← Book details Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 276

Sashe 61

Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kayan sari kona miliyon nawa kike da bu
ata zasu iso hannunki a cikin kwana biyu da izinin Allah*
*Ni Badiat Ibrahim Mrs Bukhari
awar Sabuwan maigogul, Aminiyar Iyabo, uwar
akin Tani Shanono na gwada na san amfaninshi, kema
ar uwa ki kwada zaki bani labari siyan nagari maida ku
i gida.*
*Mun sani yanzu yana da kyau duk abinda zamu siya musan ingancinshi da nagartarshi bawai muita siyan magungunan mata kara zube ba.*
*Wannan kamfanin kayansu babu algus ko almundahana a ciki, da tsoron Allah da
warewa gami da gogewa ta sanin* *yadda ake sarrafa magunguna suke aikinsu, cikin nagarta da gangariyar tsabta.*
*Abu mafi sha'awa komai a cikin kwali yake a rufe kirib*
*ga ka
an daga cikin abubuwan da kamfanin yake samarwa*
*Tsumin dadi har Madiga tareda gunbarshi*
*Tsumin no excuse mela
abin bita zaizai*
*Gumbar dare daya wanka goma, dana gari da zumarta da tsuminta duk muna dashi*
*Zumar hana bacci gumbarta da garinta*
*Munada Arabian sabaya tare d Sudanese sabaya*
*Da zumarta*
*Sabaya ce dake cuko da
a mace duk ramarta, da
anjamewarta*
*Itama da zumarta*
*muna da mummuna da aiki*
*Akwai tsumi da gumbar ta da zaune tsaye*
*muna da kogin da
*Abangaren sanyi sun samar ma mata maganin matsolilinsu*
*muna da fitattun maganin sanyin da yake fata_fata d sanyi yayi mishi korar kare*
*Khanzur Rahman herbal formular*
*Sanyi clear syrup*
*7 days for chronic infections flusher*
*Sannan kuma muna da* *Package amarya*
*Package Uwargida*
*Package irin na zawarawan da suke shirin sabon aure*
*Bugu da
ari wannan kamfani yana sarrafa magungunan maza ba a iya na mata ya tsaya ba, wannan kamfani magungunan da yake samarwa suna da yawa wannan tsakurene daga cikin kayansu*
*Da sauransu da sauransu wanda bamu ambata ba.*
*Ba fa a iya haka muka tsaya ba muna d cancada cancadan zannuwan Gado da carpet*
*Domin neman
arin bayani ku tuntu
eta a kan lambar wayarta kai tsaye*
+2348032089456
*37*
Ya fad'a muryarsa har tana rawa, sai ya ba ni tausayi ni ma na ji idona ya ciko da kwalla dama daurewa kawai nake yi.

Haka muka karya a daddafe har yaran suma gabad'aya jikinsu ya yi sanyi ganin yadda muke cikin alhini da damuwa Yusi dai ya takure a kusurwar kujera har da kuka sai da anti Yagana ta rarrashi tukkuna ya yi shiru.

Garba almajirin anti Yagana ya shigo ya ajiye robarsa a bakin kicin ya shigo falon muka gaisa anti Yagana ta ce ya yi maza ya zuba ruwa a diro amma kafin nan ya fara wanke shi.

Har ya juya zai fita sai ya tsaya yana kallon Yusi ya ce." Ka je in ji wannan din nan yama sunansa?" Ya tsaya yana tunani. fadila ta ce." Bak'on da suka zo tare?"
Da sauri ya daga kansa yana cigaba da cewa." E shi ya ce na kira shi yanzu ya je Babansa ya kira waya za su gaisa."
Na dubi Yusi da mamaki a tare da ni, dama duk safiya Yana kiran waya don su gaisa, da farko da Garba ya ce ya je na d'auka Sukairajun yana buk'atar wani abu ne bayan karin kummalon da aka kai masa.

Yaron ya tashi da saurinsa sai na dakatar dashi ina fad'in." Yusi dama Baban yana kiran waya ne ku gaisa kullum?"
Ya ce." E wataran ma har ya ce na bawa su Arif da Sultan su gaisa, ko Arif?" Ya fad'a yana kallonsa.

Ya ce." Eh hakane har ya ce a gaishe daku bakidaya.''
Na gyada da mamaki fal a tare da ni.

To shin wai me mutumin nan yake nufi ne?

Ni ban ma ga amfanin zaman Sukairaju a tare da ni ba, kuma yaro dai ni na haifi abina ba za a yi wannan munafurcin da ni ba, ka sake ni amma ka dinga bibiyar 'yan uwana har da yaron da na haifa da wani namijin.

Na ce ." To koma ka zauna ba za ka je ba."
Anti Yagana da sauri ta ce." Akan me?" Shiru na yi kawai Ina kallonta da mamakin neman dalilin da take yi wanda ta fi kowa sani.

Tana kurbar kunun gyadar da ta tsiyaya kofi ta ce." Ki kyale shi kawai ya je, idan kuma ba so kike ki fito da komai fili ba, ta inda ya fi ki wayo kenan, yadda yake tafiyar da lamarin a siyasance sai ki zuba Ido ki ga iya gudun ruwansa."
Na yi shiru Ina nazarin maganarta.

Ni dai da ta barni zan datse alakar ne daga yau din, shi ma Sukairajun na sallameshi don ban ga amfanin zamansa a tare damu ba illa dorawa masu gidan nauyi da ya yi."
Kimanin minti ashirin yaron ya yi da fita sai gashi ya shigo ya zauna yana kallon anti Yagana ya ce." Baba ya ce na gaya miki zai kira ki yanzu."
Da sauri ta ce." To shikkenan Yusifa."
Kawai na saki baki ina kallon ikon Allah.

