← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 276

Sashe 4

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay
*BOOK2
Hawaye masu d'umi suka kwaranyo mini a kumatu.

Sahura ta shigo ta same ni a haka, na kalleta sai zuciyata ta sake tsinkewa.

Hawayen suka tsananta zuba.

Ta zauna kusa da ni tare da ri'ke duk hannuwana biyu.

"Kawata d'an girman Allah ki gaya mini menene, ko wani abun ya yi miki da ki ka shiga, kin san shaidan ba abinda ba zai aikata ba.

Hancina na ja.

Hawaye gaja-gaja a kumatuna na ce." Sahura mutumin nan nema na ya yi da fasikanci wai na zama yarinyarsa, wallahi tallahi ban yi masa sharri ba.

Sahura dan Allah me ya gani a tare da ni wanda ya nuna masa ni 'yar iskace."
Jikinta ya yi kwatakes ta dinga kallona gabad'aya ta gaza yin magana tsabar mamaki da rud'ani.

Na sake yan majina a karo na biyu "Na fad'a masa idan har sai ya yi fasikanci da ni zai fito mana da to yara, ya sa a rataye su kawai."
"Kawata na yarda ba za ki yi masa sharri ba.

Na san halinki, duk kiyayyar da kike yi masa haka kawai ba za ki kirkiri abinda bai yi ba ki ce yayi, Amma don Allah maganar nan ki barta kada ki gayawa kowa, ni ma na yi miki al'kawari babu wanda zai ji.

Kin san idan kin fito kin fad'a wa duniya ba yarda za a yi ba, karshe ma ki jefa kanki a masifa, ki kyale shi da halinsa.

Tunda dai Allah Ya tsare ki shikkenan, amma zahiri na girgiza da jin wannan batu, wato Allah A zahiri fir'auna a zucci.

Kai amma mutumin nan ya
ba ni mamaki wallahi."
Hannu nasa na goge kumatuna.

Jiki a sanyaye na ce." Babu wanda zan gayawa ai, in sha Allahu sai Ubangiji Ya bi mini hakkina, na bar shi da Allah, idan halinsa zai bayyana kowa ya ga sani".

Sai yamma can Sahura ta tafi dan ko gidansu bata shiga ba saboda daf ake da kiran sallah magariba.

Ina idar da sallah Hamusu ya shigo, nan muka zauna muna tattauna maganar.

Yana gaya mini ai tun yana kasuwa ya samu labari.

Alhaji Tajo din da kansa ya sanar a shafinsa na fece book.

A lokacin 'yan jarida suka samu abin yayatawa amma inda gizo ke sa'kar ba duka yaran ya bada umarni saki ba, Kamalu ne kawai, hakan sai ya janyo cece-ku-ce a kafafan sadarwa.

Ni dashi muka yanke shawarar da muke ganin itace mafita a garemu baki daya.

Makarantar horo da ladabtarwa zamu aika dashi dake can k'aramar hukumar k'iru.

Dama gwaggwo ce abin ji, amma jin hukuncin Allah da muka gaya mata sai ta sake k'arfafa guiwar yin hakan.

Na gayawa Babanmu shima ya bada goyan baya tare da fatan alheri.
don haka ana sako yaron da kwana uku muka gama had'a masa komai yana kuka da komai Hamusu ya tasa k'eyarsa domin kai shi makaranta.

Cikin zuciyata na bi shi da fatan alheri da addu'ar Allah Yasa karshen fitinarsa kenan.

Ina kuma yi masa addu'a Allah Ya sa ya zama kangaran, mahaddacin al'kur'ani mai girma.
tun Yusi na kuka da damuwa har ya warware.

Saboda Ina gaya masa d'an'uwansa yana can makaranta zai zama babban malami, sannan ba zai yi almajiranci ba, sa'an nan kuma ba za a daure masa kafafu ba.

To
sai ya kwantar da hankalinsa domin yadda na lura babbar matsalarsa a ce Kamalu Yana bara, irin yadda ya ga wasu al'majiran ke yi.
****
Kwanaki suka shud'e aka fara lissafin wattani babu wata 'kwakkwarar magana daga 'bangaran Alhaji Muntari.

Har yanzu shi a zaman da ake yi na kira shi na bashi ha'kuri.

Gashi har na yi jini uku, na yi iddah bai ce komai ba Baba Sule yayi masifar har ya gaji.

Idan ya zo gidan ma ko gaisuwata baya amsawa.

Hankalina ya kwanta.

Ba ni da wata fargaba a yanzu. dama Kamalu ne to Alhamdullahi makarantar da aka kai shi muna samun labarin sauyin rayuwar da ya samu sosai daga bakin malaman.

Sai na cigaba da gudanar da harkokina kamar koyaushe na fitar da kudi masu yawa na sayo atamfofi masu tsada da shaddodi har da leces na tayar da jari na kaina.

Sai da na kammala din'kunan tukkuna na kira Ya Falmata a waya na gaya mata zan an aiko da kaya.

Ta ji dadin haka kuwa dama nemansu ake yi, mussaman wadda take take turawa a Abuja ta kirata a waya ya kai sau nawa.

Ko sati daya ba a yi ba, kayan suka kare Ya Falmata ta had'a mini kudina tsaf dubu dari takwas ta tura mini.

Tare da buk'atar wasu.

