Sashe 275
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna Uwani sai da fita ta gagareta saboda kunya da tashin hankali irin lalataccen kallon da 'yan uwan mijinta ke yi mata sai ta zama abin kallo ma domin
har gida aka dinga zuwa ana yin ala wadai da irin yadda ta bada goyon bayan aikata abinda Allah Ya haramta shi kuma Naziru ya riga ya gayawa mahaifiyarsa cewa bai auri Hauwa don ya saketa ba.
Amma kuma ita sai ya ce mata idan har tana so ya saketa sai ta kara masa miliyan biyu kudi sun kama miliyan biyar da yake hankalinta a tashe yake da barin gidansa babu ja'inja ta k
ra masa.
Da wannan hanyar ya dinga kar'be mata kudi har sai da ya zama ya tatiketa tsaf kuma ya ce ba zai saketa ba saboda yana sonta dangi kuma kaf suka goya masa baya.
Lamarin da ya janyo mata mummunan ciwo jininta ya hau aka dinga tiri-tiri da ita don har kwanciya ta yi a asibiti a lokacin ne muka samu labari ni da shi mun je kano hutu zai d'an gudanar da wani aiki Hajja take gaya mana halin da ake ciki domin dai duk yadda lamarin ke yi mata zafi a ranta sai da ta je har can bauchin ta duba jikin Hauwan ta kuma ce masa lallai ya tura mata da kud'i domin jinyya saboda babu tunda har ya yi rantsuwa akan janye kyautar kamfanin da ya yi mata ya ce babu amfanin mallakawa ma'kiyi abinda zai kawo masa cigaba a rayuwarsa.
Mutum ne mai bala'in riko da tsananin gaba do dai yanzu an sake girma amma dai yadda ya'ki jinin Hauwa haka ya'ki jinin mutuwarsa sunanta 'yar ta'adda a wurinsa yana rangwatawa ne kawai saboda Hajja ta nuna tsananta gaba da kiyayyar bashi da amfani tunda an riga an hadu babu yadda za a yi da juna.
To ita ga da niyyar da ta yi aure amma ga yadda kaddarar takasance
A lokacin kuwa ya tura mata da dubu dari biyar ya kuma kira wayarta tun bayan rabuwarsu wata biyar kenan suka gaisa 'kasa k'asa nake yin maganarta tana magana a hankali ya dubata da jiki sosai sannan ya ce ta duba ya tura mata sa'ko.
Ya mi'ko mini wayar wai tana son mu gaisa babu yadda na iya haka na kar'ba nasa a kunnena na ji maganarta a raunane kamar ma kuka take yi.
Zuciyata ta d'an karye kad'an amma ban bari ta gane ba muka gaisa sosai na yi mata ya jiki ta tambayi yaran gabad'aya har da k'aramarsu Mufida na ce duk nuna nan lafiya lau.
Jin ta yi shiru ya sanya na mik'a masa wayarsa na ji yana gaya mata idan da buk'atar wani taimakon gaggawa ta sanar dashi daga haka ya kashe wayarsa.
Ko da muka keb'e bai bai tashi zancan ba sabgoginsa kawai yake yi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa tun kafin mu zo nasan dalilin zuwan tunda bai gaya mini ba ni ma ban nemi jin karin bayani ba Hajja ta kira ni a waya ta gaya mini yana yi wa Kamalu gini amma bata gaya mini wane iri bane shin na gida ne ko kuwa na makaranta.
Sati daya muka yi a kano muka koma abuja cikin yaranmu da suke samun kulawa wurin masu aikin da a yanzu nake ganinsu kamar 'yan uwana saboda yadda sha'kuwarmu da su ta kara tsananta.
Babu wani sa'bani da ya sake giftawa tsakanina da shi tun bayan fitar Hauwa muka samu wani irin daidaito da kara kusanci ga juna gabad'aya hankali da tunaninnmu yana kan yaranmu mussaman ita wannan din da muka samu daga baya.
Ban ta'ba jin ya yi wata magana da ta danganci neman cikin gurbin da Hauwa ta bari ba abinda na lura da shi ma a yanzu ba wannan ne a gabansa ba amma ta fannin abinda ya danganci mu'amula ta aure babu wani abu da ya yi rauni muna shan soyayya launi-launi domin ni dashi gabad'aya mun 'ki bari kanmu ya yi murfi yadda koyaushe yake d'okantuwa da ni haka nima nake kasancewa da shi kamar wata sabuwa dalili ina kasancewa cikin gyara kaina ciki da waje yadda zai ji dad'i ya kuma yi alfahari dani tare da dakushe masa sha'awar duk wata 'ya mace.
MURFI
Bayan shekaru biyar abubuwa da yawa sun faru masu dadi da marasa dad'i mun yi rashin Hajja haka zalika mun yi rashin Dada mata uku da suka taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwarmu Gwaggo Hajja Dada duka sun amsa kiran Ubangiji suna masu tuba da tabbatar da ya'kini ga Allah.
Yadda kowa yake ha'kuri idan ya yi gagarimin rashi haka mu ma duka muka yi hakuri 'ya'ya da jikoki masu aiki da hadimai tare da abokanan arziki.
A cikin dai shekarun ne Kamalu ya taka mataki na mussaman fannin addini tauhidi tare da da'awa.
Yaro ya yi bazata to amma ba abin mamaki ba ne idan har an yi duba da irin kalubale mabambamta da aka riska tun daga farkon kuruciya har kawo wa yanzu da aka cimma manufa babu shakka addu'ar iyaye tana da tsananin tasiri akan yaransu ba ma su kad'ai takewa tasiri ba har da wad'anda ke abota da su.
Na ga zahiri domin ita addu'ar a yanzu na tabbatar da cewar itace take ri'ke da ni har na riski wannan lokacin cikin nutsuwa da hayyacina.
