Sashe 222
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da na yi magriba tukkuna na shiga kicin jallop nake sha'awa ta taliya da kifi ita na yi na zuba mana ni da Minal muka ci a kwano d'aya na ajiye wa maigidan 'yar kad'an dalili nasan ko zai ci ba dayawa ba tunda ba cimarsa ba ce taliya da makaroni.
Abinda ya fi so dangin towo kowane iri sakawara funkaso ko wainar masa ta bauchi Yana son faten doya ma abinci da miya bai dame shi sosai ba sai ya ce asa masa miya kad'an saman shinkafa.
Yana kuma son gurasa da miya sosai.
Wajan goma saura ya shigo tare da Sukairaju ashe tare suka zo garin.
Ya d'an tsaya daga bakin kofa ya kar'bi wayoyinsa daga hannuna ya gaishe ni na amsa babu yabo babu fallasa ya juya da sauri ya fita shi kuma ya karaso wajan da nake zaune hannunsa ri'ke dana Minal
A d'an hargitse yake gaskiya tsabar ma baya hayyacinsa gilashinsa a hannu yake abinda bai ta'ba faruwa ba duk rintsi da wahala baya cire gilashin nan na idonsa, sai sau daya lokacin da ya fad'i a garin bunkure yana dawowa hayyacinsa kuwa ya mayar da abinsa kamar wanda aka haifa tare da shi na ta'ba tambayarsa ko yana da matsalar Ido ya ce mini a a yana sanya shine domin kara karfin gani kuma dai ya zame masa jiki idan ma Babu shi a idonsa baya jin dad'i......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *PAID BOOK VIP 1K ON TALGRAM WHAT'S APP GRUOP KUMA,#700 VIA 0542382124....BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*149*
Na zura masa ido jikina a sanyaye ga dukkanin alamu akwai matsala.
Da kyar na bud'e bakina da ya yi mini nauyi na ce masa barka da zuwa.
Ya amsa yana ri'ke hannun Minal da take ta jan babbar rigar jikinsa.
Da ya amsa mini bai sake cewa komai ba ya wuce.
Na bi shi da kallo cikin lissafi a zuciyata shin menene ya gigita shi hakane? ko dai akwai matsala ta fannin daidaituwar jini shi da yarinyar tunda ya gaya mini zai ce ya d'aukota a yi mata genotype din tunda shi ya sanya nasa As ne kamar yadda nake As.
Idan hakan shi ya hadda masa wannan gigicewar lallai ya fito da abinda yake cikin ransa wanda yake ta nuku-nuku da shi yana kuma so ya yaudare mu kan cewa baya son auranta.
Alamu sun nuna lallai zuciyarsa ba ta so faruwar hakan ba.
Na tashi na bi shi saman na same shi zaune gefan gado Minal na ta wasa da agogon hannunsa da ya cire ya ajiye shi kuma yana zaune ya dai cire babbar rigar ya ajiye amma har yanzu yana cikin rashin hayyaci.
Motsin shigowata ya sanya shi dubana.
Bai janye idonsa ba har na isa kusa da shi na zauna still idona a kansa a takaice na ce." Me yake faruwa ne?"
Ya yi jim kafin dube ni da wani yanayi ya furta "Yarinyar As ce Amina.
Akwai matsala tunda ni ma As ne duka d'anjuma ne da d'anjummai, gidan Malam D'aha cike yake da ba'ki na nesa dana kusa sun d'ora manya tukuwane domin abincin jama'ar d'aurin aure dalili shi mutum ne na mutane k'warai da gaske da yawa jamaarsa ta mahaifina ne cikinsu wad'anda suka rage da iyalinsu babu wanda bai san da maganar wannan auran ba.
Babban abinda ya fi d'aga mini hankali anan shine yadda zan gaya masa cewa a janye d'aurin auran nan saboda wannan matsalar da bai zama lallai ya yarda da ita ba tunda ke kan ki kin sani abu ne mai wahala ya amince da koyarwar yahuduwa a matsayinsa na malamin addini kuma mutumin karkara."
Na yi shiru ina kallonsa zuciya na gaya mini ba wannan dalilin kad'ai ya sanya shi gigicewa ba akwai wani dalilin dai da yake boyewa.
Na ce." Yanzu wace shawara ka yanke?"
Ya yi shiru kawai yana kallona sai da na sake maimaita maganata tukkuna ya furta." Ban yanke ba har yanzu Amina bana jin zan iya dakatar da Malam 'Daha dangane da abinda ya niyyata ya kuma yi gangami a kansa."
Na furta." Za ka bari a d'aura auran kenan ?"
Ya gyad'a kansa yana kallona."
Sai na ce." To idan hakane menene abin damuwa tunda ka ji ka gani me yasa za ka daga hankalinka.
Ka bar wa Allah wata'kila sai ka ga kun samar da yara masu lafiya ba irin wanda ake tsammani ba."
Ya ce." Ai ba wani sonta nake ba Amina.
Maccan da nake tsoron rabuwa da ita itace nake jin zan yi hakuri na zauna zaman aure da ita idan aka ci karo da wannan matsalar ga misali nan a kanki.
Amma ina ji ina gani ba zan yi gangancin ba gaskiya magana kenan."
Murmushin takaici na yi kafin na ce." Akwai zalinci tsantsa idan har abinda ka fada da gaske ne a cikin zuciyarka to bari na gaya maka daka kai har malamin kun zalinci yarinyar nan.
