← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 276

Sashe 122

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abu na biyu kuma ga yanayin bayanin da Kamalu ya yi mini yadda na fahimta shine shi Salim yana adawa da yadda Allah ya d'aukaka Kamalu fiye dashi, ai nasan yaron yana da kirki tun kafin ya tafi karatu dawowarsa al'amura suka lalace kishi ne shi mai yasa Allah bai yi masa ba."
Ta ce." Wannan kuma Ubangiji zai kalubalanta.

Wace irin wahala da gwagwarmaya ce Kamalu bai sha ba.

Yanzu kuma Ubangiji Allah Ya d'aukaka darajarsa wannan duka ba dabararmu ba ce ikonsa ne, gaskiya a wannan ga'bar ni ma bana goyan bayan mijinki Amina Kamalu dole ya tafi ya bar musu gidansu idan sun ce ba haka ba sai ya dawo hannunki shine karshen magana."
Na ce." Anti Yagana ni na fi so fa ya koma kanon ko ya dawo nan wurinku hankalina zai fi kwanciya gaskiya, domin ai ko yana gidana ba a kashe matsalar ba tunda duk lokacin da ya fita zai iya yin karo da Salim da abokansa kin ga matsalar ai bata mutu ba."
"To ni da kaina zan kira Yallabai din a waya na bashi shawara yadda za a yi.

Ta fad'a tana nishin 'bacin rai."
Jin haka ya sanya na ce." Kada ki kira shi yanzu anti Yagana mu bari ya zo mu ga hukuncin da zai yanke idan babu adalci sai ki yi masa magana."
Ta ce." Shikkenan haka za a yi in sha Allah, na manta ma ban gaya miki ba shekaran jiya amaryar Babandi matar da ya aura ta uku ta haihu." A takaice na ce.'' A yi masa barka Allah Ya raya, domin ni yanzu ko lambarsa ma ba ni da ita yadda maigidan ya tsaneshi haka ya tsani mutuwarsa shiyasa na goge lambarsa daga wayata a gabad'aya duk domin a zauna lafiya.

Bayan sati biyu al'amura suna cigaba da tafiya da dad'i babu dad'i.

Har zuwa lokacin Salim bai kyale Kamalu ba.

Kusan kullum da b'acin rai yake shigo mini duk da yana ko'karin daurewa amma ina fahimta.

Ha'kurina yana daf da k'arewa domin tun ranar da na kira maigidan a waya na gaya masa abinda yake faruwa bai sake nema na da maganarba duk kuwa da cewa kusan kullum sai mun yi bidiyon call.

Ni ma ban sake tayar da maganar ba na bari ne kamar yadda ya ce mu jira zuwansa.

Amma koyaushe idan na dubi Kamalu na ga yadda ya rage walwala da kuzari zuciyata takan yi zafi.

Ina dalili haka kawai saboda gudun b'acin ran wani a 'kuntata zuciyar yaro.

Babu lallai fa babu dole muddin ba zai d'auki mataki ba wallahi sai Kamalu ya tafi ya bar garin da gidan gabad'aya.

Gudun aure littafin kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Ranar litinin da yamma suka sauka shi da Hauwa.

Baiwar Allah ta kuma samo wani cikin domin yanayinta kadai ya tabbatar mini da cewa laulayi take yi ta yi mugun haske dama idan tana da ciki d'ashewa take yi.

Macace mai kwainika Minal na da wata goma sha takwas.

Allah Ya sa tana da san girma, tana yawo da kafafunta da yake abincin gwangwani take ci a can ta zama rusheshiya kataf-kataf haka take yawo uban yana tsokanarta da 'yar sukuta. ko ya kira ta da giwa wai na washeta har ta fi su Hassana girma jiki tunda su jikin irin nasa ne.

Kwana biyu da zuwansu na fahimci rashin jituwa a tsakaninsu.

Kamar ma basa magana da juna.

Na yi dai shiru ina kallon ikon Allah.

Ita yini ma take yi a d'aki sai yamma take fitowa falo shi kuma har ya yi kwana biyunsa a wajena bai ce mini komai ba.

Na cika da mamaki sosai.

Lallai ma wannan mutumin wato maganar tabi shanun sarki kenan Salim ya yi daidai babu kuskure akan abinda yake yi.

Ba zan lamunta ba domin kuwa har yanzu a cikin matsalar ake sai abinda ma ya yi gaba.

Kamalu bai rasa madogara ba hakama Yusi idan har ba zai gyara abinda yake faruwa ba to na yarda ya ba ni yarana su kuma can hannun Babansu Hamusu.

Cikin wannan nazarin Hauwa ta shigo d'akina ta same ni.

Ta zauna gefan gado tana fad'in." Ko jikin ne?" Na tashi zaune Ina fad'in." A, a ni kam ai na warware na bar miki Hauwa."
Kwafa ta yi tare da cewa." Ban ji dad'in shigar cikin nan ba wallahi.''
Na dubeta a tsanake tare da cewa." Mai yasa Hauwa ki godewa Allah da fatan samun masu albarka."
"Humm!" abinda ta ce kenan kafin ta ce." Ban shigo domin na tunzuraki ko tayar da husuma ba.

