← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 276

Sashe 148

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina jinsa yana ce wa." Ni da kayana a ce za a boye mini, to wane lungu da sa'ko ne ba ki kama kaina kin d'ora a wurin ba, da hannunki fa ki ke miko mini idan kin manta wannan kirjin naki cinyesu ne kawai ban yi na taune ba, kina ba ni ina sha fiye da yadda raina yake so."
Ban ce masa komai ba har na gama kintsa jikina yana ta sakin maganganu masu tsananin nauyi wanda na tabbatar da cewa wasu na aikata da sani na, wasu kuma ban san lokacin da na aikata ba domin kuwa bayan ni da shi sai Ubangiji da ya hallicemu ne kadai ya san irin ta'barewa da haukan da muke yi idan muna auratayya."
Na dube shi bayan na juyo da fuskata, gabad'aya yanayinsa ya canza duk ya shiririce idonsa sun risina sun kankance tare da wani irin yanayi.

Yana ta ko'karin dannewa amma abin ya gagara.

Koda na zauna a gefansa sai ya janyo ni da k'arfi jikinsa na karkwarwa ya fara fadin." Na zata zan iya dauriya Amina, mai zan samu ne, ina ta shirye-shiryen tafiya legos tunda na lura babu tsarki a tare da ke."
Na cire hannunsa da yake cikin rigita a nutse na furta." Ai ba ni da abinda zan iya baka a halin yanzu."
Ya mayar da hannunsa cikin rigar yana fad'in." Ke ce kuwa ki ke da abubuwan bayarwa my love dina."
Na yun'kura na tashi hannun nasa ya sa'bule ya fito daga cikin rigata shi ma ya tashi da sauri na matsa gefe can nesa da shi." Wallahi ba ni da abinda zan baka, ba za ka samu hadin kaina ba muddin ba ka daina had'a ni da iyayena ba, na ga ji da rashin adalcin nan da kake yi mini, ni ba baiwa ba ce, idan kai 'karata shine zai sanya na shiryu to lalacewa zan yi bari ma na gaya maka gaskiya."
Ya zuba mini ido da wani irin b'acin rai a saman fuskarsa ya furta." Haka ki ka ce ko?"
Na ce." 'Kwarai haka na ce, ni da kai, duka babu yaro karami, kamar yadda ba ka so ana tiririn kai ka 'kara wurin magabatanka ni ma haka, ka san halin Baban Saude haka siddin ya zo ya ci wa Hauwa mutunci ai ni ce mai laifi tunda ba ka yarda cikin zubewa ya yi ba, amma ita Hauwa ai taimako ta yi, mai ta yi maka ka saketa kana bin ta da mugun nufi."
Ya jima yana kallona na lura takaici da b'acin rai ne suka taru suka yi masa dabaibayi.

Na ce." Don haka wallahi ni ba baiwa ba ce.''
Yana gyada kansa ya furta." Zuwan da Baban Saude ya yi domin yi muku nasiha ya tashi a banza ko?"
Na ce." Ai kai ma ba jin nasihar kake yi ba, zalinci idan abin yi ka cigaba, ba zan jure ba wallahi."
Ya furta." Wane zalinci na yi miki ba ki da yunwa balle ishirwa ba ki da matsalar sutturar sanyawa, sannan idan kina da bukata ta d'abia ina kawar mini da ita shikkenan ba za ki yi mini lefi na nuna bacin raina ba."
Na ce." Ai na gaya maka ba da gangan cikin ya zube ba, mai yasa ba ka yarda ba har sai da ka kira Baban Saude.

Idan ni da kai girma bai sanya mun gyara matsala idan ta taso mana ba to mu cigaba da tafiya a haka ni ba zan gaji ba."
Ya shiru na wani lokaci kafin ya ce." Ni kuma na gaji zam
an lafiya nake nema, sannan saboda ba kwa tsoron Allah ke da Hauwa ku bud'e baki ku ce ina dukanku ba ku ji kunyar yi mini sharri ba Amina."
"Ai kaima ka fada ka mare ta, ni ma na gani ta ina muka yi maka sharri."
"To na ji, ke kin manta ta'addancin da ki ka yi mini ko?"
Ya fad'a yana tsare ni da Ido.