Gabad'aya abincin ma da nake ci sai ya fita daga raina na zuba mata ido a lokacin da ya kirata suna magana akan rashin lafiyar Gwaggwo.

Anti Yagana ta saki jiki da baki tana ta jadadda masa yadda Gwaggwon take jin jiki har da ce masa tana kwance bata iya motsa komai na jikinta.

Da yake handsfree ta sanya wayar ina jin muryarsa tar yana cewa." Ni muna gaisawa da Yusuf na ji ya fashe mini da kuka koda na tambayeshi shine yake gaya mini kakarsa ce babu lafiya kukan yaron ya daga mini hankali kwarai da gaske dalilin da ya sanya ma kenan na kira ki domin na tabbatar ya gaya mini duk yadda aka yi, zan yi waya asibitin Malam din duk abinda ake bukata game da mara lafiyar ba zai gagara ba idan ma gado za su bata hakan zai fi sauki Allah Ya bata lafiya."
Anti Yagana tana ta amsawa da Amin Ya Allah, mun gode sosai da kulawa Allah ya kara arziki da wadata."
Suka yi sallama ta juyo tana kallona raina a tsananin 'bace na mik'a hannu dukkunsu har shi Yusi din ba su ankara ba na kife shi da marin da na tabbatar zai gigita shi .

Kiji tsoron Allah idan har kin san baki biyani kudin littafina ba to kada ki karanta zai fi miki alheri ki ha'kura ko ki biya mai hakki hakkinta.

Illai kuwa a ki'dime ya tashi ya yi hanyar waje hannunsa dafa da kumatunsa hawaye suka fara kasa tsere a kuncinsa.

Anti Yagana ta rufe ni da fad'a tana fad'in." Sai kin je kin tsiyayar masa da ruwan ido haka kawai saboda zalinci zaki kifa masa wannan mugun marin me ya yi miki?

Lefin dai ba zai wuce ya gayawa mijinki magana ba, shikkenan fa sai ki lahanta shi.''
Shiru na yi ban tanka mata ba kawai na tashi da zumar barin wajan.

Yaron da yake tsaye a bakin kofa ya d'auka dukansa zan sake yi ya fita a guje yana sheshsheka.

D'aki na shiga na zauna a gefan katifa kaina a daure domin duk yadda na kai ga ganin na hasaso abinda mutumin nan yake nufi a kaina na kasa ganewa.

Shin wai ko ya manta da cewar ya sake ni ne, wane irin munafurci ne wannan da neman lallai sai ya d'ora mini lefi.

Ka sake ni ka fita daga sha'anina mana.

Wayata na d'auka da sauri kiransa zan yi domin na ji shin me yake nufi da ni ne.

Kamar yana jiran kiran nawa karaf ya daga.

A kaurare babu gaisuwa balle girmamawa dalili duk ya zubar da mutuncinsa a idona bana son mutum munafiki.

Na ce." Ban gane abinda kake nufi ba, ko ka manta cewa yanzu babu wata alaka da take tsakanina dakai?

Ina ruwanka da bibiyar abinda ya shafe ni.

Gwaggwo dai mahaifiyar mijina ce wanda mutuwa ta yi mana kutse ta shiga tsakani, na tabbata kuwa a duniyar nan ba zan sake katari da namiji mai nagartarsa ba.

Kana ta bina da sharri, ka yi nan ka 'bata ni, ka bi nan ka 'bata ni, to ta Allah ba taka ba, ka ja tsumman rayuwarka, ba ma buk'atar ko kwabonka, ba na son munafurci ni."
Cikin nutsuwa kamar bai ji zafin maganganuna ba ya ce.'' Ai na mayar dake dama na yi ne domin ya zama gargadi a gare ki.

Kuma ba don ke nake tsaye akan abinda ya shafeki ba, saboda wasu dalilai ne, ke ki ka haifi Yusuf amma ya fi ki hankali, kuma saboda shi din na shiga lamarin, ai na san kakarsa ce ko ba itace ta haifi Aminu Salihi ba."
Cikin takaici da b'akinciki na furta." Ban mayu ba, wallahi ban mayu ba na saku har abada ni dakai dama can ba a son raina aka yi ba, ba zaka tozartani ba wallahi ko maza sun kare a duniya ba zan zauna da kai ba, kuma ko mutuwa Gwaggwo ta yi menene abinda ya dame ka, babu ruwanka ba na son munafurci fa." Na sake maimaita kalmar munafurci domin na tunzurashi.

Bai tunzuru ba a tsanake ya ce." Sai ki yi kuma ni dai na mayar dake shekaran jiya na yi sakin jiya da safe kuma na kudire a raina na mayar dake yanzu kuma na sanar miki, don haka har yanzu kina karkashin ikona."
Da sauri ya yanke wayar kamar ya san abinda yake bakina mai muni ne tabbas da bai kashe wayarsa ba sai dai ya ji ruwan ashar a kunnansa saboda yadda zuciyata take a tunzure.

Na kasa motsi daga inda nake gumi na yanko mini tsabar tashin hankali kamar yadda ya fad'a a musulunce na mayu tunda ko jini daya ban yi ba kuma ka'idar musulunci jini uku ne na fita daga idda.

Hawaye masu zafi suka fara karakaina a kumatuna.

Anti Yagana ta shigo d'akin da karsashinta ganin yanayin da nake ciki ya sanya ta d'an yi sanyi ta tsaya tana fuskantata..."Menene kuma?" Tambayar da ta yi mini kenan.

Cikin k'unci da takaici na ce." Anti Yagana a wannan karon dole ki yi hakuri na d'auki mataki da kaina domin siyarwa kaina mutunci.
Chapter 61 · 0% Book details