← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 183 OF 276

Sashe 183

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka had'a kan komai suka juya da baya domin fita cikin gari.

Sukairaju da D'ahuru suna bayansu shi da Malam Isiyaku suna gaba.

Ya d'an dube shi da gefan Ido gabad'aya ya yi sanyi mutumin fargaba ta mamaye shi.

Tausayi ya bashi kad'an domin dai babu yadda za a yi ya sake shi ba tare da ya sanya hukuma a ciki ba.

Mutumin banza ne wanda zuwansa duniya bai amfanar da kowa ba.

Abin jajantawa da tausayawa iyalinsa da ya jefa rayuwarsa cikin gagari da 'kyama ta jama'a duk da akwai ire-irensa da yawa a gari masu ci da addini da halakar da mutane amma a ganinsa wannan nasa ya yi muni sosai.

Ya ce." Ranar da ka fara yi mini bayani akan za ka yi aiki akan matata Hauwa ita dayar ba ka ta'ba wani aiki a kanta ba?''
Ya yi shiru na d'an wani lokaci kafin ya furta." Idan itace Amina gaskiya marigayiya bata ta'ba sanya ni aiki a kanta ba, abinda na sani shine ta ta'ba ce mini tana so a had'a taurarinta dana Amina din saboda nata suna da haske sosai kuma iyayen makarai ne a tare da ita tana da jalabi sosai bayan haka ma ba kasafai jifa ya ke kaita kasa ba tunda ba raguwa ba ce wurin addu'a.

Taurarinta suna da tsananin haske dalilin da ya sanya kenan itama ta buk'aci da su yi musharaka wurin haduwar taurarin.

Ya jima yana girgiza kansa da mamakin abin.

Ya jima da sanin cewa ana iya amfani da haske da taurarin mutum domin cimma wata manufa wasu lukutan mutum na zaune kaf sai a kwashe masa taurari bai sani ba.

Wato malam ka ji tsoron Malaman yanzu da suka kwashe kayansu daga gaban ma'aki.

Kwana da yini suka yi a garin jos duk yadda Malam Isiyaku yake karyar da kai da nuna ya yi nadama bai saurare shi ba.

Yana da jama'a sosai duk da wata mu'amula ba ta ta'ba had'a shi da shugaban jami'an tsoron garin ba.

Dalilin suna da shahararsa a duniya ya sanya a daran ya gana da commissioner yan'sanda suka cika hannu da Malam Isiyaku zuwa sansaninsu.

Gajiya kam sun kwaso ta daga shi har yaran nasa ga tafiyar mota sai gefen asubahi suka shiga garin abuja ana ta kiran sallar farko.

Ban san ya dawo ba sai da gari ya waye tukkuna na fito na same shi da yaran gabad'aya a falo a zaune.

Sun zagaye shi yana ta sauraransu yana murmushi Minal yar lelanshi tana kan cinyarsa.

Twins kuma na gefansa a tsaye suna ta tsalle Khalil na saman kujera a zaune.

Dukkaninsu cikin tsafta Mairo ta kintsa su.

Suna ta 'kamshi.

Na yi murmushi ina kallonsu gwanin ban sha'awa na ce." Cikin dare ka dawo ne?"
Suka juyo gabad'aya suna kallona har da shi ba su lura da fitowata ba sai da na yi magana.

Ya gyad'a kansa a nutse ya ce." Gefin asuba na shigo Amina.

Ya kuke na same ku lafiya."
Na ce." Alhamdulillahi ya su Hajja?" Domin ni ce mini yayi kano za shi kuma zai kwana daya."
A tak'aice ya furta suna gaishe ku."
Ya sauke Minal kasa Yana fadin." Zan kwanta zuwa an jima ki tashe ni."
Na ce." To shikkenan."
Ya haye sama da dan sauri.

Na dube su Usai ta yi saurin janye idonta daga kaina.

Na sassauta fuska tare da mika mata hannuna ina fad'in." Zo." Tun ranar da na mur'de mata kunne take ja baya dani.

Hassana ce ke iya zuwa kusa da ni har ta yi mini hira.

Minal kuwa yar d'akina ce tunda ita dama can akwai ta da saurin sabo."
Ta zo din kamar yadda na buk'ata amma bata kalle ni ba.

"Na ce." Menene?"
"Babu komai."
Na ri'ko hannunta a nutse na furta." Kina jin tsorona ne?"
Ta girgiza kanta.

Na d'ora ta saman cinyata ta ai kuwa sai tasa dariya tana kallona abin ya zo mata daban.

Hassana ta taho itama tana bata rai.

Na dauketa na sanya a daya gefan suka dinga dariya suna yi wa Minal gwalo ita kuwa mai neman jiran kiris ta fashe da kuka.

