← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 246 OF 276

Sashe 246

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waya ta yi kara tana can saman dirowa kusa da Sahura ita ta miko mini don yadda ake ta caccakar ubangidan nata bata iya sanya baki ba yanayinta dai da yar damuwa itama abin ya bata haushi da mamaki.

Na d'aga wayar cikin nutsuwa ya kira yi sunana na amsa ya ce." Ki zo ki same ni mu yi magana ina sama." Na ce." To shikkenan." Ya kashe waya ni ma na kashe tawa.

Suna falon Hajja Inna Uwani da Hauwa da kuma mai sunan Mamana suna ta hira Hajja yanzu ta sake da 'yar uwarta.

Sannu na yi musu na d'an tsaya muna magana da ita akan farin kwalli wai ta sanya Magaji ya nemo a can kano din ya kawo had'e da garafuni na ce to shikkenan an gode.

Ina kallon Hauwa tana d'an satar kallona domin ni kaina nasan na yi kyau sosai atamfa ce a jikina amma duk jikinta aiki ne da uban stones ko ta ina dinkin buba ne ya zauna a jikina yadda ake so.

Na haye saman zuciyata sam babu dadi ina kallon tarin kayan da su Adam suka jibge wajan 'kafar benan zan dai ji dalili.

A zaune na same shi yana waya aikin kenan na zauna har ya gama ya juyo tana kallona tare da kiran sunana.

Na sake amsawa ni ma idonsa a kaina.

Ya cigaba da cewa." Ki yi hakuri yau tun safe ban shigo ba kin san Allah bacci ne ya shammace ni mai nauyi na ce da Hauwa ta tashe ni kafin azuhur wai ta manta sai uku da wani abu na tashi sallah sai a lokacin na yi."
Na yi shiru ban ce komai.

Ya ce." Na so yau a yi wa yaran nan yanka hakan bai yiwu ba amma gobe idan Allah ya kaimu za a yi da wuri akwai shanu biyu wannan na jama'ar da suke kewaye damu ne ku d'iba Hajja ma ku bata nata ku bawa Hauwa da duk wanda yake da hakki.

Ragona hud'u ne wannan naki sai kin ga dama za ki ba ni."
Ya fad'a yana kallona na daure zuciyata na ce." To an gode Allah Ya saka da alheri da budi."
Ya ce.'' Ni ne da godiya ranar juma'a mai zuwa kuma za mu yi walima kamar dai yadda na saba abokaina da Malamai za su halarta in sha Allahu rabbi za a yi adduoi kamar yadda annabin rahama ya koyar da mu.

Ubangiji Allah Ya raya mana zuria."
Na sake amsawa da Amin Ya Allah.

Ya yi shiru na d'an wani lokaci kafin ya cigaba da cewa." Duk abinda za a buk'ata fannin ci da sha za a yi order babu buk'atar a wahalar da wani sai dai akwai turaman atamfofi da Nabila ta yi mini tallansu gasunan na saya miki ki rabawa jama'arki."
Na sake godiya a ta'kaice kafin na ce.'' To abinda yake cikin kwalayen fa."
Ya d'an yi shiru kafin ya furta.'' Zannuwa kawai na saya a wurinta amma bari mu gani."
Ya fara neman lambarta tunda wayarsa dama tana hannunsa bugu d'aya ta shiga ta d'aga na ji suna gaisawa ya ce." Bayan zannuwan da na saya menene ki ka aiko yara da shi a akwali?"
Shiru ya yi yana sauraranta da yake can k'asa take magana ban ji komai ba.

Sai da suka yi sallama tukkuna ya dube ni yana fad'in." Kin ji gudumuwa ta yi mana wai abin rabo ne duk wanda a ka bawa zani sai a sa masa cikin jaka mun gode ko?"
Na ce." Ka gode dai ai kai ta yi wa ba Amina ba.

Ya yi shiru yana kallona na cigaba da cewa." Ka ce da ni soyayya kuke yi ba wai ka zaunar da ni kana kwantar mini da kai ba.

Soyayya kuke yi a fakaice ka yi mata alheri ta yi maka zaka maye gurbin Maryam da ita ko ba haka ba ne."
Ya gyad'a kansa yana cewa.'' Sai ta iya kasancewa hakan ne amma ana ta 'bangaran fa wata'kila sona take yi."
"Kai kuma da ka gane hakan sai ka cigaba da biye mata tunda kana hangen jin dadi da nagarta a tattare da ita ko?"
Ya yi banza da ni kawai ya mike 'kafarsa ya kwanta tare da lumshe idonsa.

Na ce." Wallahi tallahi wannan abin ya ba ni mamaki da tsoro yanzu kai ba ka jin wani iri a jikinka.

Ya bude ido yana dubana kafin ya furta." Ba ni jin komai, kuma ba zan yi rigima dake ba a cikin mutane Nabila dai idan za ta sare kanta ta ba ni shi saboda so wallahi ba zan aureta ba.

Idan kun ce tana sona ba zance a a ba, amma ni fa ba ni sonta ba kuma ni da niyyar auranta.

