← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 276

Sashe 105

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D'akin Baban Saude ta nufa tana cigaba da yin k'ananun maganganu wanda kad'an na tsinta daga ciki tana ce wa." Mu a lokacin mu ina muka san wani kai 'karar miji balle yin jayayya dashi da ganin daidai ake da juna, ai duk macan da tace ba zata yarda ta zauna a kasan mijinta ba tana tare da wahala shiyasa auran yanzu ai baya karko.''
Na dinga kallonta da bugawar zuciyata to me kuma ya kawo wannan maganar idan dama ba ta shirya tsinka ni a wurinsa ba, Ina ce ai tun kafin a yi wannan zaman Baban Saude ya gaya mata abinda ya faru.

Shine kuma za ta zo ta canza magana.

Gabana ya cigaba da fad'uwa na koma cikin d'akin na zauna jikina duk a sanyaye hakika ban ji dadin gayyatota da aka yi ba domin kuwa za ta iya fad'in wasu maganganun da zai sake bashi kwarin gwiwa, kuma da take cewa su a da ba haka suke yi ba to yaushe zata had'a mazan da dana yanzu, ai yanzu lamarin rijalu ya lalace domin kuwa da yawa daga cikinsu basa tsoron Allah wasu ma idan baka fito ka nuna musu cewa daidai ake ba to ba za a zauna lafiya dasu ba.

Da yawa akwai mazan da sun fi so idan sun ce kule a ce musu cass! a hau sama a fad'o a tare a buga a goga hakan ya fi musu dad'i, amma wallahi idan suka samu mace saliha mai bin su sau da kafa sun fi yi mata iyashege da shegantaka.

Hankalina yana kan agogon da yake kafe a bangon d'akin biyar da rabi yanzu ina lissafi lokaci a k'alla yanzu ya yi awa daya da zuwa amma ba a neme ni ba, ai na d'auka ni ma za a zauna da ni domin idan ya fad'i abinda ban yi ba na kare kaina kuma a shirye nake da na amsa lefin da na yi na bashi ha'kuri.

Har na cire tsammanin cewa za a yi zaman da ni na ji muryar Baban Saude daga cikin d'akinsa yana kwala mini kira.

Na amsa da sauri tare da tashi zumbur na d'auki mayafin rigar jikina na rataya a wuyana na zura takalmi na fita.

Littafin nan na kudi ne, don girman Allah kada ki karanta mini ba tare da kin biya ni hakkina ba.

A nutse na shiga d'akin tare da sallama gabad'aya suka amsa har da shi da yake zaune a gefan Baban Saude Dada da babansu Fadila kuma suna zaune a waje daya.

Gefe guda kuma kwanukan da suka ci abinci ne a ajiye.

Gefan Dada na zauna ina 'kara daidaita yanayin da nake ciki.

A nutse na dubi Babansu Fadila na gaida shi ya amsa da sakin fuska kamar yadda muka saba gaisuwarmu cikin mutunci.

Sai da na sake daidaita yanayina tukkuna na dubi gefan da yake zaune muka had'a ido da juna domin dama tun shigowata na lura da cewa idanuwansa suna kaina.

Na ce." Barka da yamma ya hanya?"
Ya amsa babu yabo babu fallasa da "Barkanmu dai ya kike?''
Shiru na yi ban sake cewa komai ba, d'akin ya d'auki shiru na sakkoni kafin Baban Saude ya yi gyaran murya a nutse ya dube ni yana ce wa" Amina tun kafin na kira ki zuwa nan mun tattauna abinda ya had'a mu anan mijinki kafin ya fadi aibunki sai da ya gama fad'in alhenki sannan ya fad'i dalilin da ya sanya shi yi miki wannan hukuncin domin horone a gare ki.

Ya nisa kafin ya cigaba da ce wa." Kamar yadda ki ka tuba ki ka kar'bi kuskuranki haka nan shi ma a yanzu kafin shigowarki na nuna masa illa da rashin dacewar abinda ya yi, domin kuwa ganganci ne mai girma tare da yun'kurin lalata aure kauracewa mace na tsayin wannan wattanin.

Hakan ba daidai ba ne, kuma an yi wa addini tare da koyarwar Ubangiji kutse.

Ni ba malami ba ne amma a iya sanina wannan abin da ya aikata kuskure ne, kuma gashi nan a zaune ya yarda kuskuran ya yi amma ya fadi hujjarsa wadda ba yi tsamarin ace an yi wannan kauracewar ba.

Annabin rahama bai hore mu da mu hora matayenmu ta hanyar kaurace musu tsayin wani dogon lokaci ba.

Ya hore mu a duk lokacin da iyalinmu suka
mana wani abu na kuskure.

Annabi S.a.w Ya ce." Ku nesanta kanku gare su na takaitacen lokaci ko kuma ku k'aurace musu a shimfida ku buge su kadan da gefan rigar jikinku.

Gashi nan a zaune ya nuna mini ya yi nadamar abinda ya aikata amma ya fadi hujjarsa ta yin haka a cewarsa idan ya kasance a kusa dake a koyaushe zai iya d'aukar matakin da rayukan kowa zai 'baci wannan shine dalilin da ya sanya ya k'aurace miki na tsayin wannan watannin ammana tare da bin sha'aninki domin sanin halin da ki ke ciki.

Ya yi shiru kafin ya sake numfasawa ya cigaba da ce wa." Kamar yadda ki ka yi mini alkawarin cewa za ki cigaba da zama dashi a haka to ina horanki da cewar wani abu makamancin abinda ki ka aikata kada ya sake faruwa idan kin samu ciki irin na haihuwa ki barwa Allah domin dukkanin hukunci yana hannunsa.

