← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 268 OF 276

Sashe 268

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuma mun gama magana da Baban Saude kan cewa zai ba ni yaransa biyu duk da acan suna sana'ar huluna da sayar da yaduka mabambamta mussaman na hijabai da ro'ko da magiya ya amince mini domin duk wad'anda suka nemi samun gurbin zama duk da cikin family dinmu suke Ya Falmata ta ce a a daya muka d'auka daga cikinsu Halifa karamin k'aninsu Banandi sai Abahuraira da kaninsa Saifullahi yaran Baban Saude daga can kano kuma gidanmu na ce idan Hamusu da Usaini za su taho sai Ashiru ya biyo su shima tunda shi Saminu suna tare da Yusi a shago daya wanda koyaushe yake sake bunkasa dalilin kokari da cigaban da suke kawo masa a zamanance.

Wannan yanayin nasa gabad'aya sai ya dakusar mini da karsashin jikina hidimar dai kawai nake yi amma gabad'aya bana yin ta cikin dadi dalili ko bai gaya mini cewar akwai matsala tsakaninsa da Hauwa ba dole na gane tunda ya fi sati daya yana kwana a gidana sau d'aya da na yi masa magana ya 'bata ransa yana ba ni amsa kamar ba ya so sai ban sake ce masa komai ba na zura masa ido amma dai yau na yi niyyar takureshi akan sanin abinda yake faruwa yanzu abinda na gama fahimta a game dashi Hauwa ce matsalarsa tunda zahiri da bad'ini Allah Ya riga ya gama yi masa komai
Ilai kuwa ita din ce domin dana matsananta masa da tambaya abinda yake zuciyarsa ya furta mini Kai tsaye Amina zan saki Hauwa.

Zahiri na ji fad'uwar gaba da tashin hankali lokacin da maganar ta fito daga bakinsa ban kuma yi mamaki ba domin tsananin tunani da nazarin da yake yi akan lamarin ne shin ya aikata ko kada ya aikata tsayin shekarun zamana da shi na fahimci mutum ne mai nisan tunani kuma bai fiye yanke hukunci cikin fushi ba yakan ta jujjuya lamari yana nazari a kansa kafin ya yi hukunci ga misali nan akan matarsa Hajiya Maryam da ta rasu kafin ya amince da abinda ake magana a kanta sai da aka kai ruwa rana har ya gani da idonsa ya kuma tabbatar.

Jikina ya shika sosai na zuba masa idanuwana shima ya zuba mini nasa ido babu annuri ko kad'an a saman fuskarsa ya cigaba da cewa rabuwata da yarinyar nan shine kwanciyar hankalinmu gabad'aya domin kuwa Hauwa ba ta shirya zama ta gyara mini gidana ba har ta ba ni nutsuwa da kwanciyar hankali irin wadda nake samu a wurinki.

Ni ba sakaran namiji ba ne don haka ban ga dalilin da zai sanya a ce wata mace na raba mini hankali ba.

Abu biyu suke ri'ke da Hauwa a hannuna a yanzu kuma su nake dubawa shiyasa duk abubuwan da take yi nake kawar da kaina a kanta ba wai tsoron rabuwa nake da ita ba kamar yadda take nuna hakan.

Ko yau na rabu da ita gobe ina iya auro wata a madadinta idan har ina da ra'ayin hakan don haka tunda kin nemi da lallai sai kin ji matsalata to wannan ce."
A kasalance na ce." Ko zan iya sanin dalili, ai dai ka san haka kawai ba a sakin mace sai da dalili, gaskiya ka yi hakuri abin kunya ne a tsakaninku dukkaninku kun girma fa."
Ya gyad'a kansa ." Dalili akan ki ne domin duk zargi da tashin hankalin da ta shiga ganin kasuwancinki tana ganin ni na kafa ki na ce mata a a ni ma cikin nema na gan ki muka yi aure kina neman ki, bata yarda ba ta kai kara wurin Hajja wai kamar ni Hauwa ke yawon kaini k'ara saboda ba ta da mutunci tana ganin na fifitaki ina kashe miki kudi ita na bata tsohon kamfani sai dai a canza mata da abinda na yi miki shin a cikinku ko akwai wadda ta sanya ni d'aukar dukiyata na baku, alheri ne kawaii na yi muku ganin tare duka aka nemi dukiyar daku tana ganin abinda na yi miki ya fi wanda na yi mata akan hakan kuwa lallai ranta zai b'aci don ban ga dalilin da zai sanya ta tsananta k'yashi a kan ki ba, kema Allah ne ya yi miki daidai gwargwado kuma kin nema ni hannu kawai nasa miki kuma sai daga karshe ko ba haka ba ne?"
Na gyad'a kaina ina fad'in." Hakane amma akan hakan ka ke cewa za ka saketa ai ba hujja ba ce wannan kuma abinda ta nema ka fi karfinsa don ta tsananta kishi da k'yashi a kaina babu lefi ko ka manta kishi ne a tsakaninmu kowa fa da irin zuciyarsa, wallahi ban ji komai ba amma don girman Allah in dai zan baka shawara ka d'auka to ka yi mata yadda take so tunda kana da iko ka daidaita tsakaninmu itama ka bude mata plazar sai ka kar'bi kamfanin ka kawai tunda dama wahalarsa yawa gareta."
Ya girgiza kansa." Idan na yi mata plaza sauran shops din na kwari market kuma wa zai yi mata? tana cewa ai duk ni na yi miki"
Yar dariya na yi kad'an na ce sai ka yi mata menene a ciki ai Allah Ya hore maka?"
Ya girgiza kansa a nutse ya furta." Babu wanda zai karya mini rantsuwa Giwa ai na ce ta bar shi a hannuna zan a cigaba da aiki da shi a madadinta kuma abinda take han'koro za ta samu rashin yarda ne kawai da ci da zucci.