Wannan maganar idan ba ku daina yi mini ita ba daga ke har ita Hauwa wallahi sai ranku ya 'baci tunda babu wadda ta haife ni a cikinku ina dalili ne za ku dame ni da wata Nabila."
Na ce." Kai zaka daina idan har kana so a daina yi maka maganarta cikinmu babu yaro k'arami da za ka yi wa wasa da hankali."
Ya furta." Zan daina amma ba zan wula'kantata kamar yadda kuke so ba wallahi, idan zan nemi aure a cikinku akwai wadda ta isa na yi wasa da hankalita, abinda Allah da Annabinsa suka halasta mini me yasa zan ji tsoron wata hallita wadda take da rauni kuma take a k'arkashin ikona........
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA #700 VIA 0542382124...BINTA UMAR GTBANK.*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*163*
Share shi na yi ban 'kara tanka masa ba ba kuma don ba ni da abinda zan ce ba.

Na tashi na sauka k'asa jikina babu wani karsashi ya rantse da Allah ya kara rantsuwa ba zai iya auranta ba to yaudararta zai yi kenan tunda shi ma zuwa yanzu ya gane sonsa take yi muddin bai fito fili ya nuna mata baya ra'ayinta ba za ta cigaba da bibiyarsa da zaman saurare daga gare shi tunda yana sayan kayanta yana kuma bata kudi yawanci mu mata wayayene shi yanzu ga abinda yake cikin zuciyarsa a game da ita duk da ba wai ya bankad'a mini zuciyar tasa ya yi na gani ba amma dai akwai k'amshin gaskiya a maganarsa don da ya na sonta da niyyar aure ba zai yi rantsuwa da Ubangiji ba tunda ya san girmansa.

Shirunsa da yanayin yadda yake mu'amulantarta shine abinda zai k'ara mata kwarin gwiwa ta ji a ranta kamar buk'atarta za ta biya domin samun nasarar mallakarsa duk abinda take yi a kansa da wanda ya dangance shi sone ba wani abu ba.

Bandir din atamfofin irin mai sha biyu ce bandir shida kuma mabambamta ba duka iri daya ba ne, sun yi kyau sosai duka cotton irin 'yan dubu goma nan ne da ake ya yi idan za a yi ankon biki.

Duk abinda ya kamata da a yi na al'ada da fita hakki su anti Yagana sun yi hatta da atamfofin sai da suka d'ibarwa Hajja nata duk da ba ta yi wata gayya ba amma ai tana da jama'a a can garin Dambatta idan ta koma gida sai ta raba.

Nama kuwa da aka soya zallar tsoka da yawa suka zuba mata cikin fanteka tace ya yi yawa Hajiya Saratu ma kad'an ta d'iba yayin da inna Uwani ta yi kamar ta dora hannu aka ta dinga rusa ihu ganin yadda Hajja ta ce da masu aikin su kwashe nama ta d'ibi daidai gwargwado.

Hauwa d'anye ta kar'ba ba ta bari an soya ba ita kuma Inna Uwani koda anti Yagana ta nuna mini wanda ta zuba mata na ce ya yi kad'an ta 'kara ashe duk da haka ba a yi mata gwaninta ba ta ji haushi sosai saboda Hajja bata kar'bi naman da yawa ba ta bawa masu aiki.

Su kansu su anti Yagana sun samu soyayyan nama sosai fatar shanun na sanya aka gyara musu (Ganda) da kawunan suka d'iba Sahura ma ta d'ibi daidai gwargwado sannan sauran na sanya baba Tabawa zubawa a buhu biyu yan gidanmu Ummansu Hadiza gabad'ayansu dai da suka zo tare na ce idan sun je sai su yi rabon a tsanake a tamfofi kuwa kowacce sai da ta tsira da turmi shida duka cikin kowane bandir sai da kowa ya samu har da ragowar wasu.

A ranar da muka yi walima k'warai na samu alherai masu yawan gaske daga wurin manyan mutane daga cikin abokanansa da suka samu.

Kud'i kaman sai godiya yara sun samu kaya masu yawa.

Babu shakka kowace haihuwa da goshinta don haka ni dai ba ni da bakin magana sai dai godiya ga Allah.

Washe gari masu aiki na ta hidimar gyara gidan ciki da wajensa.

Su anti Yagana na ta had'a kaya don 'yan gidanmu ma su Ummansu Hadiza da sassafe suka d'auki hanya bisa bin umarnin Babanmu ya ce su taho lallai shi kuma maigidan ya yi musu shirin tafiya cikin mutunci da rufin asiri don da ya ji a motar haya suka zo ya yi fad'a sosai har yana cewa lefina ne nasan za su zo mai yasa ban gaya masa ba tun daga can ya sanya a kawo su ya fi nutsuwa.

Sahura na ta gyara mini wardrobe ita kuma Yusra na shiryawa yaran kayansu.

Hauwa ta aiko Khalil wai na bata atamfa turmi bakwai jin haka Ya Falmata ta fara fad'in ba a d'ibar mata ba dama."
Sahura ta ce." Ni na d'ibar mata turmi shida cikin kowane bandir na d'auki daya."
Ta ce." To kuma wace atamfa za a bata."
Anti Yagana ta ce." Tunda da akwai a bata mana wata'kila wani zata bawa."
Yaron ya ce." E, na ji suna magana da inna Uwani za ta tafi da su can bauchi ta yi rabo."
Ya Falmata ta dube ni tana ta'be baki ban ce komai ba na ce da Yusura ta d'ebo abinda suka rage saura turmi sha uku gabad'aya na ce a cire bakwai din da suka buk'ata a bashi ya kai mata.
Chapter 246 · 0% Book details