← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 276

Sashe 91

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanan Hauwa biyar da tarewa ya kira ni a waya, lokacin ina bandaki ina wanka, na ji ringing har sau biyu kwata kwata ban tsammaci shi din ba, domin kafin shigata bandakin na kira Anti Yagana a waya ba ta daga ba, sai nake tunanin ko itace ta kira.

Ina fitowa na dauki wayar ina dubawa wanda ya yi daidai da lokacin da ya sake kira na dan ji faduwar gaba kad'an dalili na san ba kasafai yake kar'bar uzuri idan ya kira waya ba a daga ba.

Cikin nutsuwa nasa a kunne kafin na ce komai a hasale ya furta." Kina ina ne ina ta kiran waya."
Na tausa harshena na ce." Wanka nake yi."
Tsaki ya ja wanda ya ta'ba mini zuciya sosai, tunda nake dashi bai ta'ba yi mini tsaki ba, sai yau don kawai ban daga waya ba, a ganina tsaki yana daya daga cikin nau'ika na wulakanta mutum, kuma wata'kila tana zaune a kusa dashi ya yi mini haka.

Raina ya 'baci sosai zafin zuciyata ya motsa na dinga ji kamar na kashe wayar ma domin ban san wane kalar wulakanci zai yi mini a gaba ba.

Ya ce." Hajja ta yi mini magana akan tafiyarku jibi na ce ni ba ki gaya mini ba, ban sani ba ko kina da wani mijin bayan ni kin gaya masa."
'Kafafuna ne suka dinga kyarma jin maganar da ta fito daga bakinsa sai na ji wani gumi ya yanke mini kamar ba daga wanka na fito ba.

Gabana na bugawa cikin kaduwa da furucinsa na ce" Ban gane abinda ka ke nufi?"
"Kin ji abinda na fad'a ai ba sai na maimaitamana ba, ba ni da wani mutuncin a wurinki, da ni da banza duk daya."
Na ce." Ka ga Baba, har yanzu ban fahimci inda maganarka ta dosa ba, in banda neman fitina kai ka ba ni kujerar nan ba tare dana roka ba, haka zalika kuma ka fini sanin yaushe ne tafiya, to me zai sanya haka kawai saboda kana jin haushinsa ka nemi daga mini hankali.

Me nayi maka?ka jima kana zargina saboda kawai ka aureni bazawara baka tauna magana motsi kad'an zan yi sai ka mayar da abin wata manufa, idan ka gaji da ni kana da dama a hannuna fa."
"Ki zage ni kin ji ko, ai fitsara da rashin kunya ba sabon abu ba ne a wajanki Amina, kowa yana shura ya gagara ta fannin alheri amma ke duk wanda zai bude bud'e baki aibunki zai fad'a.

Ina so ki sani wallahi tallahi ba zan juri wannan sakarcin ba, ba zai yiwu da mutuncina da k'imata a gari ki zubar mini da ita ba."
Na danne kukan da yake so ya kufce mini na ce." wani abun kuma aka ce maka na aikata? wannan cin mutuncin ya isa haka Baba, ko namiji ka kama ni dashi iyakacin abinda za ka yi mini kenan, idan ba ka sona yanzu don Allah kada mu 'batawa juna lokaci mu rabu cikin mutunci ba sai ka kayi mini 'kaharu ba."
Kashe wayar ya yi ba tare da ya sake ce mini komai ba.

Na ajiye tawa wayar a gefena tare da rufe fuskata da tafukan hannayena kuka mai karfin gaske ya k'wace mini.

Cikin rashin kuzari na dubi wayata da na ajiye lambar anti Yagana ce.

Sai zuciyata ta sake karyewa hawaye ya cigaba da zuba.

Cikin kuka na daya jin yanayin muryata ya sanya jikinta yin sanyi a hankali ta ce." Menene kuma?

Ina ce magana ta mutu tunda maigidanki da kansa ya fito ya wanke ki a idon jama'a, kukan kuma na menene?"
Na ce." Anti Yagana kisan mummuk'e yake yi mini wallahi na rasa gane inda ya dosa, ai kin ga dai ya fito ya nunawa duniya girma da matsayina, amma wallahi duk wannan k'aunar da kulawar a yanzu babu ita, a tsukin nan cikakkiyar gaisuwa bata wanzuwa a tsakaninmu abinda ya fi daga mini hankali yawan zargina da yake yi, motsi kad'an zai canza mini manufa, kin ga zargi a cikin aure haramun ne."
A sanyaye ta ce." Sai fa kin yi hakuri a wannan lukutan kin kawar da kai gefe guda, kin ki ji, kin ki gani, tunda yana da sabuwar amarya, ke ma kuma kishi yana damunki Amina, Ina ganin shine abinda ya hana ki zaman lafiya da mijinki."
"Wallahi anti Yagana ba wannan ba ne, nasan ina jin babu dadi a raina amma ya zan yi, bayan Hauwa zai iya auro wasu mu zauna, wulakancin da ya tsiro dashi ne ba zan iya jura ba."
"Amina ki yi hakuri na gaya miki, matsalarki ba ta kai wadda za ki tayar da hankalinki ba, mijinki yana sonki yayin da ya gama d'okin amarya komai zai sake shi, ke dai ki cigaba da kyautata masa kuma ki godewa Allah mahaifiyarsa tana k'aunarki to duk abinda za ki ga ni a wannan lokacin ki daure ba zai dawwama ba."
Shiru kawai na yi Ina jinta, na san ba don komai take kafe ni a gidan ba, sai dan gudun lissafin aure, yadda na san halinta hakan ta san nawa, ina da hakuri amma kuma duk ranar dana furje babu mai iya tankwarani, kuma idan na bar abu na bar shi kenan har abada.

