← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 276

Sashe 155

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ko dai Shima neman auran yake yi ne ganin ba a tambaye shi ba ya fallasa asirin zuciyarsa.

Wata zuciyar ta ce mini a a hankalinsa fa yana kan matarsa ba ma shi da nutsuwar duba wata mace da sunan aure matarsa da yake tsananin so bata da lafiya.

Anya wannan hasashen na zuciyata ya yi daidai kuwa.

Na ji maganarta a tsakiyar kunnena tana fad'in.

" Amina za mu gudu kuma ba ki ba ni lambar wayarki ba.

Da sauri na dube ta sai na ganta a tsaye tana gyara jakarta dake rataye a kafadarta.

Na mike tsaye da sauri ina fad'in." Har tafiyar ta tashi kenan, to mun gode sosai Ubangiji Allah Ya ba ku ladan ziyara da dubiya." Ta amsa da Amin tana miko mini wayarta.

Na karba na sanya mata lambata ba don raina ya so ba dalili na fahimci tana da surutu idan ba haka ba mai zai sanya daga zuwanta babu wanda ya tambayeta ta fara zuba.

Gabad'aya ma ni sai na ji zuwanta bai yi mini dadi ba na farko labarin da ta ba ni akan Momi ba wai na k'aryatata ko na gazgatata ba, nasan hakan na iya faruwa abin ya tsaye mini a rai ainun! sai kuma wannan wasan da ya kasance wanda suke daukarsa kamar barkwanci ni kuma abin ya d'an sosa mini rai wata'kila da gaske shima neman auran yake yi kuma budurwa tunda gashi abokinsa yana fad'a mutum da kudinsa kuma iyayen yara yanzu sun fi so su bawa mai aure yaransu a ganinsu za a fi kula da su.

Iyakacin rakiyar da na yi musu bakin kofar falo lokacin ma dab ake da kiran magriba.

Shi ya bi su a baya ni kuma na koma ciki kai tsaye d'akina na shiga na zauna gefan gado tare da tallafe ha'ba.

Oh hasashen da ake ta yi akan matar nan yana nema ya zama gaskiya tabbas akwai abinda take yi ko ta sanya malamanta ke yi mata akan jama'a, ai 'yar kasuwa ce mai hurd'odi da yawa mafi akasari kuwa duk eani dan kasuwan da ya yi shura a duniya yana neman jama'a walau ta hanyar Allah ko ta hanyar halaka.

Ni dai nasan ina tsananta rokona ga Allah akan ya kawo mini kasuwa da jama'a masu k'aunar abinda nake sayarwa ko a can baya ma da na dinga fafutukar tsayuwa da kafafuna addu'ata kenan Allah ka d'ora ni akan masu sayan kayana, Ubangiji Allah ka haskakani Allah ka ba ni nasibi da jalabi abinda nake roka kenan a wurin Allah ban ta'ba kauce hanya domin tara mutane ta kowace siga ba.

Tabbas ana neman jama'a ana kuma karawa da farin jini da kwarjini babu shakka akwai daya daga cikin abu biyun nan da na fad'a tana yi ko kuma tana sanyawa a yi mata.

Asirin mallaka kuma za ta iya yi masa tunda labari yazo akan cewa ba ta son kishiya idan ba mu fita ba to ita ta fita zakka a cikinmu ta zama mad'aukakiya a wurinsa.

Wannan shine tunani na akanta.

Bayan sallar Isha'i ya shigo ban ji ma da idar da sallah ba ina ma zaune saman daddumata da carbi mai lamba makale a hannuna.

Sai da ya jira na kammala tukkuna muka shafa addu'a a tare ya ce." Abinci za ki ba ni yunwa nake ji wallahi tun safe rabona da abinci Amina."
Ina ninke dadduma ban kalleshi ba na ce." Tun safe lallai da ka sani kawai ka d'auki azimi."
Ya d'an riko gefan hijabin jikina cikin sigar tsokana ya furta." Idan na yi azimi ke kanki kin san gajiya nake yi da daddare ba ni iya aikata komai kuma yau na jarabtu dake."
Ya'ke na yi ban ce komai ba.