Shiru na yi tare da zum'bura baki
Ya ce." Ni me yasa ban kai k'ararki ba?" Yafad'a yana juyo da fuskata.

Na dube shi ina fad'in." Ai da sai ka gaya masa."
Ya girgiza kansa a hankali cikin sigar rarrashi ya furta." Idan ma kin kashe ni duk a cikin soyayya ce ni babu wanda zan gayawa, amma tsakaninki da Allah na taba dukanki?"
A dan sanyaye na ce." A a sai dai zagi.''
Cikin neman sulhu ya ce." Wannan ma tsautsayi ne da b'acin rai kuma kema kin rama ko kin manta?"
Na ce." Yaushe na zage ka?"
"Ranar da ki ka tura su Yusi kano ki ka ce uban waye ya ce Maryam ta ri'ke miki yara, kin zage ni kin zagi ubana zagin ya yi mini ciwo sosai wallahi."
'Kasa na yi da kaina ganin yadda ya yi kalar tausayi da nadama.

Amma duk da haka abinda yake yi din ba zai sanya na janye kudirina ba.

Domin mutum ne mayaudari wanda ya iya rarrashi da kalamai idan yana so ya cimma wata nasara."
Ya sake matsowa jikinsa sosai yana ta daga rigar dake jikina.

Ya ce.'' Ni yanzu kwanciyar hankali nake nema nafiso mu sasanta kafin ace na koma legos, mu shirya kanmu kin ji giwa komai ya wuce."
Baki na zum'bura na ce." To yanzu ya kake so ayi, ai dama ni ba ni da matsala indai za ka gyara ka dinga adalci ka daina abubuwan da kake yi."
"Na ma gyara tuntuni na kar'bi kuskurena, zan kiyaye." Yafad'a a rikice Yana rungomu kafadata.

Na janye jikina tare da cire hannunsa dake saman cinyata na ce." Shikkenan Allah Ya ba ka ikon yin adalci."
Sai ya yi kasa'ke yana kallona don yadda nake ture shi daga jikina Ina yin baya ya yi masa ciwo.

Muka zubawa juna ido ni dashi gabad'aya ya zama kalar a tausaya masa.

Mun jima a haka kafin ya gyad'a kansa
bai sake ce wa da ni komai ya tashi tare da kama hanya zai fita.

Cikin zuciya na ce.'' Shikkenan ka ji idan da dad'i, ita matar da ka ratayawa fulawar soyayya ta iya da kai kawai gabad'aya ni ban ma yarda da nadamarka ba....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima:
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*2k complete a telegram.

What'sapp group 1k*
*0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
*101*
Muka cigaba da tafiya a gidan babu annashuwa da jin dad'in da ma'aurata kan jiyar da junansu.

Ya sauko sosai ya yi tubis da shi domin salon horon da na d'auka ba karami ba ne.

Gashi har yanzu bai cewa Hauwa komai ba dangane da zamanta a gidan domin da ya mayar da auransu a k'alla zai samu jin sau'ki ta 'bangaranta.

Ya mayar da ita bai mayar da ita ba Allah ne masani, suna dai zaune a haka ita tana wasan 'buya dashi shi kuma yana nuna mata isa da iko irin na d'a namiji tabbas ko bai fad'a ba nasan jiranta yake ta kai kanta ita kuma girman kai ya hanata ta lallaba ta bashi ha'kuri.

Amma yadda yake ta kokarin ganin mun zauna lafiya ni da shi na tabbatar da cewar ya d'auki shawarwarin Baban Saude domin ya rage wasu abubuwan sosai da yake yi mussaman akan yaran.

Ba su dai dawo gidan ba, amma a sati sukan shigo sau uku ko hud'u mussaman ranar juma'a muna yini tare da su uwar rik'on na su ta had'o su da kayayyaki masu yawa wai su kawo mana.

Ban iya cewa su mayar mata ba domin ita Hauwa kallo ba su isheta ba, kusan ni nake diban turarukan ni ma kyautarsu nake yi sauran na ce Baba Tabawa ta yi amfani da su.

Ban ta'ba tambayarsa yaushe zai dawo mana da yaran gabad'aya ba, kawai na zuba masa Ido domin ganin iya gudun ruwansa
Yadda na ri'ke wuta nake watangaririya da rayuwarsa abin har mamaki yake ba ni.
Chapter 148 · 0% Book details