Sashe 171
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yatsansa makale da carbi mai lamba yana ta rarraba ido a kanmu yanayinsa gabad'aya kamar mai nazarin wani abu damuwa da tashin hankali sun gama bayyana a tattare dashi.
Ganin mun had'a ido dashi ya sanya ni janye nawa idon.
Ina jin wani abu na taso mini da tashin hankali.
Kawai zuciyata ta fara raya mini cewa ni ma haka zan fadi na mutu yarana su sake kasancewa cikin maraici.
Ya gurfana a gabana cikin kula da ladabi ya furta."Mama ina kwana ya muka ji da hakurin wannan rashi."
Na amsa da "Alhamdulillahi mun gode Allah."
Ya furta." Allah Ya jikan Momi Ya gafarta mata."
Gabad'aya muka amsa a falon.
Na dubi Hajja tare da fad'in." Yusi bai samu zuwa ba ne.......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.
Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.
To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.
Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.
Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.
Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.
To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.
Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.
Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.
In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.
Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.
Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.
Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.
Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.
Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.
Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*PAID BOOK 2K COMPLETE ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA 1K VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK*
*07084653262*
A tsanake ta ce." A a ai tare duk muke tafe tun a waje ya ce Garba ya ajiye shi yana can tare da Adamu."
Na gyada kaina ba tare da na sake cewa komai ba.
Baba Tabawa ta kawo tire uku masu girma cike da abinci na taimaka mata wurin zubawa kowa Hajja ta ce ." Hajiya Saratu tana tafe in sha Allahu mun yi waya da Alhaji Sa'idu shi da d'an uwansa Alhaji Dahiru sun ce za su yi kokarin samun jana'iza." 'Yan uwan mahaifin maigidan ne wanda a yanzu su kadai ne suka rage musu a family din.
Na gyada kaina a sanyaye na ce." Allah Ya kawo su lafiya.
Kai na jima ban shiga tashin hankali da nadamar rayuwa ba sai a rasuwar baiwar Allah nan.
Tunda gawar ta iso gabad'aya estate din namu ya cika da motoci jama'a daga kowace kusurwa abokanan maigidan dama wasu daga ciki abokan tsohon mijinta ne.
Cikin gidanta cike da 'yan uwanta da zuriarsu tare da abokanan arziki da yaranta masu yi mata hidima na shaguna
nta.
Ana ta koke koke masu dauriyar daga ciki kad'ane.
Babbar yarinyata Nusaiba sumanta biyu har yanzu ba ta gane wanda yake kanta ba.
Nabila kuma tana ta iskokai a wani d'aki da 'yan uwansu sun kulle-kulle kofa don kada ta fito daga inda muke a zaune muna jin ihunta.
Cikin masu yi wa Momi wankan gawa har da Baba Tabawa lallai na yaba k'warai da aniya wurin jajuecewarta da dauriyarta koda yake yadda take ba ni labari a gaban idonta mahaifiyarta ta rasu kuma itace ta wanke ta.
Wannan ya kara tabbatar mini da cewa Baba Tabawa tana daya daga cikin salihan matan da Ubangiji ya ce lallai yana jin kunyarsu a gidan duniya da lahira dalilin rashin haihuwa.
Ban tashi tabbatar da cewa d'an adam ba a bakin komai yake ba sai da aka gama had'a Maryam tsaf cikin likkafani a mike cikin makara ta zama 'yar mitsitsiya a tsakiyar makarar tsabar ciwo ya cinyata
ana ta lallabata sunanta gabad'aya ya shafe daga jiya zuwa yau din wasu na kiran ta da gawa wasu na kiranta da marigayiya.
Yaranta da mijinta tare da yan uwanta sun kewaye makarar yayin da masu aikinta mata da muke tare da su a gidan suke gefe sun cure kansu wuri d'aya sai shar'bar kuka suke yi.
Adamu dake tare da Yusi ya can gefe daya kuka yake yi sosai yana fad'in." Momi kin mutu da wa ki ka bar mu a duniya, ba mu da uwa ba mu da uba.
Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!.
Sambatun da yaron yake yi ya kidima ni sosai ya kuma ba ni tausayi ainun na yi saurin d'auke kaina daga kansu Yusi yana ta rirrike shi sun kasa zuwa gaban gawar ma gabad'aya.
Hajja da Gwaggo suka nufi bakin makarar.
Na yi na yi na ja kafata domin bin bayansu na kasa don wata irin juwa da Hajijiya nake ji idona na ganinsu garagara,
Bayan haka kuma gabad'aya a tsarge nake ga yanayin kallon da na ga wata mata da na ji suna kiranta da suna Yabi take yi mini irin na wulakanci da neman fitina.
