Sashe 220
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ka kawo mini yarana na ri'ke a hannuna domin ba zan iya barin su a tare da ita ba za ta iya yi musu lahani ta kowace siga.
Idan ba za ka iya rabuwa da ni ba to bar ni anan din ni wata daula ba damuna ta yi ba.
Idan za ka shekara ba ka zo in da nake ba babu damuwa na sahale maka."
Ya cire gilashin idonsa ya sanya hankici ya goge ya mayar dashi idon nasa.
A d'an rikice ya sake cirewa ya goge kafin ya sake mayar dashi.
Na d'auke kaina a raina ina fad'in zautuwa yanzu ka fara yin ta ka wani binjimo babbar riga.
Gaskiya na karyawa Hauwa d'ankwali a wannan ga'bar da alama ta d'auki hanyar rama kashin da ya bata.
Na yarda Minal bata da lafiya amma haka kawai zuciyata ba ta amince mini da cewa da gaske ne ta suma ba
Na juya ina kallonsa a lokacin da ya kama hanyar fita kenan abujan ya nufa saboda an ce masa yarinya ta suma.
Aikuwa dai ga dukkanin alamu mutumin nan so yake yi ya yi mutuwar tsaye.
Kwana uku da tafiyarsa bai kira ni a waya ba ni ma ban kira shi ba ana hudun ne ya zo tare da yarinyar da akwatin kayanta.
Ta ma'kalkale ni tana dariya da shafa fuskata duk garin jikin nan nata sai da ya rairaye ta yi d'an wuya.
Ko da na gaishe shi sama-sama ya amsa ya bar wajen.
Na ri'ke hannunta muka haura saman a tare yana wanka da ya fito ya gan ni a zaune ya sake d'aure fuska ya d'auki basiline ya zauna can nesa da ni yana shafawa a jikinsa.
Yarinyar ta fara zagaye d'akin tana neman abin wasa.
Ni abinda yake yi ma dariya yake ba ni abinda ba zai iya ba.
Duk tsananin gabar sa ban san me ya sanya yanzu ta daina tasiri a kan kansa ba domin daga ya fara ma yake bari kwana daya biyu zuwa uku ya fara neman hanyar da za a shirya.
Na ce." Ina 'yan biyu na ga Minal ita kadai ai ba haka muka yi da kai ba."
Ya ce." Tunda kin haife ni Amina ai ya zame mini dole na bi umarininki kada na lalace ko?"
Na danne dariyar da nake ji tana yun'kuro mini na ce." Ban haife ka ba amma abinda yake a hakkina nake tambayarka ni 'yan biyu na ce ka kawo mini."
Ya furta." Wannan din da na kawo miki sai ki yi cilli da ita tunda ai ba gidan ubanta ba ne."
Na ce." Mu yi magana wadda take daidai kuma ta fahimta mu kuma cire son zuciya.
Ban ce ba zan ri'ke yarinyar nan ba tunda har ka kawo mini ita amma ba ni son tashin hankali daga kowane 'bangare.
Idan har da sanin uwarta ka daukota ta amince da hakan babu damuwa a wajena.
Amma ya zama dole a kawo mini yarana."
Ya ce." Wannan ne kuma ba ki isa ba.
Ba za ki dinga gindaya mini sharadai ba.
Hauwa ta da ba ta yanzu ba ce domin duk yadda ki ke tunanin tana 'kin ki na tabbatar da cewa ba zata zalinci yara ba, kuma sanin da ki ka yi mata ta canza sosai ta kuma kar'bi dukkanin kuskuranta."
Na ce." Babu ruwana wannan matsalarka ce kai da ita.
Ni dai Hauwa ko za ta had'iyi al'kur'ani don tsoron Allah da gaskiya ba zan yarda da ita ba domin ita din mutuniyar banza ce mara tsoron Allah."
Ya ce." Cin fuska ne ki dinga kiranta da irin wannan kalaman Amina kwanakin baya kin mare ta a fuska duka ta yi hakuri saboda tana jin maganata."
Na ce." Me yasa baka rama mata ba a lokacin ba, ai da ka sani kawai ka d'aukar mata fansa kuma yanzu ma ai bata 'baci ba ga ni zaune kusa dakai ka rama mata kawai......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700.....0542382124.
BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*148*
Share ni ya yi ya tafi ya je ya d'auko rigarsa jallabiya mai yankakken hannu ya sanya a jikinsa ya fesa turare sosai sannan ya sauka kasa ya bar ni da yarinyar a d'akin.
Na tashi tare da kama hannunta muka sauka baya falon k'asa da alama fita ya yi.
Kai tsaye kicin na nufa na d'ora sanwar dare gefe guda kuma kasan marata na d'an yi mini ciwo kadan da cijewar kafa gobe alhamis asibiti zan yi sammakon zuwa domin duba lafiyata da abinda yake cikina a auna abinda yake cikin domin tabbatar da lafiya yake kwance.
Duk inda na ajiye kafata nan yarinyar take ajiye tata tana yi mini hirar 'yan uwan nata biyu can kasan zuciyata kewarsu ta ishe ni haka kawai yanzu nake tsananin jininsu a cikin raina ba kuma na tsammanin zan iya bar wa Hauwa su wallahi sai dai duk rigimar da za mu yi muyi ta a shirye nake gabad'aya na gama dawowa daga rakiyar Hauwa.