Ta ce.

" Kina jina ko Amina." Na ce." Ina jinki Anti Yagana.

Sai ta cigaba da cewa." Akwai bikin da za a yi na yar gidan Babanmu Auwalu 'dan autan su Dada zai aurar da yaranshi uku maza biyu mace daya, shine Dada ta ce a sanar miki sabon watan da zamu shiga in sha Allahu."
Na ce." Zan gayawa maigidan, in sha Allah na san dai ba zai hana ba, dama kiran da na yi miki d'azu zan gaya miki za mu je umara ni da Hajja jibi in sha Allahu zamu tafi."
Ta ce." To kin ga kin samu dama sai ki tsananta da addu'a akan komai, dama kuma ita rayuwar duniya haka ta gada yau dad'i gobe kuka, ki godewa Allah kaddararki mai kyau ce."
Na ce." In sha Allah Anti Yagana a gaishe mini dasu Fadila da kyau.

Tunda na yi waya da Anti Yagana na ji sasaauci a cikin raina, na kuma yi kokarin danne abin a cikin zuciyata, domin na tabbatar da cewa Hajja ta fahimci damuwata ran kowa sai ya 'baci har shi maigidan.

Satinmu uku a saudiya ni da Hajja muka dawo.

Tun ina can hankalina yake kan Yusi domin kuwa zuciyata gabad'aya bata aminta da matar gidan ba.

Duk yadda nake zaton ganinsa a firgice sai kuma na ga akasin haka lafiya lau na same shi har da 'yar ki'ba ya kara.

Ko ban ce Allah Ya bi mini hakkina ba nasan zai bi mini domin na ci wuya wurin rubuta wannan labari yar uwata yi kokari ki sauke hakki muddin kina karanta mini littafi ba ki biya ba.

Nan na fahimci azancinta kishi da kisan mummuke akaina ne, amma bata ta'ba nunawa akan yaron ba, a wasu lukutan ma idan ya zo ya same mu a falo har jansa da wasa take yi shi ma da yake d'an gari ne anti ya kira kiranta.

Ranar da muka dawo na fahimci ya zama d'an dakinta sosai domin magana daya zai ce mini anti ta yi mini kaza ko ta ba ni abu kaza.

Ban tambaye shi maigidan ba, domin jiya da daddare kafin mu taso mun yi magana ta chart ya ce mini zamu dawo mu iske baya gida zai shiga Kano kuma zai kwana biyu.

Ban nuna damuwata ba domin ban sanya a raina cewa lallai sai ya yi murna da dawowata ba, abinda nake bashi kafin tafiyata yana da wadda take bashi a yau na kuwa tabbatar da cewa baya cikin bu'katuwa.

Dama tun kafin tafiyata na cirewa zuciyata da gangar jikina sha'awarsa shiyasa idan za mu had'u ban cika kallonshi ba, wanda a lokacin da muke shiri kallansa kadai kan iya jefa ni a wani yanayi balle hancina ya ji kamshin turaransa da wannan ma yana jan ra'ayina sosai.

Raina na cire a kansa ba wai don ba na jin sha'awar ba, tana motsa mini sa'i da lokaci na kan danne ne kawai tunda na kudire wani abu a raina.

Kwanansa biyu kamar yadda ya fad'a ya dawo.

Kadaran kadahan muka gaisa da juna kamar wasu abokanan gaba, amma na ji dadi da Hajja bata fahimci akwai wani abu a tsakanina dashi ba.

Yadda bai nemi ba haka ni ma ban neme shi ba duk da nasan dole ne girki ya dawo hannuna ranar kuma ni zan kwana dashi
Kwana biyuna suka tafi a banza Hauwa ta kar'bi nata .

Tsayin sati Hajja ta kara a gidan na mu kafin ta fara haramar tafiya gida, ban so tafiyarta ba amma ta kafe a cewarta dama ba ta yi mini alkawarin zama dindindin ba.

To har dai Hajja ta tattara kayanta ta koma kano gidanta na Danbatta ba fahimci komai ba dalili a tsukin kwanakin ba kasafai yake zama a gida ba da daddare kuma kafin ya shigo ya shige d'aki ta kwanta.

Yau saura kwana shiga bikin da anti Yagana ta gaya mini, kuma har ga Allah Ina son zuwa ko babu komai zan shiga cikin 'yan uwa na yi walwala ko zuciyata za ta yi sanyi.

Ba magana muke yi ba don na lura 'kebe kaina da na yi ya sosa masa zuciya sosai, ya kuma ji ciwon rashin zuwana dakinsa shiru kawai ya yi mini.

Na dinga tunanin hanyar da zan bi domin na gaya masa.

Rashin lafiya 'karya na 'kirkira, na kwanta yini guda ban fito ba.

Yusi ya dawo daga islamiyya ya gan ni a kwance ya fara tambayata sai na ce masa kaina ne yake ciwo.

Jikinsa sai ya yi sanyi ya zauna gefena yana yi mini sannu yana ta tattaba wuyana wai na tashi nasha magani, don ya kyaleni na ce masa nasha d'azu da rana .

Ya'ki ya matsa ko'ina ko massalaci bai je ba, tare muka yi magariba da Isha'i a d'aki.

Misalin takwas da rabi aka murda kofar d'akin aka shigo.

Hauwa ce cikin kwaliyya har yanzu dai tana cancarewarta irin na amare.

Mamaki sosai ya kama ni, na tashi zaune Ina kallonta.
Chapter 91 · 0% Book details