← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 252 OF 276

Sashe 252

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abinda ya faru kenan da shigarmu gidan Hauwa ni Hajja gaisuwa kawai ta ratsa a tsakani Inna Uwani ta dinga kuka tamkar wadda ta yi rashin jinji nan abu tana fad'in idan abin nan bai zai yiwu ba a rabu tunda akwai maslaha a sha'anin aure Ubangiji da ya umarci a yi shi ya hallata rabuwa (saki) domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tana kuka tuk'uru tare da jadadda Hajja Hauwa ce kadai ta rage mata a duniya a yanzu tana ji tana gani kuwa ba za ta bari ta yi asararta ba saboda bak'incin da kishiya take gumamata miji ma ya guma mata nasa.

Hajja dai shiru kawai ta yi jikinta a mace tana kallonta ita na kuka Hauwan ma na kuka irin mai ciwon nan.. ganin haka ya sanya na yun'kura na tashi jikina a sab'ule gwiwata duk ta sage saboda ganin wannan lamari bai yi mini dadi ko kad'an ba amma Allah ne shahidi idan har ina cutar Hauwa a zamantakewa to ina ro'kon Allah Ya saka mata.

Na ji maganarta tana fad'in." Dole ki tafi ki tafi Amina ke ma kin san abubuwan da kuke yi wa yarinyar nan ba ku kyautawa idan har tana da hakki a kan ki da shi mijin naku ta bar ku da Allah."
Tana kuka ita Hauwan ta ce." Ban ce miki Amina ta yi mini wani abu ba inna, ni kawai na gaji da zama da mutumin da bai san raunina ba bai kuma yarda ya haihu da ni ba sannan bai san ya rarrasheni ya tausaya mini idan ina cikin b'akinciki ba.

Wallahi da gaske nake Hajja na gaji yara Allah Ya raya su tunda dama ai ba hannuna suke ba."
Hajja ta dube ni a sanyaye ta ce." Zauna yadda muka zo tare haka za mu tafi tare ai ke ma ba bare ba ce."
Na koma na zauna din
Kamar yadda ta umarta.

Ta dube yar uwarta cikin nutsuwa ta furta." Tunda kun yanke shawara kan cewa rabuwar kuke buk'ata abu ne mai sau'ki ai Uwani dalili ni kaina lamarin nan ya ishe ni wallahi ba zan tantance wanene mai gaskiya ba a tsakaninsu Tajo ne ko ita Hauwa.

Amina kuwa ku daina sanyata a ciki babu abinda ya shafeta ban fad'i haka don ina goyon bayanta ba.

Ita da Hauwa duk daya suke bambanci kawai ita tana bin umarnina tana kuma yi mini biyayya bisa duk abinda na umarceta tana son abinda nake so wata'kila ba ku san da cewa asalin auranta da mijinta umarni ne daga gare ni ba gani daya rana d'aya da ni da ita mun roki Allah kuma ya amsa mana bata san ni ba, na nemi alfarma ta yi mini a lokacin da mata da yawa suka guji auransa saboda ceton ransu ita tace ta ji ta gani duk da tana da labarin abinda ya faru da shi a baya.

Wannan shine abinda ya dasa mini kaunarta cikin zuciyata kuma ban fifita ta a kan ki ba Hauwa na dai gaya miki bambancinku amma tunda kun yanke shawara a tsakaninku zan same shi domin gaya masa uzurinku sannan kuma ina so nasan abinda yake yi miki na take hakki ai dole ne shima a nuna masa kuskuransa tunda ni uwarsa ce kuma har yanzu yaro ne a wurina dole ya bi abinda nake so."
Littafin nan na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba
Cikin jan hancin da kame-kame ta fara magana." Abubuwan da yake mini ba za su lissafu ba Hajja dole a cikin aure nasan ana cin karo da matsaltsalu da yawa kuma dole a yi hakuri, amma ni tunda na faru a tare dashi ban ji dad'i irin yadda nake so ba duk wanda ya ba'kunce mu yasan zaman ha'kuri nake yi ya gaya mini ya kuma nuna a zahiri zama yake yi dani saboda yaran da muka haifa da kuma zumuci, duk haihuwar data ratsa tsakaninmu tsananin rabo ne yakan jima bai kwanta da ni a shimfida daya ba, ni zan ta bin sa domin neman hakkina wallahi bai ta'ba yi don dad'in ransa ba.

Ya karkata b'angare d'aya ya fifitata fiye da ni ya k'aunaci yaranta Y
yana biya mata dukkanin buk'atunta Hajja ya zan yi da rayuwata na samu ciki ya zube ya nuna bai damu ba alhalin da kyar na same shi tunda ba kwanciya muke a gado daya ba ya cigaba da abinda yake gabansa ba shi da damuwa tunda ya nuna ga da wadda ya fi buk'atar haihuwa da ita." Ta ja hanci hawaye na silalowa a saman kuncinta ta cigaba da cewa." Ni na gaya muku ba ta yi mini komai lefi nasa ne tunda ya kasa daidaita tsakani na da ita ya fifitata ni kuma yana nuna mini kamar akan dole yake zaune da ni."
Hajja ta tsira mata ido kawai tana kallonta.

Ni kuwa na shiga nazarin maganganunta.

Abinda ya kara tashin hankalinta zubewar cikinta tunda kowa ya san yadda ta jarbatu da haihuwa idan har gaskiya ne abinda ta fad'i a kansa to
bai kyauta ba wata'kila ita tana d'aya daga cikin jerin mata masu buk'ata shi kuma ba a jarrabe shi da ita ba.