Bayan sallah Isha'i ya shigo muna d'aki ni da Minal na bata wayata tana game ya buk'aci abinci ya kama hanya ya fita da jin haushi domin ya'ki sakin fuskarsa tun da ya dawo.
Na shirya masa abinda na dafa na hau saman da tire din a hannuna cikin jan kafa daya ta ri'ke mini cikin ya yi mini nauyi ainun.
Na same shi yana waya na ajiye tiran kusa da shi na juya zan fita ya dakatar da ni.
Na juyo ina kallonsa fuskata a had'e sai kuma ya ce" Je ki kawai."
Na kada kaina ba tare da nace komai ba na sauka yarinyar tana ta game cikin nishadi cikin zuciyata na ce ikon Allah kenan ban haifi yarinyar nan ba Allah Ya jarabbeta da kaunata haka zalika ni ma ina sonta sosai domin ba ta d'auko kamanin uwarta ba fuskar ta ubanta ce garin jikin ni kuma na washeta tunda uwar da uban duka sirira ne.
Ya kwana can shi kadai na kwana da Minal da safe na yi mata wanka na shirya ni ma na kintsa.
Ruwan shayi kawai na iya dafawa na soya 'kawai zalla na had'a mata tea din ta karya.
Ina yin nawa karin kummalon ne ya shigo ya shirya shi ma da alama fita zai yi da wuri a haka har yanzu babu nutsuwa da cikakkiyar walwala a tare dashi tana ganinsa ta fara fad'in." Baba ka ga." Tana nuna masa wayata dake ajiye game din dana kamo mata tana yi ban kashe ba.
Tana ta maimaita maganar "Baba ka gani."
Ya karaso ciki sosai ya kar'bi wayar yana dubawa ya d'an saki fuska yana cewa." Na gani Minal mu gaisa ko?''
Ta daga kanta sai ya mika hannu ya kamo nata yana fad'in." Haka ake cewa ina kwana."
Ta sake daga kanta tana fad'in." Baba ina kwana."
Ya amsa yana dariya wadda ban ga ya yi ta ba tunda ya shigo jiya.
Ya d'an tsira mini ido na wani lokaci kafin ya ce." Ba za ki gaishe ni ba?"
Na ajiye kofin shayin da yake hannuna na ce." Ina kwana?"
Ya amsa a tak'aice tare da tankwashe kafa a gabana.
Sai na yi kasa da kaina ban sake ce masa komai.
Ya furta." Had'a mini tea din ma nasha.
Ya janyo flat din dake gabana da soyayyan kwai fefe uku manya na d'auki kofi na tsiyaya masa ruwan shayin nasa madara kad'an da milo domin wasu lukutan ma ya fi shan tsura shima amma dai shi yana shan madarar amma kadan ba kamar Baban Saude da gabad'aya madarar ce ma ba ya sha.
Yana kurbar ruwan shayin yana kallona kamar wadda ya samu tibi can na ji yana fad'in." Naga duk kin tasa kin kara girma ina fatan lafiya." Ya fad'a yana duba yatsun hannuna da suma suka d'an yi kumburi duk irin na masu ciki.
Na ce." Lafiya lau in sha Allahu amma dai yanzu shirin da na yi asibiti zan je ina so su yi mini awo sannan kafata na ciwo amma dai hakan ba matsala ba ne in sha Allahu idan ciki ya yi nauyi ya shiga watanni shida zuwa bakwai akan ci karo da irin wad'annan matsaltsalun."
Ya gyad'a kansa yana cigaba da yi mini kallon kurulla kafin ya ajiye kofin hannunsa ya furta." Za mu je na kai ki asibitin da kaina idan ya so zan yi magana da magaji direban Hajja idan kin kammala sai ya zo ya d'auke ki ku je da Minal ku gaisa." A tak'aice na ce to shikkenan.
A mota yake gaya mini daga asibitin bunkure zai nufa domin dai gobe ne za a daura aure bayan an yi sallar Juma'a akwai zai d'auko yarinyar still su dawo asibitin a tare domin akwai likitan da ya yi magana da shi a sirrin ce zai yi mata (genotype) tunda shi dama tuntuni ya san matsayin jininsa.
Na ce." Wane irin a sirrin ce sai kace munafurci me yasa baka so a san za ka yi aure ka bugo kati kana d'ora shi a status dinka menene abin boyewa.
Ya furta." Ni yarinyar ce ba ni so a gani."
Na ce." Kasan abin kunya ne kenan ko?"
Ya yi shiru bai ce komai ba can kuma ya furta." Babu wata kunya fa akan yin koyi da annabin rahama ni dai a yadda nake garau Amina ba na shakkar zamantakewata da mu'amula ta aure da yarinya irin Hajara saboda nasan kaina zan kuma yi mata iyakacin bakin kokarina.
Kawai dai har yanzu abin ne bai kwanta mini a rai ba.
Maganar buga kati ai ba wani abu ba ne na bugawa bazawara ma balle budurwa."
Na yi shiru ina auna maganarsa.
Ni dai lokacin daurin aure na babu wani kati da ya buga tunda abin duka ya zo mana a bazata sai da aka d'aura tukkuna gidajen jaridu suka sani.
Yana nufin Hajiya Maryam ne.
Sai na share ban tanka masa ba duk
kuwa da cewa na ji zafin maganar da yake akan yarinya ya nuna budurwa ta fi bazawara kenan ita ya kamata ace an bugawa kati.