Sashe 154
Gudun Aure Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka nan muka yini da ita kadaran kadahan domin hausawa suna cewa idan ba ka iya kama b'arawo ba shi sai ya kama ka shiyasa kawai na kyaleta ban iya ce mata komai akan lamarin ba tunda ai a duniya muke akwai kuma ranar tsayuwa idan har ita ta cutar da Halisa ta d'ora mata muguwar jinyya mai wahala ubangiji zai fitar da hakki.
Muka rabu kowa zuciyarsa cike da tunani domin kuwa ko bata fito ta fad'a tabbas ta fahimci na canza mata ba kamar yadda muke a da can baya.
Lokacin da na gayawa Babansu Madina zuwanta da kayan da ta kawowa Halisa da yara ya yi godiya kawai daga haka bai sake cewa komai ba Amina kin san su maza ba su yarda da irin wannan muddin ba gani suke yi a zahiri ba domin da farko da na gaya masa nuna zargin Maryam akan ciwon dake damun Halisa ya dinga fad'a yana cewa shikkenan lalura ba zata samu bawa sai a jingina hakan da wani mutuniyar kirki ce wadda ba ta da abokin fad'a sam baya tsammanin za ta aikata haka.
Duk yadda na so na fahimtar da shi ya kasa fahimta nagartatta kawai yake fadi shi ma ya sheda ayyukan alherinta a zahiri.
To sai kawai na kyale shi domin ba zai yarda ba zai ce muna neman tayar da fitina ko mu had'a shi da abokinsa.
Tun daga ranar da ta zo taga sauyi a tare da ni sai ta janye jikinta itama.
Amma ba gabad'aya sa'i da lokaci tana kirana a waya mu gaisa ko kuma na ga aike mussaman idan zata turo kaya garin nan to za ta had'o da sakon yara mai delivery ya kawo mini har gida.
Duk shekara kuwa idan ta fitar da zakka tana turo mini ta ce na duba family din mu wanda suke da k'aramar sana'a na ba su domin su tashi da kafarsu.
Wannan shine zan fad'a akan Maryam Amina amma ban ta'ba zarginta akan dukiyarta ba dalili nasan macace mai zafin nema mussaman a lokacin da iyayensu suka rasu ya kasance girma ya hau kanta duk itace take tsaye a kan 'yan uwanta kuma mijinta ya tsaya mata sosai har ta kafu kwarai ta tsaya da k'afafunta ko a lokacin da muke mu'amula sosai nasan tana da manyan shaguna uku daya a garinsu biyu a garin Abuja.
Amma yanzu labarin da nake ji a tsakanin matan abokan mijinmu ta mallaki wurare da yawa a rassa daban daban da ake mata hurd'a ta kasuwanci.
Lokacin da na samu labarin auranta da Alhaji Tajo na yi mamaki sosai ya aka yi ta amince da zama dashi a matsayin ma'aurata bayan yana da iyali ita kuma da bata son kishiya.
Sai babansu Madina yake gaya mini wasiyyar da Alhaji Amadu ya bari kenan amma ba zan boye miki ba wallahi na shiga tashin hankali ganin da na yi mata a yau sai na ji gabad'aya duniyar ta fice mini daga rai lallai d'an Adam ba a bakin komai yake ba.
Dama na sanar da Halisa kafin mu zo shine fa ta ce idan har na zo na ce tana gaisheta da sannu da jiki wallahi lokacin da nake gaya mata sakon Halisan sai hawaye shaaa suka sauka a kumatunta har na yi danasanin gaya mata ta ba ni tausayi sosai lallai Allah ya jarrabeta da ciwo mai wahala muna ro'kon Allah Ya bata lafiya ya kuma yafe mata kuskuranta."
Ajiyar zuciya na saki a hankali na ce." Amin suma Amin, muna nema mata afuwa da sasaauci wurin Allah, ai d'an adam sai dai idan ba hallice shi a duniya ba Hajiya amma tunda annabawan Allah suka kuskurewa Ubangiji kowane bawa ba zai tsallake ba, sai dai mu yi addu'a akan Allah Ya sa kada son zuciya ya sanya mu cutar da wani tabbas ban so jin wannan labarin ba wallahi ba zan boye miki ba hankalina ya tashi amma komai dalili yake yi.
Momi ta aikata abu mafi muni shirka shine had'a Allah da waninsa cutar da wanda bai ji ba kuma bai gani ba.
Idan na ce miki ta yi mana wani abu mai razanarwa na yi mata sharri domin ni dai a zamana da ita ban hangi wani babban lamari kwatankwancin na Halisa ba.
Kamar yadda kika fad'a macace mai alheri domin ta ri'ke mini yarana da ubansu ya rasu don 'karamin ma ya fi shekara shida a hannunta babban ne bai wani jima ba wani dalili ya katse zamansu a hannunta.
Idan kin ce ta gwanance wurin kissa da kisan mummk'e wannan zan bada sheda akan haka domin halin da muke ciki kenan da ita koda take kwancen nan maigidan hankalinsa yana wurinta kuma tsayin zamansu gaskiya bai ta'ba kawo mana wani korafi ko aibu a kanta ba asalima boye sirrinta yake yi ko fad'a suka yi ba ma ganewa.
Gabad'aya ya za'be ta ya fifita akanmu.
Kuma kin ga ni dai a zahiri mun fita kuruciya da komad'a amma wallahi a kanta ko 'ya'yanta sai ran kowa ya 'baci a gidan nan.
Ni matsalata da ita kenan.
