← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 206 OF 276

Sashe 206

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rashin yarda da maganarsa ta furta." Wallahi ban yarda ba ai dama can haka ka ke yi mini ka jima kana zalintata sai Allah Ya saka mini."
A gajarce ya ce." Ni ma Allah Ya saka mini."
Ta tashi tare da kama hanyar fita ya bi ta da kallo ko daya bai tausaya mata ba domin ji yake yi har yanzu bai gama goge takaicin da ta cusa masa ba a baya.

Da asubahi ban kai ga tashi daga dadduma ba ya shigo da jallabiya da carbi tabbacin daga massalaci ya fito.

Muka gaisa ya nemi gefan gadona ya zauna har da cire jallabiyar ya ajiye.

Na ninke dadduma na ajiyeta a wajenta na zauna ina kallonsa a nutse na ce." Kwana biyu da suka wuce mun yi waya da anti Yagana tana gaya mini Dada bata da lafiya don har kwanciya ta yi a asibiti."
Da alhini ya ce." Me ya same ta?"
Na ce." Ciwon wuya ta yi amma dai da sauki an sallamota daga asibiti ina son zuwa dubata."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Ban 'ki zuwan ba amma legos nake so ki shirya mu tafi cikin satin nan da zamu shiga."
Na ce." Da dai ka d'auke mini zuwa legos din nan tun da kaga a halin da nake ciki ya kamata na zauna waje d'aya na samu nutsuwa ku je da Hauwa kawai."
Ya d'an Harare ni kafin ya ce." Dake zan je Hajiya ba wani dadewa za mu yi ba in sha Allahu mu dawo cikin yaranmu mu je mu huta ni dake na wata d'aya sannan akwai ayyukan da nake so na gabatar a can din."
Shiru na yi ina kallonsa tare da raya abubuwa da yawa na yi masa maganar Hauwa yana hararata kuma bayan tare suka kwana nuna mini yake yi har yanzu ba su daidaita ba.

Ya ri'ke hannuna yana d'an janyo ni jikinsa yana cewa." Jiya me yasa ba ki zo ba?"
Na ce."Me yasa zan zo?

Don girman Allah ka daina wasa da tunaninmu yanzu don ka sasanta da Hauwa shine abin yi mini boye-boye na fi kowa farincikin hakan wallahi."
Ya fara ko'karin cire mini hijabin jikina yana fad'in." Ni na gaya miki haka Amina kada ki yi mini rigima a irin wannan lokacin da nake tsananin kewa da bukatarki kada ki yi abinda zai dakusar da farinciki da karsashina my love.."
Ya fara sumbatar sasssan jikina a mutukar dimauce yana yin wani irin numfashi bakina ya mutu murus domin abinda jikina yake marari ne ya samu da na yi yun'kurin yin magana da turjiya sai na ji bakina ya yi nauyi bayan sa'kkonin soyayyar da yake aika mini ta kowace ga'ba.

Bakinsa ma amayarwa yake yi tare da wata irin sheshsheka haka muka kasance cikin ru'kun'kumar juna zuciyata na ta tsalle ido a lumshe can kasan zuciyata ina ta kiran sunan Allah da ro'kon Allah wanzar da alheri akan abinda za mu yi Ubangiji maji ro'kon bayinsa wata iriyar rayuwa muka yi wadda ta ki'dimar da mu.

Kuzuri da nagarta da mazantaka abin sai godiyar Allah da sake jaddada addu'a ga Malam D'aha da zuri'arsa kamar yadda ya fad'a mun ga zahiri domin kuwa ni zan tabbatar da cewa karfinsa na d'a namiji ya ninka na baya kafin a yi masa d'aurin goro.

Muna gamawa ya dinga godiya ga Allah har sai da ya ba ni tausayi a d'akina ya tsarkake jikinsa yana fad'in." Amina zan iya mallakawa Malam D'aha rabin dukiyata domin wallahi ya taka muhimmiyar rawa ga rayuwata na riga na sare fa ban ta'ba tsammanin mazantaka zata dawo ba sai gani rass da ni ki gaya mini ya ki ka ji don Allah."
Ya fad'a yana kanne idonsa daya.

Ni ma cikin tsokana na ce." A wallahi ras da kai Baba gaskiya ka yi bajinta Allah Ya sakawa da Malam 'Daha da alheri ya cancanci komai daga wajenka
Ya riko ni yana fad'in." A hankali duk zan biya ki bashin da na ci miki ko?"
Cikin nuna ya yi kokari na ce." Haba ai tun jiya ka biya ni Allah Ya taimake ka, a ai sai da na ce alhamdulillahi."
Ya kuwa fashe da dariya yana sake rungume ni a jikinsa.

Na kudi ne littafin nan kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba.

To a haka na yi kwana biyu na muna morar juna da nishadi ranar da Hauwa ta kar'bi girki kuwa ya rasa gane inda ba dosa tunda na hau na gaishe da safe ban yadda mun sake had'uwa ba marigaba na yi na shige d'akina na kuma kulle kofata duk da nasan aikin banza na yi yana da mukkulin d'akin amma dai hakan zai fi mini kwanciyar hankali ya kwana shi kadai idan ma ba zai kwanta da ita ba.