Idan kin lura da yanayin yadda muka zo da ni da maigidan babu dadi don wallahi mugun haushinsa nake ji fad'a muka casa tun a can."
Na ce." Menene kuma ya kamata ki manta da matsalar matar nan Hauwa, ki yi ta kanki haihuwa ta uku za ki yi da mutumin nan duk abinda zai yi ya je ya yi haka ya ga zai iya."
"Wallahi Amina ko kaffara ba zan yi ba matar nan ba haka ta bar mutumin nan ba."
"Mai yasa ki ka ce haka Hauwa, zato zunubi ne fa koda ya kasance gaskiya ne?"
"Amina maganar gaskiya zan gaya miki na gaji da zaman nan da muke yi na rashin 'yanci da kaskanci wallahi tallahi ba zan jiya jure ba, wannan shine dalilin ma da ya sanya ki ka ji na ce ina b'akinciki da takaicin samuwar wannan cikin na jikina, in banda ina gudun sa'bawa Allah wallahi da sai na zubar da shi.......
*Rikicin gidan Alh Tajo sai dai na ce Allah ya yayyafawa abin ruwan sanyi bari mu ya ya zata kaya....*
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*83*
Na ce." Ai ba ta yi lefi ba gaskiya ta fad'a domin shine zama na amana.

Kuma wallahi a yanzu ni Amina Hauwa ta fiye mini kai sau dubu tunda ka nuna mini zahirinka na gani, ni duk wanda za a had'a kai dashi a k'yamaci abina, ba na daukarsa a matsayin masoyi babban ma'kiyi nake kallonsa."
Da wani irin yanayi a tare da shi ya furta." Idan na fahimce ki kenan kina kallona a matsayin ma'kiyinki wanda ya za'bi Maryam da 'ya'yanta ko Amina."
Na ce." K'warai kuwa wallahi tallahi ba ka cikin jerin masoyana tunda har ka iya yadda da cewa Kamalu zai aikata wannan mummunan lamarin.

Ba na yi maka kallon masoyi."
Ya jima yana kallona kafin ya gyad'a kansa ya nufo ni, na kuwa zabura domin kallon dodo nake yi masa na ce." Kada ka zo inda nake na rantse da Allah zan illataka."
Bai daina tafiya ba har sai da ya cimmani zai ri'ke hannuna na fizge da sauri na wancakal da nasa hannun cikin zafin nama na yi wajan madubina na zari wata doguwar kwalba ta turare na ri'ke a hannuna.

Ya sake nufo ni yana fad'in." To illatani kin ji, na ce ki illatani tunda kin 'ki tsayawa mu fahimci juna.

Da k'araji na ce." Har abada na sake aminta da maganar munafiki."
Ya 'bata fuska ainun yana fad'in." Kada kuma ki wuce gona da iri, kin naushe ni a ma'karfafata d'azu na kyale ki yanzu kuma kina kira na da munafiki ranki zai b'aci fa ba ni son rashin hankali."
Na ce." Ya 'baci ma ai ba tsoro nake yi ba, menene karshen hukuncin shine saki ko to ka sake ni kaga yadda ake liyafa ai ni kassara mini rayuwata ka yi zama dakai bai amfanar da ni komai ba."
Ya kuwa 'kadu da wannan furucin ya ce." Har yaran da muka haifa ba su da amfani?" Na ce." E, ai ba nawa ba ne tunda ka d'aukesu ka bawa bushshiyar matarka nata ne taje na bar mata."
Ya dinga kallona da mamaki mai yawa kafin ya sake tunkaro ni a karo na biyu na daga abinda yake hannuna zan buga masa ya yi saurin ri'ke hannun tare da k'wacewa.

Muka yi cirko cirko a tsaye shima nishin yake yi kamar yadda nake yi kamar wanda ya yi tsere.

Mun jima haka ya ri'ke ni katamau na ja tsaki tare da yun'kurin bangaje shi ya riko kafadata jikinsa duk ya yi la'asar.

Na ce ka cika ni na gaya maka
na rantse da girman Allah da Annabi sai yaran nan sun bar hannunka tunda ka gaza ri'ke su tsakani da Allah ko da hakan zai yi sanadiyar rabuwarmu
"Ba ki da hankali har yanzu ko Amina?"
Na ce." E, ba ni dashi tunda kai din shine da kai." Murmushi ya yi ya girgiza kansa yana fad'in." Ke kam kin ci sa'a ina sonki ina ga da babu wannan da tuni mun rabu baram-baram, iskanciki da rashin kunyarki ya ishe ni.

Yanzu ni ne mara hankali Amina baki da kunya ba ko."
Juyar da kaina gefe na yi ban ce komai.

Sai ya girgiza kansa a nutse ya fara ko'karin jan hannuna yana fad'in." Zo mu je mu zauna domin mu tattauna."
"Ba zan zauna ba domin ba ni son had'a numfashina da kai." Na fad'a tare da buge hannunsa da yake jana.

Sai kuwa ya sanya mini karfi ban ankara don kamar tanka'dani ya yi na fadi a da'bas a wurin.

Kafin na yun'kura na tashi ya cimmani ya sake tura kirjina da k'arfi na kwanta kaina ya tallafo kawai yasa bakinsa a nawa ya dinga d'ura mini yawun bakinsa ba don ya ji dad'i ko don na ji yake kiss din bakina ba domin ya sanya mini yawunsa ne.

Tsayin minti hud'u zuwa biyar ya cire bakinsa tare da tashi tsaye ya tsaya a kaina yana kallona idonsa ya kada sosai da tsantsar tashin hankali a cikinsu.

Na tashi zaune hawaye masu d'umi suna silalowa daga idona.
Chapter 122 · 0% Book details