← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 276

Sashe 126

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kenan wannan ya nuna kun sake bawa yaron lasisin ci gaba da aikata abinda yake yi dalili kun nuna masa akan daidai yake, ke da mijinki kun daure masa gindi saboda kun tara abin duniya kuna ganin kun fi karfin hukuma ko? to ku d'aukaka k'ara don Allah allura ce zata tono garma menene ba mu sa ni ba Maryam na fad'a din idan ta yi miki zafi ki kaini 'kara ko kisa tsinken tsire ki tsire ni!"
Na tashi tsaye da sauri
na tare ta tare da mayar da ita kan kujera na zaunar sai huci take yi tabbacin a fusace take kuma a shirye take da duk abinda zai faru.

Hayaniya ta fito da Baba Tabawa daga kicin tana fad'in." Mai yake faruwa ne don Allah ku yi aiki da hankali da girman shekarunku kada hayaniyarku ta d'auki hankalin yaranku k'ananu har su fahimci abinda yake faruwa, kun san dai yaro da ri'ke abu a zuciyarsa...

Littafin gudun aure na kudi ne, don Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Cikin numfasawa Hauwa ta koma ta zauna tana huci! ita kuma Momi ta yi 'kasa da kanta k'walla cike a kwarmin idonta.

Alamu sun nuna cewa ba ta iya fad'a na cacar baki ba koda fad'ansu ya yi tsayi da Hauwa ita za ta kaita kasa.

Har cikin zuciyata ban ji dad'in abinda ta yi mata ba duk da cewa duka su biyun ban san menene a cikin zuciyoyinsu ba don haka ba daidai ba ne abinda ta yi tsinka na k'asa da kai ma tozarci ne ballantana wanda yake sama da kai ashekaru.

Ni da ita duka haihuwa ce ta janyo mana domin kuwa da yara ba su had'a ba ina ganin babu wani dalili da zai sanya na yi sa'insa da ita akan namijin da ba shi da wani tabbas.

Tun farko itama Hauwan da ta d'auki shawarata abinda yake yi akan matarsa ba zai dameta ba tunda ta san tafi amfanarshi fiye da ita ko a wurin tarayya ta aure ne.

Kuma ita ce uwar mai sunan mahaifinsa Ibrahim Khalil, uwa uba kuma 'yar uwarsa ta jini.

Hauwa ba ta fi ni kishi ba wallahi kawai na fita ha'kuri da juriya ne dalilin gwagwarmayar da na yi a rayuwa ita ba ta yi irinta ba.

BabaTabawa ta koma kicin jikinta duk a sanyaye bayan cikin hikima irin ta manya ta yi mana nasiha aka ci sa'a kuma Hauwa bata k'alubalanceta ba.

Falon ya yi shiru bayan gushewar baba Tabawa daga wurin babu wanda ya sake magana.

Ita Momi din tunda ta sunkuyar da kanta kasa ba ta sake d'agowa ba tabbatacin ta ji ciwon irin tijarar da Hauwa ta yi mata.

'Dagowar da za ta yi kuwa sai ya yi daidai da kwaranyowar ruwan hawaye a dakalin fuskarta.

Ba ta yi yun'kurin gogewa ba sai ta kalleni ta fara magana cikin karaya da zullumi." Amina ni na haifi Salim amma wallahi ba na goyon bayansa akan irin abubuwan da yake aikatawa na rashin kyautatawa. sannan na sake jadadda miki babu yawuna ka haifi d'a ne kawai amma ba ka haifi halinsa b.....

Hauwa ta yi saurin cewa." Kuka ai yanzu ki ka soma in sha Allahu rabbi Hajiya kina
fama da gagararan d'anki da ki ka kasa sarrafawa ina ke ina iya yi wa yaran wasu tarbiya wallahi ki ji tsoron Allah da Annabi, ga shi dai da bakin ki kin fad'a cewa Salim baya jin maganar ki, sannan nan Nusaiba ta shigo har gida ta yi mana rashin kunya, ina tarbiya anan kina so ki lalata mana yaranmu ne, ko kuma kina so su yi koyi da abinda yaranki suke yi duk a had'u a yi mutuwar kasko gabad'aya ko ba haka ba ne."
Shiru ta yi ba ta ce mata komai ba.

Na dube Hauwa da ta kasa zaune a kan kujera sai zabura take yi kamar ta yi tsalle a gabanta ta rufe ta da duka.

Gyada kaina na yi ban ce komai ba na mayar da hankalina kanta domin sauraran abinda take cewa." Na nunawa Salim takaici da 'bacin raina na kuma gargade shi akan kada ya kuskura abu mafi muni ya sake faruwa irin haka.

Ina kwance cikin ciwo jiya na samu labarin doki-in-doka da ya shiga tsakaninsu.

Wannan shine abinda ya fi tayar mini da hankali na ce kina ina har hakan ta faru.

Ban haifi Kamalu da Yusi ba, amma yau zan gaya miki wani abu da nake ji game da yaran nan a zuciyata wallahi ina sonsu fiye da yadda ki ke tsammani.

Yadda nake jin yaranku gabad'aya a raina haka nake jin wanda na haifa.

Ina rokonki da Allah da annabi kada ki yanke kyakykyawar ala'kar dake tsakaninmu.

