Sashe 58
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kina ganin abinda kuka yanke da Babandi shine mafita a rayuwarki Amina."
Na dube ta a tsanake na ce.'" Anti Yagana me muka yanke ban fahimci inda maganarki ta dosa ba."
Ta gyada kanta cikin takaici da jin haushi ta furta." Yanzu Amina a ce kamar Babandi shi ki ka bawa lasisi da ragamar auranki saboda kin zama mara mafadi babu wanda ya isa ya gaya miki ki ji, a ce wai Babandi shine zai tsara miki yadda za ki yi, Kuma ki bashi kwarin guiwa da hadin kai ya kira mijinki mutum kamar wannan da yake da kima da dattako da shekaru ya gaya masa maganganu masu kaushi, ashe Amina ni ban isa na gaya miki magana ba ko?"
Sai kawai naga kwalla ta ciko a kwarmin idonta.
Hankalina ya tashi sosai na ce." Wallahi tallahi anti Yagana ban yi haka da Babandi ba, ya takura mini da tambaya ne shine na dan tsakura masa abinda yake damuna, kuma na gargadeshi akan kada ya gayawa kowa, ban taba tsammanin ma zai iya kiransa da wata magana ba, a Ina ma ya samu lambarsa mutumin da ba kowa ya san lambarsa ba.
Hawaye suka keto kumatunta suka fara d'iga.
Sai na ji duk gwiwata ta sanyi me ya yi zafi Anti Yagana take kuka irin haka.
Hawaye suka silalo mini na ri'ke hannunta ina fad'in." Wallahi tallahi anti Yagana ban sa shi ba, ban san a inda ya samu lambar wayarsa ba, ki gaya mini abinda ya fad'a masa domin tunda naga kina kuka na san abin babba ne."
Ta goge hawayen tana cewa." Ni babbar damuwata shine duk rintsi duk wahala ki yi hakuri ki zauna a dakinki Amina, ba wai na kafe akan don mutumin nan yana da wata suttura ba a a ke nake dubawa da kuma yaranki, matsalarsa ba mai muni ba ce a ganina tsananin so ne yake janyo kishi shi kuma na fahimci duk lokacin da zai tuna maza biyu sun taba ki kafin shi yakan kasa sarrafa kansa.
Kishin maza fa daban yake dana mata wallahi maza sun fi mata kishi, mu hauka muka fi su.
Kada wani ya rudaki akan ki fito ki yi hakuri ki zauna domin Babandi ba zai ta'ba iyawa da bukatunki da na yaranki ba.
Karshe dai ki kara famtsama harkokin da ki ka bari a baya."
Ina kuka na ce." Na ji batunki anti Yagana Kuma na fahimci duk abinda kike nufi, ni kaina ba na so ace na fito daga d'akina, amma abinda nake so ki fahimta shine, bayan wannan matsalarfa akwai wata a kwance nasan baki manta da cewa samun haihuwa zai yi mana mutukar wahala a tsakaninmu ba duba da sakamakon gwaji da abinda ya faru a baya na rasuwar abinda muka haifa.
Akan iya samun matsalar haihuwar yara marasa lafiya tunda har jini ya nuna anti Yagana kuma kinga ni duka yarana biyu a duniya, shi kuma a yanzu ne yake da buk'atar tara zuria.
Haihuwa da wahala tun daga samuwar cikin raino da nakud'a.
Ba fata nake yi ba duk na gama shan wannan wahalar Kuma na zo na haifi da mai lalura daga karshe ya mutu, anti Yagana akwai ciwo da damuwa wata ta zo daga bayanka kana kallo ta yi ta haihuwa kai kana zaune."
Ta girgiza kanta cikin damuwa ta furta." Na gaya miki tun farkon lamarin nan ki k'adaita Allah, domin su kansu turawan da suka kirkiro abin nan hasashe kawai suke yi, babu fa wani mahaluki da ya isa ya canzawa Allah manufa duk abinda ya wanzar shine daidai.
Ki saki zuciyarki ki zauna a dakinki, idan za ki haifi yara goma su mutu dama haka Allah ya nufa, idan kuma zaki haifi yara goma su rayu haka Allah ya nufa.
Ai Kinga da za ki auri Aminu ba a yi gwaji ba, kuma gashi kin haifi yara masu lafiya kwarai da gaske, to wannan ma kadai ya isa ki barwa Allah abinda ya tsara miki"
Ni kukan da take yi shi ya fi daga mini hankali domin na jima ban ganta cikin yanayi na damuwa da tashin hankali ba, kukanta yana da ala'ka da abu biyu domin yau yini aka yi a gidan bikin nan ana hirar Mamanmu har wasu daga cikin 'yan uwanta suka dinga kuka, a ganina matsalata kadai ba za ta sanyata zubar da hawaye irin haka ba, tashin zancen Mamanmu da 'yan uwanta suka yi shi ya kara dagula mata lissafi sai ni ce na yi namijin ko'karin tsayar da nawa hawayen na dinga rarrashinta akan ta yi shiru ban samu hakan ba kuwa sai da na yi mata al'kawarin duk rintsi da wahala zan ha'kura na zauna a d'akin mijina
Da wannan alkawarin ta tashi ta fita ta barni cikin tunani da zullumi.
Ni dai nasan anti Yagana ba makwadaiciya ba ce balle na ce mutumin nan siyanta ya yi da kudi.
Na fi zargin dai abin a jininsa yake domin na fahimta duk wanda zai yi mu'amula dashi da wahala ya hangi kuskuransa.
