← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 276

Sashe 97

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saboda haka ina yin wanka na shirya na fito falon na same su suna kallo har da Baba Tabawa na nemi kujera na zauna hankali na saman ina tunanin ko ya sauko ko wane hali yake ciki.

Yusura ta kawo mini abinda suka yi na karin kummalo na kasa cin komai saboda bakina har yanzu babu d'aki.

Baba Tabawa ta d'umama mini ragowar towon jiya bashi dai da yawa tunda Hajja ta tafi da wani amma ya isheni kuma ni kaina na yi mamakin yadda na ci sosai a lokacin na ji karfin jikina ya k'aru...

Cikin wani yanayi na tambayi anti Yagana maigidan ya sauko tunda tun safe suna falon ta ce mini ya sauko har sun gaisa ya fita amma bai jima ba ya sake hawa saman bai kara saukowa ba kuma.

A gogon da yake falon na duba sha daya da rabi domin kada ta fahimci akwai 'baraka ya sanya na tashi ina fad'in bari na hau mu gaisa.

Kai tsaye na nufi benen da zullumi mai yawa a kirjina.

Kofar d'akin kawai na tura ta bude bai murza mukkuli ba, Yana zaune a gefan gado ya shirya sosai cikin milk din shadda tazarce da aiki mai kyau a gaban rigar hularsa tana ajiye a gefe amma as'usul gilashinsa na ka'ida yana idonsa.

Magana yake yi a waya a lokacin da na shiga d'akin na samu wuri gefansa na zauna amma gabad'aya na gagara kallonsa saboda tsananin yadda nake cikin damuwa.

Jin yana ambaton sunan Maryam ya sanya ni shiga tunani daga bisani Kuma na gane da Hajiya Maryam suke yin magana matar abokinsa da ya rasu kwanaki.

Sun jima suna tattauna abinda ya danganci mamacin yanayin maganganunsu ya tabbatar mini da cewa suna tattauna yadda za a raba abinda ya bari tunda mahaifiyarsa ta na raye kuma yana da 'yan uwa.

Dole Mamansa ta gaje shi koda kuwa 'yan uwansa ba su gaje shi ba dalili akwai maza biyu a cikin yaranshi.

Bayan sun yi sallama ya dube ni babu yabo babu fallasa amma bai ce komai ba sai ya cigaba da latsa wayarsa yasa a kunnansa ina dai zaune Ina jin shi Hauwa ya kira a wayar cikin kulawa na ji suna magana don ba na jin abinda take cewa tunda kamar ya yi kasa da murya ne don shi ma idan ta fad'i magana sai ya sake tambayarta abinda ta ce saboda maganarta can kasa take fita.

Sai na juyar da kaina gefe ganin kamar ba ya so na ji maganar da suke yi na ji yana gaya mata daga nan din kai tsaye bauchin zai taho zuwa yamma ta tsammaci zuwansa tunda tafiyar mota zai yi.

Jikina ya d'an yi sanyi Jin yadda yake lalla'bata da rarrashi har da kalamai irin na tausayawa da sadaukarwa.

Sai na tsargu da jin abinda yake yi wanda na tabbatar da cewa wanzuwata a wurin ya kawo hakan.

Na ji haushi sosai amma sai na danne domin kuwa a yanzu fushi ba nawa ba ne dalilin abinda na tabbatar da cewa ni ce mafi rinyen lefi dole a wannan ga'bar ko ban fito na gaya masa na aikata ba na nemi hanyar shiri da kuma ko'karin kwantar da matsalar don gudun fasuwar maganar.

Ya ajiye wayar a kusa dashi bayan sun kammala ya d'auki agogonshi dake saman drowar yana daurawa bai ce mini komai ba.

Na daure na ce." Ina kwana Baba?"
Hankalinsa na kan abinda yake yi ya amsa da "lafiya ya gajiya." Sai na yi shiru ina dan satar kallonshi a fakaice.

Sukairaju ya dan buga kofar kafin ya bashi umarnin shigowa ya turo a hankali cikin ladabi ya tsaya daga can nesa yana fad'in." Sir ka kammala ne?"
Ya mike tsaye da hularsa a hannunsa yana gyarawa ya ce." E, na kammala zo ka d'auki wad'annan." Ya fad'a yana nuna masa Loptop dinsa dake ajiye da 'yar jakarshi."
Da sauri ya yi abinda aka sanya shi ya bude kofar ya fita daga d'akin.

Yana ko'karin sanya hular a saman kan sa ya ce." Ni zan tafi Amina, Amma kafin nan zan je Bauchi wurin Hauwa domin dubata ina fatan ba ki da matsala ko?''
Na mike tsaye da rashin karsashi na ce." Ba ni da matsala Baba amma ina so mu yi magana dangane da abin nan da ya furu na ga kamar ba ka yarda da kaddara ba don Allah kada ka tafi da 'kullacina a cikin ranka."
Ya dube ni sosai wanda tun shigowata d'akin bai yi mini irinsa ba.

"Kin aikata hasashen Dr Iliyasu ko ba ki aikata ba, wannan amsar kawai nake so na ji daga gare ki."
Shiru na yi ina kallonsa shi ma yana kallona ido cikin ido.

Mun d'an jima a haka kafin daga bisani na janye nawa idon daga cikin nasa zuciyata na dan harbawa ko alama ban hangi sasaauci a cikin idanuwansa ba.

