Sashe 272
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya yi addu'a akan samun haihuwa kuma diya mace wadda ya nema a wurin Allah Ya amsa masa sai kuma ta zo a maririya mai rangwamin lafiya wannan ma jarabawa ce me zaman kanta amma godiya ga Allah itake nuna cikar munini tunda ai akwai ma'auranta da duka yaran nasu suke kasancewa da cutuka mabambamta kuma daya bayan d'aya ya d'aukesu su koma gare shi bayan iyayen sun sanya rai kuma ba su gaza ba wurin nemo musu magani da kudi da lafiyar jikinsu.
Ubangiji ta kowace suffa ya kan jarrabi bayinsa wanda yake so domin auna imaninsu.
Da wad'annan nasihun na d'an samu kansa amma ko bayan wannan nasan damuwar ai tana jika dalilin abinda Hauwa ta yi tamkar ba jininsa ba k'iyayyar ta munana ta kuma tsananta Allah ne mai rayawa kuma shine mai kashewa shi ya ba mu don ya kar'ba ai ba mu da abinda za mu yi tunda mu da muke zaune a duniyar zaman jiranta muke yi.
Wannan shine kawai abinda na bari a zuciyata maganganun Hauwa akan yarinyata ba su razanar da ni ba, musulmace ni dole kuma na yarda da kaddara mai kyau ko mara kyau.
Haihuwa ya ba ni ya sake ba ni ya ba ni ta mussaman wadda ba kowa ke da baiwar ba har sau biyu masu lafiya rayayyu guda shida yana kuma raya mini su cikin aminci da kulawarsa da kuma tarbiyarsa babu abinda zan ce da shi sai godiya kuma duk abinda ya zartar daidai ne.
Da Baba Tabawa muka kasance a asibitin tunda gaskiya akwai tsaro sosai ba su barin wannan shige da ficen itama saboda maigidan sananne ne yana kuma da alfarma ya sanya suka barta ta zauna.
Alhamdulillahi cikin kwanaki hud'u abubuwa sun yi sau'ki ta daina duk abinda take yi tana kuma kama nono ta sha cikin nutsuwa ta yi baccinta da kwanciyar hankali.
Muka samu nutsuwa ni da shi mussaman da likitan yake jaddada mana cewa muddin an kula an kiyaye komai kan ka'ida ciwon ba zai dinga motsa mata ba a kai-kai.
Kwananmu takwas muka dawo gida.
Ya zama kamar kufai shiru babu hada-hada ta yara duk suna ma makaranta masu aiki Mairo da Taburni na kicin Hassan da Usaini na bacci bayan wankan da aka yi musu shi kuma Sultan na tare da su a kicin.
Na kira Hadiza a waya na gaya mata na dawo cikin kasa da minti ashirin sai gasu gabad'ayansu suka kewayeni duk babu wata annashuwa a tare da su babyn tana ta bacci babu halin d'aukarta domin dai likitanta ya bada umarni hakan kada a yawaita jagwalgwala mata jiki sai dai ido kawai Fati take tambayata da wane suna za a dinga kiranta tunda wai Sukairaju ya gaya musu sunan Hajja ne da ita na ce Mufida haka babanta ya ce a kira ta.
Yini muka yi tare da su har yaran suka dawo daga makaranta ganina a gidan ya sanya su shiga tsananin murna hankalinsu gabad'aya nakan babyn sai sun d'auketa Minal har da kuka sai da na kira Mairo tukkuna na ce ta ja ta su fita domin wani irin ciwon kai nake yi kukan da take yi kuma yana sa'bata da yanayin yadda duk na gansu cikin damuwa mussaman Khalil duk jikinsa ya yi sanyi na kasa gane shin akan menene ba ni tsammanin ubansa ya gaya masa ya saki uwarsa sai dai idan ita za ta gaya masa kuma ba na tsammanin ta tafi tana gidanta tunda na ji lokacin da yake magana da Mairo yana gaya mata sakon Ladidi tunda k'awarta ce idan Hauwan ta aikota sukan dan jima suna hira akwai wani k'aramin gari a cikin bauchi mai suna giayade anan cibiyar iyayensu take duk da ba su had'a wata dangantaka ba hirar yau da gobe ta sanya suka fahimci garinsu daya.
Washe garin ranar da muka fito Hajja da yayarsa suka dira dama ya gaya mini shine ya dakatar da su tunda ko sun zo muna asibiti ganin hakan ya sanya ni ma na hana anti Yagana zuwa tukkuna can gidanmu ma haka na gayawa Babanmu a waya cewa su bari sai mun fito Sahura kuwa kusan kullum sai mun yi waya.
Sai dare tukkuna muka samu ke'bewa Hajja fadi take yi Hauwa abinda ta yi muku Amina Allah Ya yi mata ba zan yi mata baki ba ba kuma zan nunawa duniya Tajo ne nawa ba amma da wahala ta sake yin katari da namiji da abokiyar zama kamarki zahiri kin yi iyakacin bakin kokarinki wurin ganin kin kawo daidaito a tsakaninku kin yi bajinta kwarai kuma kin yi da jiki da aljihunki a tarihi ban ta'ba ganin kishiya irinki ba Allah ya biya ki da aljanna Ubangiji Allah Ya dubi rayuwarki.
Wad'annan yara kuma ina yi miki addu'a akan Allah Ya ba ki wuyan d'auka Allah Ya raya mana su.