Ya kamata duk wani b'oye -boye da kake yi ka fito fili ka yi wa mahukutanku bayani nufi na walliyanku wai shin kai karamin yaro ne?
A tunanina saurayi dan shekara a shirin da biyar ba zai yarda a yi masa irin wannan kutsen ba ya yi shiru sai dai dama idan yana so.
Idan ka bari aka daura maka aure da yarinyar nan to dama kana sonta a cikin ranka.
Soyayyar da za ka nuna mata da iyayenta a yanzu ka fito musu da gaskiyar abinda yake zuciyarsa kuma ka gaya musu babban dalilin da ya sanya ka janye nasan ko wasu basu yarda ba wasu daga ciki za su yarda tunda duka yanzu kai ya waye."
Cike da kosawa ya ce." Na gaya miki Amina Malam D'aha fa ba zai ta'ba amincewa da wannan batun ba.
Akwai shi da hujja wadda zai fatattaki duk likitan da na kai masa domin ya fahimtar da shi.
Ni dai da bakina ba zan iya furta masa cewa na janye ba saboda ga dalilina akwai hujja mai karfi a wajensa.
Na ce." To shikkenan na ji idan an d'aura menene makomar yarinyar abinda nake so na ji kenan."
na kudi ne don girman Allah kada ki karanta ba tare da kin biya ni hakkina ba
Ya daga kafadarsa yana fad'in." Wallahi ban yanke hukunci ba tukkuna amma dai ina jadadda miki ba ni yin zaman aure da ita.
Na bari a d'aura auran domin kada na katse masa hanzari bayan tarin jama'ar da ya gayyato gidansa ana ta hidima.
Akwai ciwo da takaici a ce an fasa abin zai yi muni da rashin dad'i."
Na ce." Babban abinda zai yi masa muni shine a daura auran ka bar masa yarinya a gida a jingine wannan shine asalin cin mutunci da wulakanci don haka wallahi kada ka fara."
Ya zura mini ido yana kallona kafin ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta furta." Ya zan yi to Amina na gaya mini dalilai na."
Na ce." Gobe tunda sai an sakko daga sallar Juma'a za a daura ka buga sammako ka d'auki likitan da ya yi muku genotype din ku je dashi gaban malamin ya yi masa cikakken bayani tare da illolin ciwon da yadda yaran da aka haifa suke shan wahala iyayensu ma suke cikin wuya duk a dalilin ciwon.
Ubangiji sai ya dubi zuciyarka ya sanya malamin ya fahimci abinda ake so ya gane."
Ya ce." To idan an yi haka mu yi yaya da jama'ar da muka gayawa wasu daga mutanansa fa na ce miki sun zo gidansa a cike yake da jama'a."
Kai tsaye na ce." An yi haka da yawa ai ba a kanku za a fara ba irin wannan idan kaddara ta gifta sai wani ya maye gurbi.
Idan hakan ya kasance yadda muke so kun fahimtar da malamin ya gane sai ka yi gaggawar kira na a wayar zan nemawa wani auranta sai a daura da shi kawai."
Ya yi sakato yana kallona na ce." Wannan itace hanya mafi sau'ki da za ka warware matsalarka ni ma zan baka gudumuwa daidai gwargwado amma idan har ka bari aka daura auran da wata niyya a zuciyarka ka cutar da yarinyar sosai kuma ba ka yi wa malam 'Daha adalci ba.
Ya rike hannuna tamau yana sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta." Na gode giwa Allah Ya yi miki albarka kaina ya d'aure gabad'aya a yanzu neman mafita nake yi."
Ni ma na sauke ajiyar zuciya a nutse na ce." Na kawo maka abinci ko?"
Ya gyad'a kansa yana fadin." Kawo mini."
Na tashi na fita.
Lokacin dana dawo yana bandaki na zauna gefan gado Minal tana tsakiyar gadon nasa a zaune tana ta wasa kira ya shigo wayarsa.
Minal ta d'auko wayar ta miko mini tana fad'in." Ana kiran wayar Baba, Mama ana kiran wayar Baba."
Na kar'ba na duba sai na ga mamanta ce Hauwa.
Na ajiye wayar har ta katse ta sake kira a daidai lokacin da ya fito da toilet din ya zo da sauri ya d'auki wayar yasa a kunne.
Ya amsa gaisuwar da take yi masa.
Jim kad'an ya ce." Malama na ce."A a itama Aminar za ta dawo nan cikinku in sha Allahu."
Ya d'an yi shiru yana sauraranta can kuma ya ce." To shikkenan ku zo ke da yaran gabad'aya ku sauka a gidan Hajja zan yi magana da Ade ku yi duk shirin da za ku yi yau da daddare."
Ya yi shiru yana sauraranta na dan wani lokaci sai ya ja tsaki ya cigaba da cewa." Wai sau nawa zan gaya miki ne gidan ba shi da spece din da za ku zauna ku biyu can gidan Hajja akwai part dina ku sauka a can hakan ya yi ko?"
Ya sake yin shiru dai yana sauraranta ta jima kuwa tana yin magana kafin ya ce." To na ji za a gyara in sha Allahu, zan kira ki da safe kafin ku taho."
Ya kashe wayar yana kallona kafin ya ce." Hauwa ce wai ita dole sai ta dawo kano itama yara kuma can duka suke karatu gobe Juma'a na ce su zo gabad'aya lahadi da sassafe mu koma gabad'aya har dake."
Shiru na yi ban ce masa komai ba.