"Shirunki da yanayin yadda alamun rashin gaskiya suka bayyana a tattare dake ya bayyana mini ce wa." Dr Iliyas ba karya ya yi miki ba saboda haka ni kawai sai dai na ce na barki da Allah."
Daga haka sai ya kama hanyar fita daga d'akin.

Da saurin gaske na cimmasa idona cike da hawaye masu radad'i na furta." Maganar bari da Allah ba adalci ba ne, ka yi duk hukuncin da kake ganin za ka yi mini tunda ka'ki kar'bar kaddara, amma kwata kwata ka daina had'ani da Allah
"Shi kadai ne zai yi mini maganinki tunda ai kin gagara Amina kin nunawa duniya cewa baki da na gaba dake kin fi 'karfin kowa ciki har da mahaifinki ni dai muddin ina da hakki akanki to fa ba zan daina cewa Allah Ya saka mini ba."
Ya sanya hannu zai bude kofar domin fita na sake tare hanyar a karo na biyu cikin jarumta na ce." Ubangiji ba mutum ba ne kamar kowa kuma akan yi masa lefi a tuba ya yafe duk sharri da bala'in da kake nema dashi da izinin Allah ba zai same ni ba domin kuwa wanda ya hallice ni ya fi ni sanin menene a zuciyata Ina ce dai idan na gaya maka gaskiya shikkenan ai ikon hukunci ko azabtarwa ko d'aukar rai duka ba a hannunka suke ba.

Na yi kuskure tabbas a lokacin da na tabbatar da cikin a jikina na yi kokarin fitar dashi kamar yadda Dr Iliyas din ya gaya maka.

Dana fahimci bai zube ba sai na ha'kura kawai na barwa Allah kuma na ro'ke shi gafara a sa'in da na kuskure masa kuma ina da tabbacin ya gafarta mini, abinda zan iya gaya maka kenan domin a duniyar nan babu wanda baya kuskure Ina me baka ha'kuri hakan ba zata sake faruwa ba."
Ya jima yana kallona da yanayi na mamaki da al'ajabi ni kuwa ban ji komai ba domin kuwa na lura rufe maganar da nake yi bashi da wani amfani gwara kawai na sanar da shi gaskiyar lamari tunda ya fi ni sanin hujjata ta yin hakan.

"Hakan ba zata sake faruwa ba." Wannan maganar ya fad'a kafin a gaggauce ya bud'e kofar d'akin ya fice da saurin gaske.

Na jima ina nazarin maganar da ya furta sai na shiga zullumi da tunanin domin ya yi ta ne a d'ukunkune karshen dai hukunci shine saki a shirye nake da kar'bar gakan daga wajensa.

Da yamma muna zaune a falo anti Yagana suka yi waya da Babanmu nan take sanar dashi kwana biyu ni ce ban ji dadi ba shine dalilin da ya sanya ba mu sake zuwa ba tun ranar da aka sallameshi daga asibiti.

Na ce mata ta gaya masa na ji sau'ki don zai iya tashin hankalinsa jin ba ni da lafiya
Duk da ta gaya masa haka kuwa washe garin ranar sai da suka zo duba ni tare da Baba Sule sun jima a gidan muna tattauna sha'anin Hadiza domin kuwa kowa ya riga ya mik'a wuya don a zaman kutu na farko da aka yi ba a hangi sasaauci a tare da alkalin ba.

Yanzu tana can gidan kaso kafin shari'ar ta kammalu a yanke mata hukunci.

Bayan sun tafi da kad'an sai ga Gwaggo Hamusu ya kawota to ita tare muka yini har dare sai bayan Isha'i, tukkuna ya taso daga shago ya zo ya d'auketa a babur ya kai ta gida.

Sai da na warware sosai sannan na gayawa Sahura abinda ya faru da ni amma ban gaya mata cewa ni ce sila ba.

Ta jajanta mini sosai tana fad'in Allah bai yi rayayyu ba ne itama haka tasha wannan wahalar lokacin da nata tagwayen suka zube ta ce mini za ta zo ta duba ni ranar da babu aiki.
****
To tafiya ta mik'a sosai don yau sati uku kenan da abinda ya faru amma tsakanina da maigidan muguwar gaba ce ta 'kullu.

A zahiri shi ya d'auki lamarin da zafi na sani kowaye aka yi wa haka ba zai ji dad'i ba amma ya kamata ace ya yi hakuri ya kar'bi tubana tunda na gane abinda na yi ba daidai ba ne.

Na kira shi ya kai sau bakwai tun bayan tafiyarsa na tura text amma daga karshe ma sai ya sanya ni a black list idan na kira duka layinkansa busy.

Ban damu ba da farko saboda a ganina duk fushin da zai yi na dan wani lokaci ne zai ha'kura ya sauko ya kar'bi tubana ni kuma na kiyaye a gabana.

Na dai ji dad'i sosai da ya rufe maganar bai gayawa kowa ba dama kuma kusan haka halinshi yake yana da zurfin ciki mussaman akan mas'ala irin wannan.

Littafin nan na kudi ne kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

Duk da damuwar da ta fara yi mini 'kawanya ban yarda anti Yagana ta fahimci wani abu ba har dai ta tattara ta tafi bayan an yi zaman kotu daya da ita inda ake tsammanin zama na gaba za a yanke hukunci na karshe.
Chapter 97 · 0% Book details