Gwani Kamaludden Aminu Salihi a yanzu yana da masters degree (gwani) bayan fafutukar da aka sha wajan neman ilimi littafan addini tun daga kan al'kur'ani mai girma babbbak'u farfaru haddace shi da kuma rubuce shi.
Idan muka zo kan kan litattafan addinin musulunci irinsu fi'kihu ahlari ishmawi iziya risala askari muwad'da malik muddawara kulasatunurulmubin, arba'una hadis, zadizzaujen.
Wad'annan littafan addini ne da duk wani mai neman ilimi fannin da'awa ya karance shi Gwani Kamalu ya zauna zaurukan malamai da yawa domin k'arin sani kafin malamansa su bashi izinin zama kan mumbari a katafariyar makarantarsa da uban rik'onsa ya gina da sunansa mai suna *Gwani Kamaludden tahafizul-kur'an* Ya k'ara da gina massalaci kusa da makarantar domin zaman tafsiri da warware wata mas'alar idan ta taso wadda ta shafi addinin musulunci a k'arshe kuma ya ce ya nemo aure gidan mutunci da tarbiya domin k'ara samun goyon baya da nutsuwar gudanar da al'amuransa.
To rasuwar Hajja ita ta gyara zazzafar gabar dake tsakanin Inna Uwani da Hajiya Saratu domin dai Inna Uwani kuka take yi sosai da Hajiya Saratu a ganinta itace take zuga Hajja ta'ki yafe musu ta zo ta sake zuwa wurin Hajja domin neman gafara da kuka da ro'ko ba a rabuwar arziki a tsakaninta da Hajiya Saratu domin cikin ikon Allah duk zuwan da za ta yi sai ta risketa a gidan su yi ta babu kyau babu dadi ita Hauwa na can babu wadatacciyar lafiya domin yawan hauhawar jininta ya sanya mata nakasa k'afarta daya ta lanjare da 'kyar take janta a gidan Naziru ma gabad'aya ta zama maririya domin babu wani abinda take iya aiwatarwa tunda babu lafiya kwanciyar aure wannan ba kasafai yake yi da ita ba saboda babu nutsuwar yin kullum cikin ciwo yau da lafiya gobe babu adalci d'aya da ya yi a lamarinta da ya cigaba da zama da ita a hakan bai saketa ba.
Ko saukar al'kur'ani da Khalil ya yi Inna Uwani ce kawai ta samu damar zuwa nan abujan tunda ran Hajjan aka yi wannan bada'kala domin kuwa da kuka ta bar gidan sakamakon irin k'yama da gudun da yaran Hauwa ke yi mata ga Hajiya Saratu ta hana ta motsi a lokacin ne Hajjan ta tsawatar mata tana gaya mata ko bayan ranta bata yarda da wannan matsanaciyar gaba ba babu yadda za a yi da juna tunda an hadu abinda ya riga ya faru sai a bar wa Allah tunda ya wuce yara kuma kada a kuskura a dasa musu kiyayyar uwarsu..
Bayan rasuwar Hajjan ne na ga sun d'an daidaita domin dai mutuwar ta ki'dima mutane da yawa.
Har ita Hajiya Saratu ta je can bauchin ta duba Hauwa data na bani labarin halin da take ciki sai da ruwan hawaye ya ciko idona lallai dan adam ba abin komai yake ba Hauwa ta had'u da jarrabawa da kuma ciwo mai tsanani wanda a halin yanzu maigidan ne ke hidima da maganinta mijinta kwabonsa bata ciwon kai ina ma ya ga kudin.
Gidansa dai babu yunwa zai kawo ko babu dadi Sadiya ta dafa ta sammata a kwano amma ita da yake Hajiya ce ta fi Hauwan kudi takan yi miyarta ta kaji ko ta namar rago duk ranar dai bai yi cefane Mai kyau ba ta tsakura ta ci ita da yaranta abinda ya kawo shi take bawa Hauwa tunda dai ita kacangal bata iya yi saboda babu isashshiyar lafiya kullum tana dakinta a kwance cikin zullumi da koke koke da wata kafurar nadamar da har ta mutu ba zata musulunta ba.
Zuciyar imani ce ke sanya Sadiya kulawa da ita saboda tana tuna wasu alherai da ta yi mata a lokacin da take da dama a shakarun baya.
Hajiya Saratu da kanta ta zo ta same ni kan cewa idan har Kamalu bai zai tsayar da matar aure ba to sun bashi Aslamiyya jikarta ce ta wurin d'anta na biyu Hafiza ce don kuma tasha wakiltar makarantarsu wurin gasar al'kur'ani k'asashen musulci.
Na ce mata ba ni ya kamata ta nema da maganar ba d'an uwanta za ta gayawa tunda dashi suke yi magana ta ce ta sanar da shi kuma ya yi murna sannan ya ce zai tuntubi yaron wannan ha'kkina ne dole a gaya mini.
Na ce tunda hakane sai dai kawai na yi fatan alheri da tabbatuwar al'amarin.
Dama Salim matarsa yanzu tsohon ciki ne da ita haihuwa ko yau ko gobe ya yi aure shekarar da ta wuce yar gidan abokinsu Alhaji Sulaiman mai suna Suhailat amma ba Hajiya azizaa ce ta haifeta ba matarsa ta biyu ce.
Nan gidansu ya gyara wani sashe ya zauna da matarsa amma karfin zamansa yana can legos kusan yanzu shi ya kar'bi ragamar zaman can din shi da Adamu, maigidan ma yakan je idan ta kama amma baya jimawa a can yake dawowa gida k'arfin zaman yanzu yana nan Abuja tunda akwai masu ri'ke masa wata ragamar a can legos din.