Ni a karan kaina na san shi din mutum ne domin kuwa duk inda ake neman dattako da nagarta taimako da tausayi ya kai a jinjina masa.
Amma a dabi'a da halayya irin ta dan adam dole a same shi da wani nakasu wanda sai mu da muke zaune dashi za mu tabbatar.
Baya ga mummunan zarginsa babu komai a tsakanina dashi face alheri domin har yau har gobe ina kallonsa da hakan, amma ina ji a cikin raina zamanmu ba zai yi dad'i irin yadda anti Yagana take so ba muddin bai canza dabi'a ba, ni kaina ba wai so nake a ce mun rabu ba domin duk abinda take yi mini hange ni ma ina yin hagen haka, to amma ai zaman ba zai yi tasiri ba idan da cin zarafi a ciki.
Kamar yadda ta ce mini na kira shi na bashi ha'kuri bayan wanda ta bashi ban ce to dan na yaudareta ba na yi aniyar kiran nasa sai dai fargabata ban san irin martanin da zai mayar mini ba tunda na gama fahimtarsa bai iya b'acin rai ba.
Sha biyu da wani abu idona biyu na kasa rintsawa saboda fargaba da tunanin d'anyan kan da Babandi ya yi mini, kawai don ina jin nauyinsa ne ya sanya ni dannewa amma tabbas da wani ne ba zamu wanye lafiya ba.
Wayata na d'auka wadda har na kashe na ajiye zuciyata ta kasa nutsuwar barin gari ya waye na kira shi, na san yanzu da wahala idan ya kwanta ya kan kai karfe daya yana aiki da computer kafin ya kwanta.
Da fargaba na lalubi lambarsa na kira hannuna na dan karkarwa karon farko kenan da nake jin fargaba da tashin hankalin wani raddi daga wajansa.
Sai dai kuma daga zarar wayar ta fara shiga sai ta katse.
Na tashi na fita falo wai ko network ne nan ma ta dinga yankewa, ni ce dai har farfajiyar gidan amma ta'ki tafiya.
Babu kuzari na koma daki na zauna da wayar a hannuna na rasa wane nazari zan yi.
Kai tsaye dai ba zan yanke masa hukunci ba, amma ai ban ta'ba kiran layinsa ya yi mini haka ba.
Ban ha'kura ba na jarraba kiran Sahura sai gashi ta shiga har ta fara ringing na katse da sauri na sake nemo lambartasa a karon da babu adadi ta sake katsewa.
A lokacin na gazgata hasashena a busy ya sanya ni.
Bai d'auki waya ba na san ko text na tura masa ba zai duba ba tunda dama can ya kan tara messages na mutane kafin ya samu damar dubawa.
Na kwanta cikin zullumi da tunani lallai akwai maganganun da Babandi ya gaya masa dama ai mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awakai yanzu shawo kansa sai na kusa zama k'aramar mahaukaciya.
Ban ta'ba kawowa zuciyata saki a cikin irin hukuncin da yake ganin zai yi mini ba, domin ni kallon da nake yi masa ma kome zan yi masa na takaici ba zai d'auki matakin sakina ba sai gashi na wayi gari da ganin text dinsa na saki d'aya Inda ya rubuta a takaice da kuma babban hafarai "NI ALHAJI TAJUDDEN IBRAHIMU NA SAKI MATATA AMINA SALISU SAKI DAYA." Na yi bala'in kad'uwa daganin sakon gabana ya dinga bugawa da mugun karfi yayin da wani irin yawu ya tsinke mini a bakina.
Da kyar bakina ya kar'bi abinda zuciyata take amayowa na dinga nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Zuciyata na harbawa da mugun karfi.
To da yake babu abinda ya fi ambaton Allah samun sasaauci a lokacin dadi da b'akinciki, cikin kan'kani lokaci na dan shiga nutsuwata na fara tunanin yadda zan yi na shawo kansa ya mayar da ni ba tare da kowa ya ji ba.
Babbar damuwata Anti Yagana da alkawarin da na yi mata jiya kafin ta je ta kwanta, amma ni idan ta ni ce zan iya jurewa tunda ba shine karo na farko ba.
Har yanzu zuciyata ta'ki aminta da cewar da sanin mahaifiyarsa ya sake ni.
Ya yi mini hakan ne saboda ya nuna mini ni din ba komai ba ce.
Kishi ba hauka ba ne yana da kyau ya ji ta bakina kafin ya d'auki d'amarar tozartani.
Hawaye masu zafi suka kece mini suka fara kasa tsere a dakalin fuskata.
Na yi kasa'ke da waya a hannuna gwiwata ta sage tamkar an buga mini guduma, komai ya dagule mini na rasa ma abinda zan yi.
Shi din zan nema domin na ji ba'asi akan abinda ya yi mini, har yanzu ban yarda da cewa abinda na aikata na cancanci hukuncin saki ba, ai ba rufe kofa na yi da Babandi ba, sannan kuma duk abinda zuciyarsa zata kitsa masa a kaina bai gani da idonsa ba, ni ba mazinaciya ba ce, idan ma yana hasashen hakan a kaina.
Na kira shi ya fi sau goma sha biyu bata shiga.
Hawayen nadama da tausayin kaina suka dinga gudana a kumatuna.
Ba zan kira mahaifiyarsa na na gaya mata ba, domin na tabbatar da cewa ba ta san abinda ya faru ba domin da yawunta ba zata bashi goyan bayan yi mini wannan tozarcin ba.