Khalil yana yin dariya ya ce ni zo na goya ki."
Na ce." Zo nan goyo kike so ko?"
Ta daga kanta.

Na ce." To ta kwana gidan sau'ki je ki ce Mairo ta bada abin goyo."
Ta kuwa ta fi da sauri.

Na dire su a kasa ina fad'in." Idan ba ku sanyata kuka ba bakwa jin dadi, kun yi girman banza."
Ina shiga d'aki ta shigo da towel din Sultan tana mika mini na ce." Aiki ya same ni kenan, gashi wanka zan yi yanzu Minal amma muje."
Ta biyo bayana na samu Taburni da yaran tana had'a musu tea na ce." To zauna ki ci abinci idan na yi wanka na fito zan goya ki."
Mairo da ke goge musu kayan makaranta ta ce." ashe da gaske goyon za a yi Hajiya."
Na ce." K'warai kuwa Mairo na juya na fita daga d'akin ina jinsu suna yi mata dariya.

Na sami Adam a falon a tsaye wanda shigowarsa kenan.

Muka gaisa yana tambayata Baba ya dawo?"
Na ce masa ya dawo amma ya kwanta sai zuwa an jima ya dawo lokacin ya tashi.

Ya ce to cikin sanyin jiki kafin ya juya ya fita na bi shi da kallo gwanin ban tausayi.

Wajan daya da rabi na tashe shi domin yin sallah.

Ya tashi zaune yana kallona goye da Minal a baya.

Ya ce "Wacece a bayanki?"
A tak'aice na ce." Name sake dina ce."
Sai ya yi murmushi ya ta shi ya shiga bandaki ina zaune ya fito d'aure da alwala na ce." Adam kuwa ya shigo nemanka d'azu."
Ya ce." Zuwa an jima zan nema shi.

Sallah zan yi yanzu ki kawo mini abinci.".

Na tashi na sauka kasa na had'o masa abincin da abinda zai buk'ata na koma na same shi ya idar amma yana gyangyadi a saman daddumar hakan kuma ba dabi'arsa ba ce.

Na ajiye tiran ina tashinsa ya tashi ya nufi bed yana fad'in." Baccin zan sake komawa.

Da mamaki na ce." Abincin fa.''
Ya rufa da bargo yana fad'in." Sai na tashi tukkuna.

To wasa-wasa haka ya wanzu tsayin kwanaki hud'u yana wannan baccin gabad'aya yin ibada ne kawai yake tashinsa idan ya gabatar ya ce zai koma ya kwanta da rigima sosai yake cikin abinci ya zama kamar wani sususu jikinsa babu kuzari sai bacci sai kace wani rik'akken d'an 'kwaya.

Hankalina ya fara tashi domin na ce masa ya kira likitansa ya duba shi bashi da lafiya ya ce na kyale shi a hankali zai warware kawai dai na cigaba da kunnansa karatun al'kurani.

Ganin abin nasa ya'ki sau'ki na fara kuka domin tunda ya yi tafiyar nan ya dawo bai kwanta da ni mun yi sunna ba kwana biyar yanzu wanda a tarihin rayuwarmu hakan bai ta'ba faruwa ba.

Muka dinga rigima akan na ce zan gayawa Hajja ba shi da lafiya a ganina ai mai matsalar aljanu da farfadiya ya kamata ace ana kunnawa akaratun al'kur'ani a saitin kunne, ga yanayin jikinsa ya nune babu kuzari amma ya ce shi lafiyarsa lau wace irin gajiyace wannan da zata mayar da shi d'an maye kullum bacci....
*BINTA UMAR ABBALE*
https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa.

Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono.

To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba.

Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu.

Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya.

Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne.

To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji.

Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba.

Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu.

In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi.

Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama.

Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare.

Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki.

Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki.

Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu.

Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
*Gudun aure paid book 2k complete on telegram what'sapp Gruop 1k via 0542382124....

Binta Umar gtbank*
*07084653262*
*124*
A cikin kwanakin da ya kasance cikin wannan yanayin ki'ba ya yi ta fuska sosai ban sani ba ko baccin da yake yi ne ya janyo faruwar hakan oho! tunda gaskiya ba abincin kirki yake ci ba ballantana na ce tun asali ma mutum ne shi da bai fiye tasa abinci a gaba ya yi ta narka ba, kuma ba shi da irin ciye-ciyen nan na masu kudi.

Cikin dare na tashi na yi sallah raka'a biyu na tsananta addu'a sosai domin abin ya fara daga mini hankali yanzu kuma na gano babu shakka akwai abinda ya faru wanda yake b'oye mini.
Chapter 183 · 0% Book details