Babu kalar rarrashin da bai yi mini ba ta waya na ce ba da ni ba wallahi duk yadda nake jin zafinta a raina ba zan yadda ya had'a kai da ni a zalinceta ba to ballantana ma yanzu da da ta sauko take neman shiri ba na jin haushinta amma fa na ki sakin jikina da ita.

A haka muka cigaba da rayuwar a gidan har ya ha'kura ma duk ranar girkinta baya nema na ban san dai ya suke 'karkewa ba tunda nakan dan ganta jefi jefi ta hau saman a ranakun da take da girkin ta kara ramewa kwarai da gaske ta zama silent ma kamar ba Hauwan da na sani ba mai neman fitina da son kin zaman lafiya.

Kuma har yanzu jiya I yau tsakaninta da 'ya'yanta sai dai ido idan ma ta kira su wajenta Minal dai ba ta zuwa Khalil ne koda zai je a cikin fargaba da shakku yake zuwa saboda ta saba dukansa."
"Hauwa Legos za mu tafi ni da matata ban hana ki zama ba tunda kina ganin za ki iya amma wallahi tallahi kada na ji kada na gani akan yarana da wanda ki ka haifa da wanda ma ba ki haifa ba lafiya lau za mu tafi mu bar basu da masu yi musu hidima duk abinda ya faru a gidan nan zan yi kuka dake kuma zan yi miki hukunci mai tsananin gaske."
Ta ce." Hukunci ya wuce wanda kake yi mini a yanzu.

Ni ina ruwana da yara kuma abinda ya dame ni daban me zan yi musu ai ni ba azzalima ba ce."
"Na dai gaya miki domin na san halinka ba ki da mutunci babu ruwanki da kowa."
Ta fashe da kuka tana fad'in." To na ji, yanzu sai ka gaya mini menene makomata ai ba maigadi ba ce ni.

Wane irin zalinci ne wannan kake yi mini 'kiri-'kiri an raba da ni da yarana suna k'yamatata ai duk tsiya ba za su canza ni ba."
Shiru ya yi mata.

Ta cigaba da cewa." Ka gaya mini menene matsayina gaskiya na gaji wallahi, Allah kuma yana ji yana gani."
Ya dube ta sosai tare da cewa." Na yi na yi na ga na ha'kura na yafe miki na kuma sanyawa zuciyata sonki da kaunarki amma kin san Allah babu waje a cikin zuciyata da farfajiyarta Amina ta shimfida mashinfidinta ta zauna daram da can Samira tana da waje amma yanzu Amina ta mayaye ko'ina ita kadai ce a ciki ba kuma na tsammanin har abada wata maccan za ta samu irin wannan sararin."
Ta dinga wani irin kuka mai tsuma zuciya da sosai rai wanda duk wanda ya ji sautinsa sai ya tausaya mata amma a wajensa ma damunsa take yi so yake ta tashi ta fita ta bar masa d'akinsa.

"Ni ba zan ta'ba yi maka irin wannan 'kiyayyar ba domin ko banza mun had'a jini kuma na haihu da kai yara uku duk irin cin fuskar da za ka yi mini da tozarcin da za ka yi mini ba zai dame ni ba, hakkina dai da yake rataye a wuyanka wallahi ba zan yafe maka ba, ka zalince ni kana k'untata mini kuma ba zaka sawwa'ke mini ba idan an yi duniya don manzon rahama ba zan sake nemanka ba."
Ya ce." Hakan ya fi miki Hajiya ai ban hana ki ba idan kina da kwanjin da za ki kwaci hakkin na ki bismillah ai ga ni a zaune."
Ta tashi jiki a sab'ule ta kama hanyar fita kamar zata mutu saboda b'akinciki.

Har ga Allah ba na jin dad'in fuskar gizagon da yake yi wa Hauwa gabad'aya duka kowa ya gane Hauwa bora ce a gidan zaman ha'kuri take yi masu aiki duk sun gane irin zaman da suke yi da ita da maigidan.

Abin ya dinga damuna a ganina ai shi ne namiji kuma jagora ce ya ci ace ya tsahirta da wannan tsatstsauran hukuncin da yake yi mata ta dahu lugub ta yi mugun laushi ta kuma tsunduma a cikin nadamar abinda da ta aikata.

Shine bai sani ba ko kuma na ce ya sani yana takewa amma mugun zunubi yake nannagawa kansa domin wannan fad'in Annabi Muhammadu S.a.w ne.

Wannan dalilin ya sanya ni ranar da za mu tafi Legos din da daddare na shiga d'akinta na sameta a zaune ita kadai kan gado ta kunna tivi amma gabad'aya hankalinta ma baya kanta kuka take yi tana waya ganin shigowata ta katse wayar tana share hawaye na yi kamar ban lura ba.

Na zauna gefenta muka gaisa na ce." Ya gaya miki Legos za mu tafi gobe ko?''
Ta ce." E, ai jiya mun d'an jima muna magana da shi akan tafiyar taku.".

Na d'an yi shiru Ina nazarin maganarta wadda na tabbatar da cewa 'karya ce kawai wai ita dole sai ta nuna mini suna shiri bayan komai a bayyane yake.
Chapter 206 · 0% Book details