← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 276

Sashe 159

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daki ne na mussaman shi da matar tasa don ina hangenta a can wani gado a kwance irin na marasa lafiya shi kuma yana wata kujera.

Na ce." Ba mu da imani fa ka ce?"
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Kwarai kuwa ba ku da shi wallahi, kin ga yanzu yadda za a yi tunda ita ta gudu ta bar shi ke ki yanke abinda ki ke so na biya ki ki kula mini da shi kafin na dawo."
Na ce." A a daka bar shi a hannun Nabila zai fi alheri, idan zan kula da shi har sai na kar'bi kudi a hannunka mai ka mayar da ni."
Ya ce." Nasan ki da alheri ai, don girman Allah idan yaron nan yana wurinki ki sanar da ni hankalina zai kwanta jiya na gaya miki mun yi magana da Nabila ta ce mini ba ki kai mata shi ba."
Ganin yadda yake had'a ni da Allah ya sanya ni cewa." Yana hannunmu ni da Baba Tabawa cikin kulawa da koshin lafiya kuma tun jiya na kira Dr Sailuba ta had'a mishi duk abinda aka buk'ata."
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta." Na gode sosai my love life Allah Ya yi miki albarka.

A dan sanyaye na ce." Babu komai." Ina hangen Momin ta tashi zaune daga can wurin dake tana kallonshi shi ya juyo mata baya ya dage sai kalamai yake yi mini na dadin baki.

Na ce." Ka juya ka ga ta tashi fa."
Ya d'an juya a hankali yana fad'in." Ok jiya na ce miki tana so ku gaisa ko, amma bari mu bari zuwa yamma zan sake ta'bo ki sai ku gaisa."
Na ce." To shikkenan a ma sha Allah na ga jikin ya yi kyau Allah Ya kara sau'ki."
Ya amsa da Amin Amin mun gode giwa Allah Ya yi miki albarka." Na ce." Amin a takaice.

Ni na fara datse wayar saboda ganin kamar tana buk'atar magana da shi.

To yaro dai na d'auka tunda ta tafi ta bar shi zan yi iyakar bakin kokarina.

Bayan ubansa babu wanda nake jin zan gayawa ko Hajja kuwa amma tabbas nasan Hauwa rikici da gangami ta shiryawa kanta, dalili kuwa shine yadda abin nan da ta yi ya kidima shi ba zai kyaleta ba, to ma ji ma gani dai Allah Ya kyauta.

Sai bayan sallar azuhur tukkuna na samu Hauwa a waya.

Ta daga hankalinta a kwance domin ban ji alamun nadama da danasani a muryarta ba.

Jikina ya mutu sosai da kyar na furta." Kina ina Hauwa?"
Kai tsaye ta ce." Ina nan Bauchi."
Na danne takaicina tare da cewa." Ashe kin shirya hakan tuntuni to hakan da ki ka yi a ganinki daidai ne ko?"
Da d'an murmushi ta ce." Shine daidai Amina, domin wa'adin zamana ya kare a gidan tunda na haihu yaro kuma ai gidan ubansa ne tunda ba dashi na zo ba, mai zai sanya na d'auko shi na kawo shi inda babu tarbiya ba Amina sunan Amadu fa ya fi sunan ubana an ce mini ubana ba komai ba ne a lokacin da na nuna shi din wani abu ne, tuntuni na gaya miki dama ba zan jure wannan rashin mutuncin ba."
Cike da takaici na furta." Amadu fa aka ce shine Mahmudu Muhammadu.

Ki tuna mai wannan sunan shine wanda aka yi duniya dominsa Annabi Muhammadu S.a.w a ganina wannan abin alfahari ne a wurinki."
Ta yi murmushi tana cewa." A a ba da wannan niyyar ya sanya sunan Amadu ba.

Abokinsa mai rasuwa fa shi yayi wa takwara na ce masa ina son sunan mahaifina tunda na farko ya sanya sunan mahaifinsa daga fad'in haka ya fara gaya mini magana tabbacin dama haushina yake ji to menene saura a tsakaninmu na fita daga iddarsa da dama."
Na gyada kaina ina danne abinda nake ji a raina na ce." To kina ganin Allah ba zai kama ki da hakkin yaron ba shine ina ruwansa."
Ta yi dariya tare da furta." Allah Ya yafe mini shi kuma idan rayayyene Allah Ya raya shi."
Na yi shiru domin kamar kalaman bakina sun kare da kyar na ce." Yanzu mai ki ka gayawa inna Uwani."
Da sauri ta furta." Tun daga farko a har karshe wallahi ban boye mata komai ba, Amina ai na yi hakuri na yi kuma biyayya, ke kan ki ban shure shawararki ba, na yi ta ha'kuri tsayin wattanin dana d'auka a matsayin sakakkiya mutumin nan baya kula ni kuma bai furta ya mayar da ni ba, duk wata dama ya samu bai yi magana ba yanzu kuma ai komai ya zo karshe na gaya mata komai haka zalika ma babu wanda bai sani na a family din Babanmu."
"Kenan Hajja ta ji komai?"
Na tambayata cikin zullumi.

Ta furta." Kwarai kuwa d'azu nan suka gama waya da Inna." Na yi shiru Ina nazari kafin daga bisani na furta." Hauwa idan zu'kata sun huce a daidaita don Allah kuma yaron nan da kaina zan kawo miki shi gobe in sha Allahu rabbi, ki yi hakuri don girman Allah ki kar'bi d'anki kada ki wulakantashi domin bakisan baiwar da take tare dashi ba."
"Na rantse da girman Allah a yanzu dai Amina ko kin zo da yaron nan sai dai ki koma dashi don wallahi tallahi ba zan karbe shi ba sai ubansa ya zo da k'afafunsa ya nuna nadama akan abinda ya yi mini, idan har ke za ki iya jure wulakancinsa ni kam ba zan iya ba.

