Sashe 6
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokaci guda bakina ya fara rawa, dan wani bala'in kwarjini suka yi mini......."A a yanzu dai bani dashi amma ina shirye shiryen y......"Ai ba a daura ba ko?"
Hajja ce ta katse ni."
Na ce." E ba a daura ba Hajiya amma an kusa."
Sai ta riko hannuna katamau!
" Don Allah ki auri Tajo kin ji 'yar nan, na yaba da hankalinki, kuma duk na ji irin addu'oin da ki ke yi akan neman miji nagari, ki sanya a ranki adduarki ta kar'bu shiyasa Allah ya hadamu anan, don Allah don Annabi ki taimakeni ki auri yaron nan kin ji ko."
Gwiwa ta dinga rawa kafafuna sukayi mugun sanyi jin yadda matar take ta hadani da girman Allah har jikinta na rawa.
Muryarta na wani irin karkarwa wai sai na amince tukkuna zata sakar mini hannu.
Hawaye suka kwace mini da rawar murya na ce." Hajiya ni ba budurwa ba ce bazawara ce, aurena biyu, ina da yara biyu, sannan ba a auran na taso a gaba ba, neman kudi nake yi duk domin iyaye da yarana, don Allah ki yi hakuri ku bar maganar nan."
Sai kawai itama ta fashe da kuka.
Tana ce wa." Ai taimako na ce ki yi, duk abinda kike buk'ata na rayuwa kin samu a wurin Tajo, ni na haifi abina wallahi bashi da matsala, lafiyarsa lau, kaddara ce kawai take d'awainiya dashi, amma in sha Allahu daka kanki komai ya zo karshe "
"Hajja wace irin rigima ce wannan, dan Allah ki sakar mata hannu, kada hankulan mutane ya dawo kanmu, dole sai an bi komai a hankali, idan Allah ya kaddara sai ki ga an yi amma ba wai yanzu a tursasata amincewa ba."
Gabad'aya muka dubeta a lokacin da take maganar ni ina can tunanin abubuwa masu yawa.
Mahaifiyarsa tana nan tana shaidarsa mutumin kirki ne, bata san manemin mata ba ne.
"Saratu haka kawai na ji yarinyar nan ta kwanta mini a raina, na tabbata addu'ar da na yi ce Allah ya kar'ba a take, ko kina so na mutu banga abinda Tajo zai haifa ba."
A sanyaye ta ce." Ina so mana Hajja, amma kamata ya yi a bi komai a hankali."
Duk maganar da suke yi hannuna yana cikin nata ta ri'ke kamatau! da kyar na furta." To shikkenan Hajiya zan yi shawara in sha Allahu, duk abinda muka tattauna da mahaifina sai na sanar daku."
Ta sassauta rikon da tayiwa hannuna Kin tabbata."
Kaina na d'aga mata tare da furta"In sha Allahu rabbi, na yi hakan ne domin ta cika ni ba wai don na amince da bukatartata ba.
Maganar da Hajiya Saratu take yi a waya itace ta d'auke mana hankali gabad'aya.
"Cikin dariya take fad'in." Ga mu nan a tare ai ta samu wata yarinya wai dole sai ta aureka tana nan ta ri'ke ta tamau don rigima, to kai Tajo ai ka yi mata kuma."
Da yake hands free ne muna jin muryarsa yana fad'in." Matar aure kuma a ina?"
Ta ce.
Anan muka had'u da ita, ni ma kuma na yaba gaskiya na yi maka sha'awarta."
" Ku ajiye maganar nan Saratu, kada ku kawo 'yar mutane ta rasa rayuwarta, na ha'kura da auren nan fa, ba ni ma sha'awarsa gabad'aya."
Abinda ya fad'a ya daga hankalin mahaifiyartasa ta kar'bi wayar ta fara yi masa fada akan me zai sa ya furta haka.
Ha'kuri ya dinga bata har ta sassauta.