Hawaye masu d'umi suka silalo kumatuna wanda ya yi daidai da lokacin da na yi hu'bbasa wurin sarrafa 'kafafuna amma suka doje ban san yadda aka yi ba kawai na ji ni a k'asa na zube a lokacin ne kuma naga kamar gilmawar wani abu daga sannan ban sake gane komai ba sai dana farka tukkuna na tabbatar da cewar suma na yi lokacin har an kaita makwancinta an dawo.
Anti Yagana sun iso tare da Inna Uwani.
Ban yi mamakin ganin yanayinsu ba domin akwai d'imuwa da tashin hankali na rasuwar da aka kwantsama.
Ko baka da ji'bi da mutum fad'in Annabi ne mutuwarsa dole ta nasheka balle wannan matar da alherinta kowa yake gani.
Hajja ta shigo d'akin da muke tana fad'in." To alhamdulillahi tunda ta tashi da ji da ganinta da kuma lafiya mun gode Allah Yagana taimaka mata sai mu koma can gidan nasu mu yi namu zaman domin nan din zaman zai zame mana fitina.
Gwaggo da fitowarta daga bandaki kenan d'aure da alwala ta ce." Ni ma shawarar da na yanke kenan hakan zai fi alheri."
Anti Yagana ta dube ni a d'an sanyaye kafin ta ce." Sannu ba dai kya jin komai a jikinki ko?"
Kaina na gyad'a mata a nutse na ce." Ashe kun zo?"
Ta ce." Mun zo mun tarar an d'auki gawar gidan a kacame ana ta hayaniya ke kuma gaki a sheme sai da likitanku ta zo ta dubaki fa dogon suma ki ka yi."
Shiru na yi ina nazarin maganarta kafin na ce." Anti Yagana mai ya faru ne?"
Ta'be bakinta ta yi ba ce mini komai ba.
Na daga kaina na kalli Hajja dake tsaye jikin bango rumgume da hannunta a k'irji nan take na karanci damuwa da b'acin rai a saman fuskata.
Ban sake wata magana ba na tashi zaune hijabi na da yake gefe anti Yagana ta miko mini na zura a jikina tana taimaka mini na yun'kura na tashi ta ri'ke ni.
Na ce." Ki cika ni zan iya tafiya da kafafuna.
Inna Uwani ta ce." Da dai kin bari ta rike ki jikin naki ai har yanzu bai gama daidaita ba.
Hajja da Gwaggo suka yi gaba.
Wani irin kallo dangin marigayiyar suke mini na tsana da kyama.
Anti Yagana ta juyar da kanta ba ta ce komai ba.
Ni ma ban ce musu komai ba na ji ita wannan matar mai suna Yabi tana fad'in." Kun kai ta kasa kun ji dad'i, sai ku jirayi hakki domin wallahi ba mu yafe muku ba, duk abinda za ki nuna a banza a wofi Maryam dai karshenta ya yi kyau ku kam in sha Allahu mutuwar wulakanci za ku yi."
Maganganunta ne suka dinga yi mini amsa kuwawa! a kunne gabana ya dinga bugawa da karfi da karfi.
Wannan babban kalubalen ban shirya tararsa ba a yanzu domin ba ni da hujjar da zan kare kaina Allah shine shahidi.
Muka fita tun daga haraba cike da jama'a har zuwa waje mutane cike cikin manya manyan rumfunan da aka kafa.
Kafafuna suka dinga hard'ewa gabad'aya sai na tsargu domin maganganun da matar nan ta yi sun sake dakusar da duk wani karsashi da kwarin gwiwata.
Shin wane irin kallo jama'a suke yi mini a yanzu dana fito cikinsu.
Cikin dubara na janyo saman hijabina na rufe fuskata dashi dama rike nake a hannun anti Yagana.
Ina jin sanda Hajja ta tsaya suna gaisawa da ire-iren abokanan Yallabai din na ce da anti Yagana ta yi sauri mu wuce domin ba ni da wani k'umaji da nutsuwar da zan iya tsayuwa a gaban jama'a domin kar'bar ta'azziya.
Muka yi gaba muka bar su ita da Gwaggo suna gaisawa.
K'uryar d'akina anti Yagana ta dangane da ni na zauna kan gado kamar wata sabuwar amarya na yaye hijabin da ya katange fuskata.
Muka had'a Ido nan take na rushe da kuka na ri'ke hannunta katamau!