Ba zan yi wata plaza ba yanzu wannan shine karshen magana."
"To kasan halinta da rashin yarda da kuma taurin kai kenan idan kai da kake matsayin jagora baka yi yun'kurin ganin ka nemo mafita ba lamarin zai lalace ai."
"Ai na nemi mafita tuntuni aiwatarwa zan yi kawai ko kin ga na yi miki kama da namijin da mace za ta juya ne Amina.

Wasu lukatan Kawai ina biye muku ne domin ba na son hayaniya wa za ta gayawa taurin kai ne ni da ita shege ka fasa."
D'akin ya d'auki shiru bayan ajiye maganarsa na sauke numfashi Ina dubansa na ce." Yanzu kasan yadda za a yi tunda abin ya zo da haka me yasa ba za ka kara mata kudi akan kamfanin ba."
Harara ya wurgo mini kafin ya ja tsaki yana fadin.

"Ba zan k'ara mata ko kwabo ba wallahi."
Rantsuwar da ya yi a karon farko sai jikina ya mutu ba wai bashi dashi ba ne bayarwa ne kawai ba zai yi ba Amma ni ina ganin idan har ya k'ara mata kudi akan kamfanin da take ganin darajarsa ba ta kai plazata ba zuciyarta zata yi sanyi ga shi kuma ya rantse da gaggawa.

Na ce." To ni zan k'ara mata amma a madadinka."
Ya dinga shillo mini harara kafin ya yun'kura ya tashi bai ce komai ba ya shige toilet yana tsaki.

Ni kuma a ganina ai ba abin jin haushi ba ne don zan bata kud'i ba ni son ya saketa ko kad'an wallahi domin abin ba zai yi mata kyau ba daraja dai da alfarmar tana a hannunsa ta yi hakuri ta barwa Allah ikonsa kamar yadda ya fadi yanzu Ubangiji ne ya yi mini wallahi ban ta'ba tunanin zan kai matakin da nake a yanzu ba.

Kwanaki biyu muna ta abu daya gabad'aya ma ya'ki ya saurare ni da shawarar da na kawo sai hanya hanya yake yi yana ta shirye-shiryen tafiya Legos abinsa ni kima ina ta damuwa ga ciwo ciwon da na fara cin karo da su na kasala da zazza'bi taruwar yawu a baki da yawan bacci ciki ne da ni na tabbatar domin ban ga al'adata ba rashin sukuni da abubuwan da suka kutso ya sanya bai lura da canje-canjen da na sake samu ba.

Cikin wannan yanayin muka bude shagunanmu da bisimillah abin sai godiya da sake godiya wurin Ubangiji mun samu alheri kwarai da gaske domin yanayin yadda aka s'aukaka farashi a karon farko ya sake janyo mana suna a duniya da costumer's mabambamta.

Daga cikin manema labarai ('yan jarida) har da ni Binta Umar Abbale na tafi da biro da takardata domin d'auko rahoto na samu abin rubutu a kai
Na shiga cikin mutane ina ta ra'be-ra'be duk na ki'dime hankalina ya kasu kashi -kashi shin rahoton zan d'auko ko kuwa kallon zan yi kaya na alfarma kamar za su bud'e ido jama'a kuwa ga su nan hamsha'kai suna ta parking din motocinsu
Allah sarki ashe ta hango ni a labe ina le'ken shagon supplements dinta da ya tumbatsa da ya kaya ni shine ya yi bala'in d'auke mini hankali na saki baki galala ina ta hango manyan supplements din da suke tumbatsar da mace da tayar mata da komad'ar jiki cikin zuciyata ina ta fad'in dama ina da kud'i zahiri da na sayi wanda zai dawo ni shamshakiyya kalar 'yan gayu irinta duk da yake supplements din kala kala ne amma dai ga dukkanin alamu duk abinda yake cikin wannan shamsh'akin shagon nata sahihi ne babu cutarwa. 08089965176 domin neman karin bayani Aikuwa ganina sai ta yafitoni da hannu da wannan fara'arta tata ta ce da ni na za'bi abinda nake so.

Na dinga washe bakina don saura kad'an na daka tsallen murna na ajiye 'yar zabirata a can wani waje inda wani mutum yake zaune da Loptop a gabansa amma ban iya ajiye biro da doguwar pepper din da take hannuna ba.
kai tsaye shagon na kutsa ina zagaye shi bakina ya ki rufuwa.

Wani kwando nai zurfi na ciko da supplements ina ayyanawa a raina Allah Ya sa kada ta ce sun yi yawa na mayar ni kaina nasan na so zuciya amma cikin ikon Allah ta kar'ba ta dudduba tana murmushi ta ce a zuba mini a leda.

Na yi ta godiya na kar'ba ina duba jikin ledar wadda ta kasance ta mussaman mai d'auke da logo da bayanai bambamta a jiki.

Daf da zan fita kawai na hangi wasu mata masu kumari sun k'oshi 'kwarai daka gani sun ci sun tayar da kai
suna ko'karin kutsa kansu shangon zannuwa.
Chapter 268 · 0% Book details