Yana fad'in." Ina sa ran yau da daddare zan shigo garin sai na ga matar na amince, indai hakane burinki Hajja."
Ta juyo tana kallona." Kin ji shi ya amince ko, kema kin amince ko Amina?"
Shiru na yi ban iya furta komai ba, kawai Ina mamakin karfin hali, da rikici irin na tsufa.
Haka kawai daka ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaki.
Ni abinda ya fi d'aga mini hankali ma yadda duk matan da ya aura suke mutuwa.
Ta ya za a yi Ina ji Ina gani na kashe kaina, akan wane dalili, tabbas dana san taimakon da na yi mata haka zai janyo da na yi gaggawar barin wurin ban tsaya mayar da magana da su ba.
Babanmu na hango Yana zuwa wurin da muke tsaye.
Yana karasowa na ce." Hajja ga Babana nan tare muke da shi." Da sauri ta saki fuskarta.
Na ce." Baba wannan mahaifiyar Alhaji Tajo ce wannan dan kasuwar, ita kuma wannan 'yar'uwarsa ce."
Cike da girmawawa ya gaisheta ya d'ora da fad'in." Mun gode sosai da karamancin da akayi mana, Allah Ya saka da alheri, ai yaro ma tuni muka tura shi makaranta yana nan ya shiryu yana ta yi wa al'kur'ani hidima."
Ita dai murmushi take yi don bata gano akan abinda yake magana ba.
Hajiya Saratu ta ce." Kada dai ki ce kuna da alaka da yaron nan Kamalu wanda ake zargin sun yi masa b'arna a kamfaninsa wattanin baya"
Babanmu da sauri ya ce." E, itace mahaifiyarsa ai, yaranta biyu marayu ne ubansu ya rasu, sai Allah ya jarrabi babban da fitina ake ta fama dashi, amma dai yanzu alhamdulillahi."
Girgiza kai Hajjan ta yi ta ce." Lallai akwai shirin Allah a cikin al'amarin nan, shiyasa ya shirya haduwarmu a wuri d'aya, idan an jima Tajo din zai sauka, idan ya so sai ku zo masaukinmu ku same mu domin akwai muhimmiyar maganar da zan tattauna da ku."
Babanmu fuskarsa ta yalwata da fara'a, irin wanda na jima ban ga irinta ba, tun kafin ma ya ji akan abinda ake nemanmu, sai godiya yake yi.
Ni dai Ina tsaye sai kace dasashen itace babu abinda yake aiki a jikina sai zuciyata.
Domin babu irin sa'ke-sak'en da ba ta yi mini, wai shin me yake shirin faruwa da rayuwata ne?" Ba zan ce da na sani ban zo ba, amma hankali ya tashi ainun ganin yadda jikin Babanmu yake rawa, a hanyarmu ta zuwa masauki yana ta Addu'a Allah Ya sa alheri ne.
Farincikin da mahaifina ya shiga shi ya kara sagar mini da gwiwa na dinga tunanin hanyar da zan bi wurin ganin na yi wa al'amarin da yake shirin tunkaro ni tutsu.
Daf da magariba baba ya sake komawa massalaci domin yin sallah.
Ina kallonsa ban yi yun'kurin bin sa ba dalilin rashin karsashi da kwarin jiki.
Zuciyata babu irin sake-saken da ba ta yi mini na zuwana garin.
Tana raya mini dana san abinda zai faru kenan da ban zo ba.
Matar nan da gaske take nema take yi ta 'ka'kaba mini d'anta wanda babu shi kwata- kwata a tsagin rayuwata.
Bai yi mini ba, baya burgeni ko kad'an, kudinsa kuma babu su a gabana.
Ina so na samu namijin da Yayi daidai da ra'ayina, mai rufin asiri daidai gwargwado.
Wanda yake da ilimin zamantakewar rayuwa da fahimta kamar Yaya Aminu.