Amma ta fanni asiri ni ban yi imani da cewa jifanta zai yi tasiri a jikina ba koda tana yi din wallahi ba a zaune nake ba nima ina ko'karin kare kaina da addu'a da neman tsari.
Ban 'ki ba shi maigidan domin a wasu lukutan abubuwan da yake yi kamar mai rangwamin hankali.
Amma duk ba wannan ba yanzu ta lafiyarta ake yi domin sai da lafiya ake komai.
Duk abinda muke zargi ko hasashe a kanta idan har tana aikatawa muna roka mata gafara daga wajan Allah mu ma ba mu wuce mu tsinci kanmu akan hanyar da ta bi ba ba mu da wayo ko dubara sai ta Allah.
Allah ya yafe mata da mu bakidaya."
Ta amsa da Amin Ya hayyu ya 'kayyymu, ai in banda na zo na ga halin da take ciki hankalina ya tashi wallahi babu wani dalilin da zai sanya na tashi maganar nan in banda yanzu kin ji babu wanda na ta'ba zama da shi na gaya masa sai dai zargi da hasashe da mutane suke yi a kanta, sannan da wasu maganganu da na ji ana yi a kan ku wai kun had'e mata kai ba ku sanyata a cikinku kun wareta kin san maganar duniya bata 'buya shine fa abin ya ba ni mamaki cikin zuciyata nake fad'in yadda nasan Maryam da wayo da kissa anya za ku iya kai ta 'kasa kuwa."
Da mamaki mai yawa na ce." A a wallahi ba mu ware ta ba sharri ne kawai irin na mutane amma ke don Allah a ina ki ka ji wannan maganar."
Tana yar dariya ta furta." Wallahi a gari na ji ni ma shine nake ta mamakin Hakan saboda nasan Maryam ba zata ta'ba yarda ta yi boranci a tsakaninku ba."
Na girgiza kaina da damuwa mai yawa na ce." Aikuwa masu fad'in haka sun d'auki hakkinmi ba mu ware Maryam ba wallahi, sharri ne kawai irin na mutane idan an ce babu jituwa a tsakaninmu na yarda amma babu maganar mun had'e mata kai ko mun ware ta."
Ta ce." Allah Ya kyauta dai yanzu gashi Halisa yaranta hud'u fa a gidan Murtala shine ai nake cewa Allah ya tsine abinda ba zai wuce ba."
Kafin na bud'e baki na yi magana suka shigo su biyu maigidan ne da mijin nata Alhaji Sulaiman.
Sai yanzu na sheda fuskarsa lokacin haihuwar twins da ya shirya walima na gan shi ya zo da kuma lokacin d'aurin auransa da Momin na ga hotonsu a tare ashe shine.
Suka iso wurin da muke zaune Alhaji Sulaiman din ya fad'in." Uwargida ta gidan Tajo ina 'yar uwar taki take ne?"
Ina d'an ya'ke na ce." Hauwa tana ciki ba ta jima da tashi ba, ina yini ya hanya mun gode sosai fa."
Ya ce." Ai ta ce za ta shigo ku gaisa ina can tsaye ina jiranta kusan minti talatin me kuka tattauna ne?"
Ya k
rasa maganar da barkwanci sai na yi dariya ganin mutum ne shi mai raha ba irin abokin nasa ba na ce." Hira muke yi ta duniya idan kana so ku ji abinda muka tattauna sai ku gaya mana abinda kuma ku ka tattauna a waje."
Sai kuwa ya fashe da dariya yana dukan kafadar abokin nasa kamar wani kurma yana tsaye yana kallonmu cikin dariyar dai ya ce." Ka ji fa mutumina to mu ai ba zai wuce sabgar kasuwanci muka tattauna ba ko ba haka ba ne?"
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Ita fa kishi ne da ita shiyasa take bugun cikinka ko tana tunanin aure zan 'kara."
Hajiya Aziza ta yi caraf ta ce." A haf yanzu gashi babu wanda ya matsa bakinka ka fad'a abinda yake zuciyarka kenan zaka kara aure tunda ya baka labarin yana neman cike gurbi ko."
Yasa dariya yana cewa." Wallahi ya gaya mini kuma wai budurwa ko?''
Ta ce." Budurbazar dai ba budurwa."
Sai suka fashe da dariya a tare.
Na yi sakato da baki Ina kallonsa yadda yake ta kyalkyala dariya yana tambayar Hajiya Aziza wai menene budurbazar ita kuma tana ta jin haushi domin daka ga ni da gaske mijin nata auran zai yi kuma budurwa."
Yana dariya ya dube ta yana fad'in." Ke in banda abinki ai abinda ake ya yi kenan kuma tsoho da kudinsa sai ya sha shagali ko ba haka ba ne mutumina."
Alhaji Sulaiman yana gyara babbar rigarsa ya ce." 'Kwarai kuwa Alhaji to menene sunna ce fa mai karfi kuma iyayen yaran nan ma yanzu sun fi so su bawa irin mu aure."
Na ce." Makwad'aitan iyaye ba, amma gaskiya kuna da budurwar zuciya kai fa har jikoki ne da ka, amma shine za ka d'auko musu magana."
Maimakon maganata ta bashi haushi sai ma ta bashi dariya tunda na lura mayen dariya ne tunda ya shigo bakinsa a bud'e yake ya ce." To shine me?
Amina daga kawai ina da jikoki uku sai aka ce na tsufa a ah ni yanzu ji na nake yi kalau da ni wallahi."
"Um!" Kawai na ce na juyar da kaina gefe abin yana damuna.