita ce.''
Ta zura mini ido tana kallo kafin ta ce." Ai ko nono ba ta dashi wannan yarinyar ba ta isa aure ba don bata da 'barage ba na tsammanin ba ta fara jinin haila."
Na ce." To ya kar'bi dai auranta sai ya cigaba da raino amma dai da kamar wuya tunda d'azu yake gaya mini wai za su yi gwajin gyonotype kin ga kuwa da sha'awar sabon waje a cikin ransa mussaman budurcin k'aramar yarinya irin wannan ba na tunanin zai zura mata tsayin wasu shekaru."
Ta ce." Don Allah ki daina fad'in haka Amina kunya ma nake ji wallahi yanzu shi sai ya iya tu'bewa a gaban wannan tatsitsiyar?"
Na ce." To me ye a ciki Amina wallahi ki daina mamaki da sha'anin maza abu ne mai sau'ki a wajansa."
Ta yi zugum tana dubana kafin ta ce." Lallai mutumin nan ya ba ni haushi wallahi gaskiya abin bai yi mini ba ya kuma shirya cinye muku fuska yarinyar 'yar cikinku ta kalleku a banzance tunda ai duk ranar da ya kwanta da ita to gabad'aya ba ku da bambanci wallahi.

Na yi shiru Ina nazarin maganarta tabbas hakane ranar da ya kwanta da Hajara to itama daga lokacin za ta ji kanta a matsayin matar gida daidai da kowa.

Ba ni fargaba akan tarbiyar yarinyar amma yau da gobe idan zama ya yi zama dole wasu daga cikin d'abiunta su canza dalili itama tana ji kanta cewa matar gida ce."
Sahura bakinta ya mutu duk kaud'in nan nata a kansa bakinta murus ya yi tana jin haushin haka ta yi la'asar ta yi mini sallama ta tafi.

Ba ta jima da barin gidan ba ya dawo.

Ya yi wanka a dakinsa na sama ya canza ya kaya na shan iska ya sauko kasan ya same ni zaune a kujera Ina kallo ya zauna kusa da ni yayin da kamshin turaransa ya game wajan gabad'aya.

Na dube shi kad'an kafin na janye idona ban ce komai ba.

Sai ya riko hannuna yana cewa." Ta karfi da yaji dai kin zama bebiya giwa wai me ya yi zafi ne uhum?''
Ban ce komai ba na zare hannuna.

Ya kamo yatsan da ya sanya mini zoben nan ya sumbuta ya ciro shi daga yatsansa ya sake mayar mini yana fad'in." Ban yi zuciya ba amma ya kamata ki sassauta mini ki yi mini adalci akan duk abubuwan da suke faruwa ke kan ki kin san abinda ki ke yi ba daidai ba ne ko?"
Na ce." Adalci wane iri kake so na yi maka na hana ka kar'bar auran da aka baka ne?

A lokacin daka gaya mini addu'a na yi maka kuma dole sai ka yi hakuri a wannan lokacin tunda ni kaina ba jin dad'in jikina nake yi ba."
Ya d'ora hannunsa saman cikina yana fad'in." Na sani amma me yasa ki ka cire duk wani subsidy a kaina kin daina sona ne."
Ban iya kallonsa ba saboda takaici.

Ya juyo da fuskata yana cewa." Zan fasa auran nan fa wallahi ba zan iya ba."
Na yi shiru dai ban ce komai ba daidai lokacin ne Hauwa ta kira shi yana d'agawa ta fara kuka tana fad'in." Minal ce ta suma!"
Ya ki'dime sosai hannunsa har yana karkarwa yana tambayarta ya ake ciki yanzu.

Yadda take bashi amsa ya sanya na fahimci cewa k'arya take yi wallahi.

Kawai dai za ta fake da ciwon yarinyar ne ta daga masa hankali.

Ya kashe wayar da tsananin tashin hankali yana fad'in." Ki yi wa Allah da annabi ki tashi mu tafi yarinyar nan Minal tana sonki Amina kada hakkinta ya kama ki tunda ta dalilinki komai yana iya faruwa kada mu yi rashinta.

A nutse na ce." Ka je ka kawo mini su nan gabad'aya zan ri'ke su Ina nan akan bakana ba ni sake zama da Hauwa.

Idan kuma za ka canza mata gida ni ta bar mini wanda take ciki sai na koma."
Ya ce." Ba ki ji an ce suma take yi ba.

Na gaya miki cewa jikinta ya'ki dad'i wallahi tunda ki ka bar gidan nan."
Na ce." Ni da hankalina sarai babu abinda Hauwa za ta k'irkira ya firgita ni.

Minal kuwa Ina tsammanin ma uwarta ba ta kaini sonta ba."
wannan littafin dai na kudi ne don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Ya yi shiru yana kallona na wani lokaci kafin ya haura samansa.

Na dubi agogo biyar da rabi jim kad'an ya sauko cikin manyan kaya babbar riga da 'yar ciki.

Cikin zuciyata na ce." Aiki ya same ka in dai Hauwa ce sharrinta yawa gare shi neman kudi ma wataran sai ka yi da gaske za ka yi."
Ya tsaya gabana yana fad'in." Rarrashi da ban ha'kuri babu irin kalar da ban yi miki ba.

Ba a yi maccan da zan dinga kwantar mata da kai tana gara ni kamar gare-gare ba.

Ki sani Amina kina da magabata kuma hukuncin saki a hannuna yake sai na ga dama zan yi.

Wallahi tallahi zan d'auki mummunan mataki akan abinda ki ke yi mini.

Na ce." Sanar da magabatana halin da muke ciki shi zai kara dagula maka lamari domin wallahi ba zaka taba samun kaina ba.

Shekara nawa ina ha'kuri dakai tare da bin umarinnka ina so ko ba ba na so.

So kake yi na zauna da Hauwa wataran ta d'auki makami ta farauci rayuwata.

Ko za ka gaya mini cewa har yanzu ba ka fahimci irin tsananin kiyayyar da take nuna mini ba.
Chapter 219 · 0% Book details