Kada ki yi yun'kurin datse k'akkarfan zumuncin da yake tsakanin Adamu da Yusuf domin kuwa d'azu Adam ya je mini cikin damuwa cewa kin tura yaran nan kano, ki yi hakuri yara su dawo mu cigaba da rayuwa cikin aminci na yi miki alkawari wani abu makamancin wannan ba zai sake faruwa ba.

Kuma in sha Allahu Salim zai shigo ya baki ha'kuri komai ya shige da izinin Allah."
Ta gama maganar tana sanya hannu domin share hawayen da yake ta tsiyaya a fuskarta.

A nutse na ce." Ki yi hakuri ki daina kuka akan wannan lamari Momi wallahi ban k'ullaceki ba, kuma ni har abada akan yara ba zan yi rigima dake ba, amma ina so ki sani ce wa muddin Kamalu da Salim na tare a Inuwa daya to sa'bani ba zai daina giftawa a tsakaninsu ba.

Abinda ba na fatan ya sake faruwa.

Ba wai ba ki isa ba ne, kin fi karfin komai a wurina domin ban mance alherinki ba, ki yi hakuri yara dai har abada sun bar nan in sha Allahu suna can hannun dangin Babansu sai dai su zo da ziyara. kuma ban isa na yanke zumuci da ala'ka ba tunda ai ba ni na had'a ba......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*85*
Babu wanda ya ce komai sakamakon saukowar maigidan daga sama ya canza kaya amma ga yanayin yadda fuskarsa ta ke a cude nasan duk ya ji maganganun da Kamalu yake furtawa.

Bai ce mana komai ba haka zalika bai kalli inda muke ba ya kama hanyar fita cike da tsananin b'acin rai a tare da shi.

Yusi da sauri shi ma ya bi bayansa ba tare da ya yi wa kowa sallama ba.

Hauwa ta ja tsaki tana fad'in." Haba ai ni yau kwanan farinciki zan yi wallahi, irin wannan mutanan rashin mutunci da tijara shine daidai da abinda ya kamata da su."
Muka yi shiru babu wanda ya tanka mata.

Ta dubi Kamalu da har yanzu yake huci yana numfarfashi.

A nutse ta ce." Kada ka wani damu Kamalu abinda ka yi shine daidai domin idan har da ni da uwarka za mu zauna mu zuba ido akan abin nan to wallahi tallahi babu wani mataki da uban rikonka zai d'auka.

Abinda ka aikata a yanzu shine ya tabbatar mini da cewa kai dan halak ne ka haifu kuma kana kishin kanka, sannan kuma ya nuna cewa Salim sharri ya yi maka baka aikata ba, kada ka sare ko ka tsorata don suna da kud'i wallahi ba za su yi nasara a kanka ba.

Idan har Salim da uwarsa sun ce za su bi kadin jinin da ka zubar masa ni zan biya su zan kuma shige maka gaba tsayuwa gaban alkali masifa yanzu aka fara wallahi."
Na jima ina kallonta tare da yin nazari a kan maganganunta.

Yadda ta d'aukaki lamarin take sake zuzuta shi shine abinda yake sanya ni tunani.

Ita da Momi din duka na kasa gane inda suka sa gaba.

Masifa yanzu aka fara.

Wannan maganar tata ita nake ta nanatawa a cikin raina.

Tabbas k'azafin da Salim ya yi wa Kamalu mai muni ne sosai, to amma ni ban shirya tsayuwa gaban alkali akan hakan ba.

Kamalu dai duk da ba a shedar mutumin yau ina da tabbacin bai aikata ba.

Ba ni son bala'in ya yi tsayi domin shaidan ya samu mafaka.

Tunda ni da yaro mun tauna tsakuwa shikkenan nasan duk daran dadewa gaskiya zata bayyana.

Ba zan tsaya da ita domin yin shari'a akan yara ba, ba kuma zan ce mata komai ba domin bata isa ba, mijinta da ya daure mata gindi shine daidai da ni.

Sai dai yadda Hauwa take zafafa lamarin da ko'karin sake rura wutar rikicin shine na kasa gane azancinta na yin hakan shin soyayya ce ko kuma da wata manufa a zuciyarta.

Ba ni so akan abinda ya shafe ni auranta ya samu tangard'a amma na lura ita ba wannan ne abinda ya dame ta ba.

Tunda har na riga na yanke hukunci na kuma gaya mata ya kamata ace itama ta sassauta saboda gudun afkuwar abinda zai sanyata ta shiga nadama tare da danasani.

Yusi ya sake dawowa a karo na biyu daga bakin kofa ya tsaya yana fad'in." Ka zo in ji Momi."
Hauwa ta kalle shi sama da kasa kafin ta ja tsaki ba ta ce dai komai ba.

Sai harara da ta ke wurga masa.

Ya sake maimaita maganarsa "Momi ta ce ka zo."
Ya ce." Ka je ka ce mata gani nan."
Har ya juya zai fita na ce." Yusi zo nan." Ya juyo yana kallona na ce." Zo."
ya zo ya durkusa kusa da ni.

Na ce."Ka za'bi Momi ko?" Ya yi shiru bai ce mini komai ba.
Chapter 126 · 0% Book details