Ga ciki ta samu tana murna tunda ta fad'i dama ba ta so na fita yawan yara a gidan to sai kuma ya zube shi mai cikin bai nuna damuwarsa ba, ga ni kuma ina haihuwar bibbiyu shine babban tashin hankalinta abubuwa da yawa suka taru a zuciyarta."
Na ji Hajja tana fad'in.

" Haihuwa ta Allah ce Hauwa itama Amina bibbiyun da take haifa ba ita ta bawa kanta ba rabo ne, kuma akwai gadonta a jininta.

Amma kuma idan har da gaske ne abinda ki ka fada lallai akwai buk'atar zama a tsakani domin ai ke ba baiwa ba ce mutum ce me zai sanya shi ya dinga take hakkinki a shimfida wannan cutarwa ne ki yi hakuri ki barwa Allah ikonsa kin ji ko, wad'annan da ki ka haifa uku ki yi ta yi musu addu'a Allah Ya raya miki su sai ki ga sun tara miki garke guda.

Wani ma yana can Allah bai ta'ba bashi haihuwar ba kuma haka zai koma ga mahallicinsa.

Lallai zan yi masa magana idan har ba zai gyara ba to sai ya baki takarda ba dalili ba ne wannan Allah cewa ya yi idan har ba za a yi adalci a tsakanin mata biyu uku hud'u ba to kada a yi domin gujewa sa'bawa Ubangiji."
Inna Uwani ta goge fuskarta tana fad'in.'' Ni kaina abin nan ya ishe ni wallahi na gaji da bata ha'kuri da danneta akan ta zauna.

Yanzu ga shi ta hadu da hawan jini saboda tarin damuwa."
Hajja ta ce.'' Uwani na ce miki abin zai zo da sauki ai, shi wanda yake da alhakin sakin a yau zan zauna da shi domin mu samu matsaya kada wannan ya dame ki."
Ta yi sakato da baki tana karyar da kai gwanin ban tausayi.

Ta yun'kura ta tashi a hankali tana gyara yafan mayafinta ta dube ni tana fad'in." Tashi mu tafi." Na tashi da sauri domin dama kamar akan 'kaya nake a zaune a wurin.

Ta dubi inna Uwani tana Fadin." Idan an yi Isha'i sai ki shigo domin jin ina aka kwana."
Da sauri ta ce." To shikkenan." Ta sake duban Hauwa a karon da ba zai lissafu ba ta ce." Ke Kuma ki kara hakuri kin san dai illar yawan tunani da damuwa ko tunda ga abinda ya haifar miki don haka ki cire duk wani zullumi da tunani da ba'kin kishi a ranki Hakan shi zai sanya ki samu zaman lafiya."
Daga haka sai ta kama hanyar fita na bi bayanta cikin rashin karsashi.

Muka isa gidana babu wanda ya yi magana. ban ta'ba ganin tsananin bacin rai a fuskarta ba sai yau damuwa gabad'aya duk ta dabaibayeta ga tarin shekaru don ma da kula sosai amma matsalar nan kadai ka iya tayar mata da ciwonta.

Na rasa da wane kalami zan rarrasheta domin kwantar mata da hankali saboda gabad'aya yanayinta ya canza da bakincikin abinda ya faru.

Na gyara mata fillo a masaukinta ta kwanta tare da mike kafarta na fita daga d'akin cikin mutuwar jiki da tunanin mugun kishin Hauwa a kaina shi zai halaka mata rayuwa kamar yadda hajjan ta fad'a domin kuwa duk mai hankali yasan tsananin kishi ne yake damunta da ganin k'yashi.

Ban san yadda ta kaya a tsakaninsu ba domin tunda na shiga d'akina ban fito falo ba ya dai kira ni a waya da ya dawo to nasan dole za su zauna zaman tattaunawa yara ma sai Mairo ce ta kawo mini su tunda wurin baba Tabawa na bar su.

Sai can wajan goma da arba'in na dare ya kira ni a waya lokacin nasan sun tashi.

Na leka domin dubata tana saman dadduma a zaune da cazbaha a hannunta ganin haka ya sanya na ja mata kofar kai tsaye saman nasa na nufa zuciyata na dokawa haka kawai rashin hakurinsu na nema ya d'agawa tsohuwa hankali.

Ya fito daga wanka yana sanya kaya a jikinsa kafin na zauna ya ce na kawo masa abinci ban ce komai ba na sake sauka kasan da zummar bin umarinsa.

Abinci ya ci ya koshi sosai ina kallonsa babu wata damuwa mai gigitarwa a tattare da shi ya kammala ya goge bakinsa da tissue ya ja gefe na sauka da tiran abincin kasa na dawo na same shi jingine jikin gado yana duba wayarsa.

Zamana bai sanya ya dube ni ba.

Abin nema yake yi ya shafe ni kenan tunda magana ma ta gagare shi.

Ban nemi lallai sai na ji halin da ake ciki ba tunda bai shafe ni ba idan shi ya gaya mini zan saurare shi ba ni da wata shawara da zan ba shi akai duk abinda ya yanke a tsakaninsu daidai ne.

Na daure zuciyata na kalle shi a nutse na ce." Ina tsammani tare za mu tafi da Hajja zuwa Kano Gwaggo fa jikinta babu dad'i tun lokacin haihuwar yaran nan take ta fama wallahi ya kamata na je dubata."
Ya yi shiru bai ce komai ba.
Chapter 252 · 0% Book details