Na kira Hamusu kan maganarmu ta kwanaki ya nemo mini shago mai yalwa wanda ya kasance a bakin titi zan kama haya sannan ya samu m
ini k'wararrun teloli da suka iya d'inki na gida da na waje mussaman irinsu sinigal mali da nijar.

Samun telolin bai yi wahala ba, nan da nan aka same su dan har sun haura adadin dana buk'ata.

Shagon ne duk wanda za a samu sai a loko, ni kuma na fi son na bakin titi.

Sai ya cigaba da nema cikin ikon Allah aka samu amma yana hade da gida.

A titin kuntau.

Kuma maigidan ya ce ba zai bada hayar shagon kadai ba dole sai da gidan dubu dari uku a shekara.

Na je na duba wurin, al'karya ce ta jama'a, kuma unguwa ce ta masu hannu da shuni, Ina ganin za a samu alheri a wurin.

Na yi shawara da Babanmu ya amince.

Na kira anti Yagana ma na gaya mata ta yi mini fatan alheri.

Sai kawai na roki Allah sa'a, na biya kudin.

Karin farincikina ma shagon kato ne zan iya zuba kekuna sama da biyar a ciki.

Zuciyata ta fara raya mini wani abu, hakan ba haramun ba ne, sai dai illar dake ciki, da kuma fassarar da jama'a za su yi mini akai.

Allah Ya rufa mini asiri a yanzu na bawa miliyan biyar baya kuma neman kudin nake yi, ba a san abinda gobe zata haifar ba.

D'akin da nake bashi da yalwa ga zafin tsiya, Ina ganin zan komai gidan da shagona yake sai na samu 'yar tayin zama. hankalina zai fi kwanciyar da hakan.

Ina kallon duk abinda yake faruwa ba, bayan haka zan samu saukin zurga zurga tunda ba ni da abin hawa.

Wannan shawarar ita na gayawa Babanmu.

Ya jima yana dawurwura kafin ya amince.

Na ce zan tafi da Usaini.

Sannan zan nemi alfarma Sahura ta ba ni Yusura.

Da kawu Sule ya ji sai ya hau fada yana cewa na yi arziki zan guji gida na tafi uwa duniya na yi zaman kaina.

Allah ya ce Annabi ya ce, dole idan zan tafi na d'auki daya daga cikin yaransa mata.

Na ce hakan ba matsala ba ne Fiddau ta shirya kayanta sai mu tare gabad'aya.

Itama Sahura bata musanta mini ba, ta ba ni Yusura har tana cewa babanta ya ce ya bar mini har auranta.

Na yi dariya sosai ina fad'in Allah Ya ba ni ikon sauke nauyi.

Cikin ikon Allah komawata kuntau sai ta fashe mini.

Domin na nemi sa'a a wurin Allah, na kuma mika masa al'amura ya kuma dubi zuciyata.

Harkoki suka bud'e mini neman kudin nake yi haikan.

Bayan manyan dinkun nan da nake yi ana fitar mini dasu.

Har zannuwa Ina sayarwa.

Na sanya aka yi mini singbord mai d'auke da tambarin shagona A&A fashion designer wato (Amina Aminu kenan) a jikin bannar din hotona ne cikin ado da kwalliya irin na mutanan nijar da sinigal sun yi masifar kyau.

Wani irin jiki ne da ni mai d'aukar ado babu wanda zai ce na ta'ba aure balle yara biyu.

Singbord daya aka sanya shi a farkon titi.

Na biyu Kuma aka sanya shi a kusa da shagon.

Hakan sai ya k'ara haskaka lamarin.

Cikin unguwar da sauran dake makotaka da ita suka fara kawo mana aiki.

Ba na kwatanta yin hakan akan Fiddau da Yusura dalili iyayensu Amana suka ba ni.

Kuma 'yan mata ne, akwai mutanan da ba su da fahimta.

Hankalina bai kwanta ba sai da na tabbatar sun cigaba da karatunsu, boko da islamiyya duk makarantun kudi ne har Yusi.

Sune dai suke yi mini hidimar gida idan sun dawo, Usaini kuma yana tare da yaran shagona.

Ni kuma aikina tallata kasuwancina a kafafan sadarwa.

TikTok fece book Instagram Whasap da sauransu.

Sutturuna suka yawaita dalilin fashion din da nake nunawa a duniya bagraoud muke samu a cikin gidana mai kyau a yi mini hotona masu kyau cikin dinkuna kala kala na watsa a Media tare da lambobin wayarmu da location dinmu.

Hakan ya kar'bu mutuka gaya dalilin kyawun suffata.

Duk kayan da na sanya sai sun zauna mini.

Kafin wani lokaci na tara followers na ban mamaki.

Sai ya zamana 'yan film suka mayar da shago da gidana sansaninsu.

Jin haka hankalin Babanmu ya tashi ainun!

Takanas ya zo da sassafe ya rufe ni da fad'a irin wanda bai ta'ba yi mini irinsa ba.

"Amina kada ki ga na zuba miki Ido ki nemi ki zubar mini da mutunci a duniya.

Ina samun labarin duk irin abinda kike aikatawa.

Wato watsa hotonanki da kike yi media hakan bai wadatar ba har sai kin had'a guiwa da 'yan film me kike so ki zama a duniya, Ashe shine dalilin da ya sanya ki ka nemi da ki kebance ke kad'ai domin ki yi abinda ki ke so ko?
Chapter 4 · 0% Book details