Na dinga amsawa da Amin Amin amma bayan haka ban iya furta komai ba akan abinda suke tattaunawa Hajiya Saratu tana ta fad'a akan zaman da take yi tunda an yi ta ta kare babu wata sauran igiya zaman me take yi kuma har tana fad'in da safe za ta je gidan ta ji dalili babu sauran wani mutunci da zumunci a tsakaninsu tunda har ta iya rufe idonta ta yi wa dan uwanta wannan cin fuskarsa.
Gaskiya ne a wannan ga'bar takai-takai kawai ake yi kowa nasa ya sani domin kuwa abinda ita Inna Uwanin ta nuna kenan.
Wannan karon Hajja ta saki ragamar hannun yaranta ai kuma magana ta 'kare babu sauran gyara babu amfanin zamanta a gidan ta kama hanya ta tafi yara kuma ta bar su a gidan ubansu.
Da wannan suka rufe maganar ni dai magana akan Hauwa ta k'are a bakina domin ban san abinda zan ce ba ta gama goge mini hadda ta tilawa.
Aikuwa kamar yadda ta kwana da al'amarin garin Allah Yana waye wa ko karyawa ba ta yi ba ta nufi gidan Hauwa.
Ni dai Ina d'aki da yake kofar a bud'e take saboda yaran sun shigo mini kafin su tafi skull na ji fad'anta a falo har ina tsinkayar muryar maigidan.
Fadi take yi zaman nata ai bashi da wani amfani ban kuma yarda da abinda ta fad'a ba wai juna biyu gareta ko za ta tafi sai a bari ta haihu tukkuna shin kai ka san cikin ne da ita.
Cikin rashin karfin sauti na ji maganarsa amma ban ji abinda yake cewa ba.
Na yi zuru ina mamaki cikin da take ta ha'kilo a kansa shin tasan dama tana dashi ta yi wannan rashin mutuncin ko kuma dai karya take yi don kada ta tafi ne.
Wani sashi na zuciyata ya dinga gaya mini karya take yi da tana da ciki da kowa ya sani tunda abinda take nema ne kenan kuma ba zata zafafa bakincikinta ba.
Can wajan minti ashirin da biyar a tsakani na dinga jin kuka kasa k'asa da maganganu suna tashi sai da na kasa kunne tukkuna na gane muryar Hauwan ce take wani irin kuka mai cin rai Hajja tana ta yi mata magana akan ta yi shiru amma sai kara karfin kukan take yi.
Cikin babban sauti na ji muryar Hajiya Saratu tana cewa kan ki kika tonawa asiri Hauwa ba mu za'bi Amina ba saboda muna 'kin ki.
Mun za'bi kyawawan halayenta ne da kuma biyayya amma tunda yanzu magana ta kare babu buk'atar a yi ta maimaitawa sai dai addu'ar Allah Ya fitar da sakamako da gaggawa a tsakaninku wanda ya cuci wani sai Allah ya saka masa ba mu da wata hanyar gyara kuma babu wata mazahaba da za a bi saki ukun ai ba a lokacin daya ya yi miki su ba an yi daya da farko ya zo ya maimaita miki biyu saboda haka baki fara yin nadama ba Hauwa kuma muna nan ba za mu fasa addu'a ba idan shi ya cutar dake kamar yadda kike yawaita fadi Allah Ya saka miki.
Saboda irin bud'e wutar da Hajiya Saratu ta yi a gidan sanya kowa jikinsa ya yi sanyi masu aiki kaf ba su fito ba domin sun jima a falon suna musayar yawu tana ta jaddada mata 15m din da take tunanin maigidan ne ya bata to ba shi ba ne ni ce hakan ya kara tsananta kukanta ina daga d'aki ina Jin gurnaninta cikin tashin hankali kamar wadda ke shirin tayar da sarkin aljannu.
Shi gabad'aya ma bai sauko ba balle ya tanka takaici da b'akinciki ya na ta nukurkusarsa.
Babu arziki Hauwa ta kama hanyar garinsu jin zafafan kalamai raddi masu kauri da jefa zuciya cikin rud'ani
da bala'in yanayin da ba zai misaltu ba dama aka ce duk wanda ya ce tukunyar wani ba zata tafasa ba tabbas ta shi ko d'umi ba za ta yi ba.
Washe gari Nusaiba ta zo mini da yaranta kaf muka yini tare su kuma su Fati suna jiran zuwan anti Yagana tukkuna don ba su kai ga tafiya ba.
Kwana biyu a tsakani ta iso da yamma kuma matan gidanmu gabad'ayansu har da Babanmu da Baba Sule suka kwana da yamma suka yi shirin tafiya gabad'aya amma ban da anti Yagana saboda na ce ta bari tukkuna sai nan da sati d'aya
Yaran shop's dina har da securities din dake gadi a wajan Lawan ya jagorancesu a daran da su Fati suka tafi muka jima da suma muna tattauna cigaban da ake samu koyaushe.
Haka na dinga samun baki daga wannan sun tafi wasu za su zo Sahura ita kadai ta zo mini wannan karon Yusura ta sake samun ciki sai kawai na ganta da yarinya jale-jale tana koyar tafiya yarinyar Idiris ce uwarta ta cire ta daga nono lokacinta bai cika ba ta yi aure a cewarta baya kawo kudin abincinta iyayanta suka ce ta cire ta daga nono a kai masa 'yarsa suka kawota suka dire babu Imani uwar ta tafi ta yi aure.