Amma me za a yi da irin auran su Alhaji Muntari da Tajo, a ganina babu ci-gaba sai dai koma baya.
Auran nutsuwa da kwanciyar hankali ya fiye mini auran sanannan mutumin da duniya ta suturtashi da arziki a zahiri, amma kuma a badi'ninsa mutumin banza ne.
Yadda ake masa kallo kamili babu wanda zan fito na gayawa abinda ya aikata mini ya yarda.
Shiyasa barin maganar a cikina ta fiye mini alfanu.
Yanzu dai babbar damuwata yadda zan sa'bule ba tare dana 'batawa Babanmu rai ba, uwa uba waccan matar da ta kwallafa rai a kan na auri d'anta.
Ringing din wayata ya katse mini tunani lamba ce sabuwa kuma special irin ta manyan mutane.
Zuciyata na harbawa na daga wayar da sallama a bakina.
Muryarta ta karad'e mini kunne.
'Yarinyar kirki Mamanki ce, ai ni na cewa Saratu ta sanya mini lambarki sai mu yi magana, za ku zo ko?"
Duk lokacin da matar za ta yi mini magana nakan rasa kuzari a tare da ni, uwa uba bakina ya kan yi mini nauyin furta mata maganar dana san zata bata mata rai.
Da kyar na iya furta." Baban namu Yana massalaci Hajiya."
"To kin ga Tajo din ma ya iso muna nan a tare ku kadai ake jira, ai shi ya amince ya ce ma ko gobe a daure sai a nemi albarkar ranar tunda Juma'a ce."
Gabana ya dinga duka!
Na shiga rawar baki da kyar dai na iya furta."Hajiya don Allah ki yi hakuri kada ki ce na yi miki gardama wallahi ban shirya aure yanzu ba, akwai muradaina da yawa da nake so na cika, kuma ko bayan haka ma mutumin nan ya fi karfina, ni din ba kowa ba ce, haka zalika mahaifina ma ba kowa ba ne a duniyar nan."
Murmushi ta yi a hankali ta ce." Yanzu nan Saratu ta gama yi mini bayani a kanki, mu ba mu kyamaceki ba Amina, me zai sanya ke ki kyamace mu, Tajo gashinan a zaune da bakinsa ya furta Yana sonki domin Shima ya yaba da dabi'unku, kada ki sanya wasu tunane tunane a ranki in sha Allahu alheri ne auran nan naku."
Bakina ya mutu na kasa cewa komai.
Ina dai jinta tana sake kashe mini jiki da nasihunta.Wasu hawaye masu d'umi suka fara tsiyaya a kumatuna .
Wai shin wace rayuwa ce take Shirin fuskanto ni.Tunda nake ban ta'ba rayawa zuciyata auran mutumin nan ba amma lokaci guda kaddara tana nema ta canza tunana.
Mota suka turo da ita aka d'aukemu ni da Babana.
Masaukin da suke mallakinsa ne saboda wasu alamomi dana gani a wurin.
Yawanci ma'aikatan hausawa ne suke yi musu hidima.
Yar uwa wannan littafin na kudi ne kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.
Hakki dai sunansa hakki komai 'kankantarsa mu kiyaye da hakkin junanmu.
Katafaran falo ne mai d'auke da kayan alatu na more rayuwa.
Duk wani abu na morewa da jin dadi akwai shi.
Sanyi da wani masifaffan kamshin da nakasa tantance turarene ko 'ya'yan itatuwa ya dinga surnanowa hancina.
Hotonsa dana mahaifiyarsa gasunan kala kala a manne a falo.
Akwai kuma wasu biyu da yake tare da sarkin garin wanda yake a yanzu.
Hakan ya kara tabbatar mini da cewa lallai Yana da Ido a garin saudia domin gidan ya yi kama dana shahararran balaraben da ya ci ya tayar ya tada a kai a kasar.