Ki ri'ke shi kawai na bar miki."
Bakina ne ya mutu murus na rasa abin cewa tunda har ta riga ta rantse nasan abu ne mai mutukar wahala ko na kai mata yaron ta kar'ba......
*GARKUWAR MATA.*
*BINTA UMAR ABBALE*
[6/4, 3:03 PM] Hauwa Galadima: *2K ON TALGRAM WHAT'SAPP GRUOP 1k VIA 0542382124...

BINTA UMAR GTBANK*
*V-VIP AREWAPEN*
*07084653262*
*110*
To wannan lamarin na su sai dai na ce Allah ya sawwa'ke har ga Allah ban so rigimar tasu ta yi tsayin da har magabatansu su shiga ba.

Saboda daga shi har ita babu yaro duka sun mallaki hankalin kansu su din masu yi wasu gyara ne, duk da mas'ala ta aure akan sameta a kowane gida amma abinda yake cikin gidan nan namu sai dai mu godewa Allah daga wannan sai wannan ashe kalmar hakurin nan da manya suke nanata mana akoyaushe tana da tasiri gabad'aya sha'ani na aure a yanzu ya zama abinda ya zama domin kuwa k'alubalan da ke cikinsa ba kowace macace zata jura ba.

Zawarawa sun yaiwata wad'anda mazajensu suka rasu ga 'yan mata nan birjik a gari suna yawo idan ma kana murna ka aurar da d'anka to ka bi shi da addu'a kawai domin kuwa zamani ya zo da mata da yawa suke ganin gwara su rayu babu aura akan yin sa saboda riskar rikici da tashin hankali idan ba a yi dace ba.

Abu ne a bayyane ba kowane a yanzu zamu bud'e baki mu gaya masa cewa ba ma cikin nutsuwa ya aminta ba.

Dalili ana ganin Ubangiji ai ya yi mana gamnakatar da auran attajiri wanda ba mu rasa komai ba na jin dad'in duniya tabbas ba mu rasa komai na jin dadi ba amma mun rasa kwanciyar hankali domin kuwa idan ana murna an kashe wannan wutar sai ya sake kunno wata da kansa.

Kwanaki biyu ba ni ganinsa a online hankali ya tashi domin tunda suka tafi tsayin sati uku kullum sai mun yi magana.

Na shiga damuwa sosai na kuma kasance cikin duba wayata a akai-akai.

Misalin goma da rabi na yi shirin kwanciya don ban jima da fitowa daga d'akin Baba Tabawa ba na d'auki wayata na duba sakon voice note din shi ya shigo na bud'e ina saurara yana gaya mini suna kan hanyar dawowa gobe domin sun gama shiri kuma alhamdulillahi ta ji sau'ki."
Jin haka ya sanya hankalina kwanciya domin tsakani da Allah kwana biyun nan na yi sune cikin fargaba da tunanin halin da suke ciki ko kuma na ce yake ciki tunda ta hanyar wayar ne kawai muke magana.

Washe gari da wuri kuwa na kira yarinyar nan da ta yi mini 'kunshi ta zo ta zana mini baki da jaa kafafu da hannayena.

Ya yi kyau ainun.

Na ce da Baba Tabawa ta shirya masa towon somovita ayi miyar kuka domin duk cikin kayan kad'i ya fi sonta.

Tare muka shiga kicin na taimaka mata tana goye da yaron a bayanta yana bacci muna d'an ta'ba hirar rashin lafiyar Momin har muka kammala tsaf towo semo da farfensun kayan ciki tunda shi ma yana daya daga cikin abinda yake so domin shi kam ya fi kauri ga abincin gida.

Lemo kam ba kowanne yake sha ba ya ma fi jin dadin zob'on da Baba Tabawa take yi masa mai cike da kamshin citta da kaninfari.

Na riga ta fitowa daga kicin din wanka na yi a gurguje na d'aura alwala tunda daf ake da kiran sallar magriba na shirya jikina a cikin atamfa java kalar sararin samaniya mai d'auke da adon zaiba da stones a tare fittedgwon ce ta d'an kama ni amma ba sosai ba.

Yanzu ina iya sanya matsatstsun kaya dalilin maganin tumbin da na yi amfani da shi wanda ya narkar mini da mugun tumbin da ya yi mini zuguda a ciki. 08089965176 wurin GARKUWAR MATA na sayi maganin yana da kyau sosai kuma harbel ne ba shi da side effect.

Ban yi cikakkiyar kwalliya ba domin can dama ban fiye fenta fuskata ba na dai shafa hoda tare da sanya kwalli na sanya jan janbaki a le'bena.

Na gyara gashin kaina sosai kafin na daura d'ankwalin daidai da zamani.

Ni ce har da had'a kankana da zumar mata ta goron tula itama dai duka order ce daga wurin GARKUWAR MATA na hada da madara na cika kofi na shanye wannan hadin idan na yi shi yana bala'in saukar mini da ni'ima sosai gefe guda kuma ga ruwan kaninfarin da nake yaiwata sha shiyasa kusan koyaushe a jike nake don ba ni da matsalar bushewa balle matsi da koyaushe idan wata mu'amula za ta kasance sai ya yi kiki-kaka kafin ya samu damar ratsa jikina.
Chapter 159 · 0% Book details