Mijinki ya tabbatar mini da ce wa shi ma har yanzu yana sha'awar cigaba da zama dake domin yana sonki wani dalili mara karfi ba zai sanya shi rabuwa dake ba ko da kuwa Allah bai kaddara masa haihuwa ba.

Saboda haka Dada da maigidan Yagana za su zama shaida a tsakanin zaman nan da muka yi wanda nake da burin Allah Ya sa ba za a kara maimaitama shi ba a tsakaninku, idan matsala ta fuskantoku za ku yi maganinta a junanku tunda dukkaninku ba yara ba ne."
Ya juya ya dubi inda yake zaune cikin nutsuwa ya furta." Ranka ya dad'e kamar yadda dai na gaya maka da farko cewa wannan yarinyar marainiya ce mahaifiyarta 'kanwata ce ni kuma a matsayin uba nake a wurinta.

Don Allah ka ri'ke ta amana domin babu wani dalilin da zai sanya ka aureta cikin sutturarta ka dinga dora ayar zargi a kanta.

Koda a gidan karuwai ka auro mace yana da kyau a ce daraja ta aure ya sa ka mutuntata to ballantana Amina da tun tasowarta a nutse take duk da irin jarabawar rayuwar da ta fuskanta a baya hakan bai sanya ta sarayar da mutuncinta ba.

Sanin da na yi mata ita din za'kwa'kwa'kura ce mai himma da zuciyar neman na kanta amma ba a ta'ba yi mata shedar banza ba.

Matarka ce idan da rabo watarana za ta zama uwar 'ya'yanka don haka muna neman wannan alfarma a wurinka a matsayinka na mai nisan shekarun da suka fi nata a duk lokacin da ta yi maka lefi wanda ba ma fatan haka sai ka kira ni a waya ka gaya mini, ni kuma zaka ga yadda za mu kwashe da ita.

Maganar gaskiya Alhaji Tajo idan Amina ta sake aikata maka wani lefin makamancin wannan ka sake d'aukar matakin da shari'a ta haramta zahiri ni zan shige mata gaba ko'ina domin a a kar'ba mata hakkinta." Shiru ya ratsa d'akin kafin ya sake nisawa babu wata fargaba bare shakku ya cigaba da maganarsa.

"Sannan Kuma sai abu na gaba, a madadin ni da mahaifinta da sauran 'yan uwana
Muna sake baka ha'kuri bisa abinda ta aikata maka ta yi kuskure zahiri wanda ko waye a ka yi wa hakan ba a kyauta masa ba, yadda ka ce ka yafe mata a gabanmu, Allah Ya sa hakan take a zuciyarka yanzu zan sanyata ta sake baka ha'kuri domin tabbas yin hakan shi ya dace da ita, tunda gabad'ayanmu maslaha da kwanciyar hankali muke nema.....
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/3, 8:38 PM] matar mijinta: *Wannan littafin na kudi ne vip 1k akan telegram.

Normal What'sapp group kuma #700 hanyar da za a biya kudin ita ce wannan...0542382124...Binta Umar gtbank ko kuma 7084653262...Binta Umar Opey bank.

'Yan nijar dala dari katin airtel za ku tura mini bayan kun kankare hoton.

A tura da sheda ta wannan lambobin iya What'sapp kawai.*
*07084653262*
*08089965176*
*V-VIP AREWA PEN
*70*
Jikina ne ya yi sanyi jin abinda yake ce wa, na yi shiru tare da sake yin k'asa da kaina ina jin Dada tana ce wa." Kuma ka rufa mata asiri baka tona mata ba, Allah Ya yi maka albarka mun gode sosai ka ji ko, Allah Ya saka da alheri, don Allah kada ka sanar da iyayenka da 'yan uwanka saboda kada su tsaneta a zahiri kowa zai ga ta yi maka mugunta tunda ita ai tana da yara da wani namijin, kaine abin tausayi da jaje, mun gode bisa rufe maganar da aka yi Ubangiji Allah Ya shi maka albarka."
Sai ta fashe da kuka ta sa gefan mayafinta tana share hawaye cikin kukan take ce wa." Uwarki tana kwance a kabarinta amma nasan a dalilin wannan zaman sai an tasheta ta ji abinda ki ka aikata, ai ita biyayyar aure ce ta kasheta ba ta ta'ba sa'bawa ubanki ba har ta koma ga Allah, ga Yagana nan tunda take da mijinta shekara da shekaru bai ta'ba kawo mana 'kararta ba, sai ke ko Amina, dama ai Yagana ta gaya mini kin ce badamuwarki ba ce don a lissafa miki aure, ai ba a kanki a kafara ba, to wallahi ba za mu yafe miki ba idan har ki ka sake kashe wannan auran, babu mu babu ke."
Baban Saude dariya ce ta kama shi jin irin zantukan da take yi ya ce ." Ai magana ta riga ta kare Dada menene na kuka kuma, babu wani dalili da zai sanya a tashi uwarta daga makwancinta, in sha Allahu ta nan lafiya lau kamar yadda muka je muka rufe ta, tana cikin rahamar Allah."
Ji na yi zuciyata ta tsinke dalilin kukan da Dada
take shar'ba wanda na tabbatar da ce wa mikin da ya jima da warkewa daga zuciyarta ne a ka fama mata, dama duk lokacin da ake yin wani taro a family dinsu sai sun yi kuka idan suka tuna da ita.
Chapter 105 · 0% Book details