Ya sake janyo hijabin nawa a karo na biyu har sai da na yi tangal-tangal na ce." Menene hakane?"
Ya cika gefan hijab din yana fad'in." Je ki kawo abincin mu yi magana."
Ban ce komai ba na fita kai tsaye kicin din na nufa Baba Tabawa ta gama shirya komai jallof din shinkafa ta yi ta ji alayyahu da busashen kifi ta yi kyau sosai tana ta kamshi ta had'a zobo shima da ya ji kayan kamshi Baba Tabawa akwai tsafta da gwanancewa wurin shirya abinci mai rai da lafiya.

Na shirya masa duk abinda ya kamata a tire na d'auka na fita daga kicin da takaicin abubuwa da yawa a raina.

Yana kwance saman gadona yana waya na dire tire din hannuna tare da zama can gefe ya d'an jima yana wayar kafin ya kammala ya sauko kasan kafet yana fad'in." Ki zo mu ciyar da juna mana."
"Ka ci kawai zan ci an jima."
Bai sake magana ba ya zuba abincin da kansa bai nemi dana zuba masa ba lemon ma shi ya tsiyaya abinsa ya yi Bismillah a nutse ya fara cin abincin.

Na d'auki wayata ina dubawa sai na tsinkayi maganarsa yana fad'in." Hirar me kuka yi ne da Aziza Amina?"
Ya fad'a tare da dubana.

Na kalleshi da mamaki namiji da son jin gulma kai tsaye na ce." Hirar matarka muka yi.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: Ya ce." Hirar matata kuma?"
Na ce." E, mun yi hira akan lalurarta da kuma wata mas'alar da ta shafe ta.''
Ya d'an kalle ni kafin ya mayar da hankalinsa kan abincin da yake gabansa ya furta." Ku fa mata ba a raba ku da gulma Amina wace mas'ala kuma?"
Da mamaki na ce." Ka ji ka da wata magana ai yanzu gulma ta tashi daga kan mata ta koma kan maza wallahi."
Ya kalle ni na wani lokaci kafin ya ce.'' To ba ni na sha wace mas'ala ce?"
Yadda ya fadi maganar cike da son jin labarin sai ya ba ni dariya sosai na ce." Ka gani ko? dama na gaya maka gulma ta tashi da ka kan mata."
Sai ya 'bata rai yana cewa." Me ki ke nufi ?" Nasa dariya tare da cewa." Ai ban ce maka magulmaci ba misali na yi kawai."
Murmushi ya yi kafin ya cigaba da cin abincin d'akin ya d'auki shiru na wani lokaci na ji gyaran muryarsa na dube shi ya gama cin abincin ya ta so ya zo kujarar da nake zauna ya nani'ke ni sosai yana fad'in." Bari na zauna kusa dake sosai zan fi fahimtar gulmar yadda ya kamata."
Murmushi na yi ban ce komai ba.

Ya kamo hannayena yana dubawa kafin ya ce." Wai ke ba ki jin kunya ne?"
Na kalleshi da sauri kafin na ce." Me kuma na yi maka?"
Ya bud'e tafukan hannayensa yana fad'in." Ya kamata ace hannayena da naki sun bambamta ki dinga yin lallai na gaya miki yana yi mini kyau."
A jiyar zuciya na d'an sauke a nutse na ce." To zan yi in sha Allahu.''
Wayarsa aka kira ya je ya d'auka daga tsaye ya amsa kiran na d'an wani lokacin kafin ya kammala yana kashe wayar yake fad'in." Lokacin madam ne yanzu kashe wayoyin zan yi gabad'aya sai Allah Ya kaimu kuma."
ina kallonsa ya kashe duka wayoyin nasa kafin ya dawo ya zauna kusa da ni yana cewa." Ba ni labari."
Sosai na dube shi kafin na ce." Kasan Halisa k'anwar Hajiya Aziza?"
Ya d'aga kansa yana fad'in." Kwarai na san sunanta amma a zahiri ban ta'ba ganinta ba.
Chapter 155 · 0% Book details